Tabbas, Yazid Ibn Mua'wiya Ne Ya Sa Aka Kashe Imam Husein (A.S) –Inji Ibn Taimiyya


 

YAZID IBN MU'AWIYA YA KASHE MUTANEN MADINAH. YAZID BA SAHABI BA NE, HASALIMA BA MUTUMEN KIRKI BA NE... INJI IBN TAIMIYYA.

BAYAN AN KASHE HUSAIN(AS) AN CIRE KANSA AKA KAIWA YAZID IBN MU'AWIYA, YA DINGA WASA DA HAKORAN HUSAIN(AS) YA NA JIN DADI AKAN KASHE SHI. - INJI BUKHARI, AZ-ZAHABI, AT-TABARI, AHMAD IBN HANBAL...

YAZID IBN MU'AWIYA NE YA BADA UMARNIN KASHE IMAM HUSAIN(AS). INJI IBN KASIR, AZ-ZAHABI, AT-TABARI...

Ibn Taimiyya ya na cewa:

"Ra'ayin Mutane ya kasu kashi 3 akan Yazid Ibn Mu'awiya...

Ra'ayi na 3 (ra'ayin Ahlus-sunnah; akan Yazid):

Yazid sarki ne daga cikin sarakunan Musulmai [ba khalifan Annabi(saw) ba ne], ya na da kyawawa da munanan ayuka, a lokacin khalifanci Usman(r) aka haifi shi, ba kafiri ba ne, amma fa tabbas shine ya yi sanadin kisan Husain(as), doriya akan ya yiwa (Sahabbai da Tabi'ai) Mutanen Madina kisan gilla. Don haka (Yazid) ba Sahabi ba ne, hasalima ba ya cikin bayin Allah nagari (mutumin banza ne); wannan shine ra'ayin jamhurin ma'abuta hankali da Ilimi, kuma shine ra'ayin Ahlus-Sunnah wal Jama'a (akan Yazid)":

ﻗﺎﻝ ﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ :

ﺍﻓْﺘَﺮَﻕَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱُ ﻓِﻲ ﻳَﺰِﻳﺪَ ﺑْﻦِ ﻣُﻌَﺎﻭِﻳَﺔَ ﺑْﻦِ ﺃَﺑِﻲ ﺳُﻔْﻴَﺎﻥَ ﺛَﻠَﺎﺙُ ﻓِﺮَﻕٍ : ﻃَﺮَﻓَﺎﻥِ ﻭَﻭَﺳَﻂٌ .

ﻭَﺍﻟْﻘَﻮْﻝُ ﺍﻟﺜَّﺎﻟِﺚُ : ﺃَﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﻣَﻠِﻜًﺎ ﻣِﻦْ ﻣُﻠُﻮﻙِ ﺍﻟْﻤُﺴْﻠِﻤِﻴﻦَ ﻟَﻪُ ﺣَﺴَﻨَﺎﺕٌ ﻭَﺳَﻴِّﺌَﺎﺕٌ ﻭَﻟَﻢْ ﻳُﻮﻟَﺪْ ﺇﻟَّﺎ ﻓِﻲ ﺧِﻠَﺎﻓَﺔِ ﻋُﺜْﻤَﺎﻥَ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﻛَﺎﻓِﺮًﺍ؛ ﻭَﻟَﻜِﻦْ ﺟَﺮَﻯ ﺑِﺴَﺒَﺒِﻪِ ﻣَﺎ ﺟَﺮَﻯ ﻣِﻦْ ﻣَﺼْﺮَﻉِ " ﺍﻟْﺤُﺴَﻴْﻦِ " ﻭَﻓِﻌْﻞِ ﻣَﺎ ﻓُﻌِﻞَ ﺑِﺄَﻫْﻞِ ﺍﻟْﺤَﺮَّﺓِ ﻭَﻟَﻢْ ﻳَﻜُﻦْ ﺻَﺎﺣِﺒًﺎ ﻭَﻟَﺎ ﻣِﻦْ ﺃَﻭْﻟِﻴَﺎﺀِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟﺼَّﺎﻟِﺤِﻴﻦَ ﻭَﻫَﺬَﺍ ﻗَﻮْﻝُ ﻋَﺎﻣَّﺔِ ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻌَﻘْﻞِ ﻭَﺍﻟْﻌِﻠْﻢِ ﻭَﺍﻟﺴُّﻨَّﺔِ ﻭَﺍﻟْﺠَﻤَﺎﻋَﺔِ .

- ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ : ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ، ﺝ 4 ، ﺹ 481 - 483 ، ﻣﻔﺼﻞ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻓﺼﻞ : ﻓﻲ ﺍﻓﺘﺮﻕ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﺛﻼﺙ ﻓﺮﻕ .

Mahallush-shahid a maganar Ibn Taimiyya; mai tabbatar da Yazid ne ya sa aka kashe Imam Husain(as):

ﻭَﻟَﻜِﻦْ ﺟَﺮَﻯ ﺑِﺴَﺒَﺒِﻪِ ﻣَﺎ ﺟَﺮَﻯ ﻣِﻦْ ﻣَﺼْﺮَﻉِ " ﺍﻟْﺤُﺴَﻴْﻦِ ".

