YADDA AKA YI IDIL GHADEER A BABBAN RAMI

Daga Auwal M. Tukur

A ranar Asabar 15/8/2020 da ta gabata ne, 'yan'uwa almajiran Sheikh Zakzaky na garin Babban Rami suka gabatar da taron Idil Ghadeer, wanda ya samu halartar daruruwan  'yan'uwa maza da mata,wadanda suka rika tudadowa daga Unguwanni daban daban cikin ado, suna zuwa zuwa wurin taron a Unguwar Kabawa inda Markhaz take a cikin garin Babban Rami.

Sai dai taron wanda ya fara gudana ne, da misalin karfe 8:30pm na dare. Inda aka fara da bude taro da addu'a da kuma karatun Al-Qur'ani tare da kanta ziyarar Amirul Mu'uminin daga nesa.

Malam Muhammad Tukur Wakilin 'yan'uwa almajiran Sheikh Zakzaky na garin shi ne wanda ya zama babban Bako a wurin taron. A cikin jawabinsa da ya gabatar, Malamin ya kawo Ayoyi da Hadisai a kan halifancin Amirul Mu'uminin, Imam Ali (A.S). Sannan ya yi ishara da albishir ga 'yan'uwa ma'abota wulaya da cewa; "Duk wanda ya samu tagomashin da wulayar Ahlul Baiti, to, ya godewa Allah. Malamin ya ci gaba da nuna cewa a ranar Alkiyama  za a tambayi duk wani mahaluki da ya bar  duniyar nan ba tare da wulayar Imam Ali (A.S) ba.

Malamin a cikin jawabinsa ya cigaba da nuna cewa; "Mu fa sakon Manzon Allah ne muke isar wa zuwa ga al'umma. Saboda a cikin hudubar da Manzon Allah yayi a ranar nadin halifan a bayan sa. Ya bayyana cewa, Uba ya sanar da Dan sa, 'Da ya sanar da Uban. Sannan wanda yaji ya sanar da wanda bai jiba. Shine yasa kuka ga a duk rana 18 ga watan Zulhijji mukan taru domin sauke nauyin da yake akan mu."

A kashen jawabin, Malam Muhammad Tukur, ya yi kira ga al'umma cewa lallai wajibine su tashi tsaye wurin neman ilimi, domin ta hanyar neman ilimi ne zasu Kara sanin suwaye Ahlul Baiti. Domin idan kasan ko su, suwaye  to shine zaka iya ganin su da kima. Sannan har ka samu a ranar Alkiyama katsira a gaban Allah.

A kusan kashen taron an raba walima. Tare da yin addu'ar Allah ya karbi wannan muhimmiyar ibadar da aka gudanar a muhallin na Markhaz, sai Malam Muhammad Tukur ya rufe da addu'a aka sallami kowa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post