YADDA AKA GUDANAR MU'UTAMAR A YANKIN KONTAGORA KARO NA 3 A GARIN BABBAN RAMI

~Auwal M. Tukur da Shana Islam

 11 August,2020


Ranar Asabar 8/8/2020 din da ta gabata ne. Yan Uwa matasa Dalibban Makarantu  na Da'irar Kontagora da kewaye. A Karkashin Jagorancin Shiekh Ibraheem El Zakzaky (h), suka gudanar da Taron Mu'utamar Karo na Uku.  Mai taken suna: *GINA SHAKSIYYAR MATASHI A TAFARKIN GWAGWARMAYAR TABBATAR ADDININ MUSULUNCI.*


Taron ya gudana ne a garin Babban Rami dake Cikin jihar Niger state, a yankin Kontagora. Inda program din ya fara ne Karfe 10:30pm safiyar Asabar. Sai dai an fara ne, da bude taro da Addu'a. Sai karatun Al-Qur'ani mai girma, kammala karatun ke da wuya aka cigaba da gudanar da Program din. Inda aka bawa Ittihadu dama domin su kamsasa filin da wakokin yabon Ahlil Bait. Sai dai a Ranar ta farko wajen taron ya samu halartar malamai masu jawabi kamar haka: 👇

 (1) Malam Muhammad Tukur B/Rami Wanda ya gabatar da maudu'in *ILIMI ADO GA MATASA*


 (2) Malam Yahya Kontagora ya gabatar da jawabi akan maudu'in *MU'AMALAT WAL AKHALAK* 

 

(3) Malam Abdullahi Bangi shima ya gabatar da nasa maudu'in Mai taken suna; *KYAKKYAWAR TARBIYA ADO GA MATASA* 


 ```Sai sallah da cin abinci```

 

Bayan dawowa daga sallah da cin abinci 


(4) Malam Isah Gulbi ya gabatar da nasa maudu'in na *GUDUMMAWAR MATASA A HARKAR MUSULUNCI A LOKACIN TSANANI DA KUMA LOKACIN SAUKI*

 

(5) Malam Abubakar Arzika Gulbi inda ya gabatar da maudu'in sa Mai taken suna *DA'AWAR SAYYID ZAKZAKY (H) FITINTINU DARASI GA MATASA*


 Sai sallah da cin abincin dare. Bayan dawowa aka sake dorawa daga inda aka tsaya.

 

 (6) Malam Muhammad Bello Wanda daya ne daga cikin wakilan mu'assatu Shuhada. Inda ya gabatar da maudu'in sa Mai taken suna *MUHIMMANCI BIYAN HAKKIN SHUHADA*

Duk cikar wa yannan malaman da aka  zaiyano. Sun gudanar da muhimman  jawaban nasu ne a ranar Farko. 

Suma Matasa ba a bar su a baya ba sun gudanar da wani shiri da suka Kira da suna Muryar matasa. Inda a cikin wannan shirin sun ba junan su shawarwari da zaburantar da juna a kan sha'anin gwagwarmaya, da fadakarwa a kan abubuwan yau da kullun. Inda  Mustapha Imam Kontagora ne yayi Ta'alikin wannan shirin.  Mustapha acikin jawabin sa ya karfafa  matasa sosai akan sha'anin neman ilimi. Wannan shine abinda ya guda a ranar farko.


*Sai Tahajjud da muhimman addu'o'in da aka yi a cikin Daren*


Sai da a rana ta biyu kuma ranar karshe Lahadi 9/8/2020, an ci gaba da program din. shima da misalin karfe 9:30am na safe inda, program din yaci gaba da gudana kamar yadda aka tsara. Bayana budewa da addu'a sai karatun Al-Qur'ani sai Sha'irrai suka yi baitucin wakoki da yake wannan ranar ce ranar karshe. 


Sai aka gabatar da Malam Umar Mariga Wanda ya gabatar da nasa maudu'in sa *HADAFIN HARKAR MUSULUNCI A NIGERIA KARKASHIN JAGORANCI SAYYID ZAKZAKY (H).*  Daga kammalawar sa ne aka Shiga agenda ta gaba.


 Inda aka gabatar *kacici kacici* tsakanin Brothers da Sisters. 


Sai Kuma aka gabatar wani maudu'i Mai suna *Muryar matasa* Wanda Mustapha Ibrahim Imam ne, ya gabatar da shi Wannan jawabin. Sai

jim kadan da fara jawabin na sai ga Babban Bako ya karaso filin program MALAM IBRAHEEM IMAM (Wakilin  yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H),na Garin Kontagora da kewaye). Wanda shi ne yayi Ta'alikin duk wani abinda aka gabatar a wurin. Inda Malam Muhammad Tukur (Wakilin yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Garin Babban Rami ) ne, ya gabatar da Fasihin Malamin. Inda Malamin yayi jawabi sosan gaske kai! abin dai  sai wanda yaji ya gani da Kuma aka yi a gaban  idanuwan sa.


Bayan Malamin ya kammala jawabin sa. Aka yi wasu tambayoyi ya amsa.  


Sai dai an sake gabatar da Malamin. Domin ya mikawa wasu daga cikin Dalibban da suka nuna hazaka a lokacin gudanar da kacici kacici kyautukka. 


Sai Wakilin matasan Garin na Babban Rami Safiyyanu M. Halilu,ya gabatar da jawabin godiya ga Malamai da Kuma mahalarta  Wannan program din.


Sannan kuma daga bisani  aka sake mika Malamin  abin magana domin yayi  Addu'a. Inda gama bayan kammala Addu'ar ne aka  sallami kowa.


Muna Amfani da wannan damar wajen mika sakon Gaisuwa da Ban gajiya ga Mahalarta taron Musamman Malaman mu da suka taso daga garuruwa mabanbanta suka zo. Da sauran yan uwa maza da mata. Da fatan kowa ya koma gidan sa lafiya ? Allah ya saka da alkhairi.


*Daga kwamitin shirye shirye tare da hadin gwuywar wakilan Kontagora Media Forum da na Shafin Ma'asuma*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post