Kalmar ﻣَﺼْﺮَﻉِ ta nufin kisa:

ﻣَﺼﺮَﻉ : ﻣﻘﺘﻞ، ﻣﺼﺎﺭﻉ ﺍﻟﻤﺤﺎﺭﺑﻴﻦ : ﺃﻣﺎﻛﻦ ﻣﻘﺘﻠﻬﻢ . - ﻣﻌﺠﻢ ﺍﻟﺮﺍﺋﺪ : ﻣَﺼﺮَﻉ .

Ibn Taimiyya ya na cewa:

"An haifi Yazid Ibn Mu'awiya ne a lokacin khalifancin Usman Ibn Affan(r), don haka dukkan malamai sun yi ittifaki akan Yazid ba Sahabi ba ne; tunda bai yi zamani da Annabi(saw) ba. (Yazid) ba'a san shi da riko da addini ba, ba ya cikin mutunen kirki (mutumin banza ne)":

ﻗﺎﻝ ﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ :

ﺇِﻥَّ ﻳَﺰِﻳﺪَ ﺑْﻦَ ﻣُﻌَﺎﻭِﻳَﺔَ ﻭُﻟِﺪَ ﻓِﻲ ﺧِﻠَﺎﻓَﺔِ ﻋُﺜْﻤَﺎﻥَ ﺑْﻦِ ﻋﻔﺎﻥ ‏( ﺭ ‏) ﻭَﻟَﻢْ ﻳُﺪْﺭِﻙْ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ‏( ﺹَ ‏) ﻭَﻟَﺎ ﻛَﺎﻥَ ﻣِﻦْ ﺍﻟﺼَّﺤَﺎﺑَﺔِ ﺑِﺎﺗِّﻔَﺎﻕِ ﺍﻟْﻌُﻠَﻤَﺎﺀِ؛ ﻭَﻟَﺎ ﻛَﺎﻥَ ﻣِﻦْ ﺍﻟْﻤَﺸْﻬُﻮﺭِﻳﻦَ ﺑِﺎﻟﺪِّﻳﻦِ ﻭَﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺡِ ...

- ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ : ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ، ﺝ 3 ، ﺹ 410 ، ﻣﺠﻤﻞ ﺍﻋﺘﻘﺎﺩ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻓﺼﻞ : ﻓﻲ ﻭﺟﻮﺏ ﺍﻻﻗﺘﺼﺎﺩ ﻭﺍﻻﻋﺘﺪﺍﻝ ﻓﻲ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭﺍﻟﻘﺮﺍﺑﺔ، ﺃﻋﺪﻝ ﺍﻷﻗﻮﺍﻝ ﻓﻲ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ .

Bukhari, At-tirmizi, Ahmad Ibn Hanbal... su riwaito; bayan an kashe Husain(as) an cire kansa an kaiwa Ubaidullah bin Ziyad (Gwamnan Yazid), ya dinga wasa da hakoran Husain(as) ya na jin dadi akan kashe shi:

ﺣَﺪَّﺛَﻨِﻲ ﻣُﺤَﻤَّﺪُ ﺑْﻦُ ﺍﻟْﺤُﺴَﻴْﻦِ ﺑْﻦِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﻗَﺎﻝَ : ﺣَﺪَّﺛَﻨِﻲ ﺣُﺴَﻴْﻦُ ﺑْﻦُ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﺣَﺪَّﺛَﻨَﺎ ﺟَﺮِﻳﺮٌ، ﻋَﻦْ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻋَﻦْ ﺃَﻧَﺲِ ﺑْﻦِ ﻣَﺎﻟِﻚٍ ‏( ﺭَ ‏) ﺃُﺗِﻲَ ﻋُﺒَﻴْﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺑْﻦُ ﺯِﻳَﺎﺩٍ ﺑِﺮَﺃْﺱِ ﺍﻟْﺤُﺴَﻴْﻦِ ‏( ﻉَ ‏) ،ُ ﻓَﺠُﻌِﻞَ ﻓِﻲ ﻃَﺴْﺖٍ، ﻓَﺠَﻌَﻞَ ﻳَﻨْﻜُﺖُ، ﻭَﻗَﺎﻝَ ﻓِﻲ ﺣُﺴْﻨِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ، ﻓَﻘَﺎﻝَ ﺃَﻧَﺲٌ : ﻛَﺎﻥَ ﺃَﺷْﺒَﻬَﻬُﻢْ ﺑِﺮَﺳُﻮﻝِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ‏( ﺹَ(، ﻭَﻛَﺎﻥَ ﻣَﺨْﻀُﻮﺑًﺎ ﺑِﺎﻟْﻮَﺳْﻤَﺔِ .. .

- ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ : ﻛﺘﺎﺏ : ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ | ﺑﺎﺏ : ﻣﻨﺎﻗﺐ ﺍﻟﺤﺴﻦ، ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ . ‏( 3748 ).

- ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻓﻲ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻤﻨﺎﻗﺐ ﻋﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ‏( ﺹ ‏) ، ﺑﺎﺏ ‏( 3778 ‏) ‏( 119 / 6 ).

- ﻣﺴﻨﺪ ﺃﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﻣﺴﻨﺪ ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ‏( ﺭ ‏) ‏( 13748 ‏) ‏( 285 / 21).

Az-Zahabi da At-Tabari sun riwaito; lokacin da Ubaidullah bin Ziyad ya sa aka kashe Husain(r), ya sa an sare kan Husain(r), ya aikawa Yazid Ibn Mu'awiya kan Husain(r), Yazid ya ji dadin sosai akan kisan Husain(r), ya karawa Ubaidullah girman mukami:

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ ﻭ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ :

ﻟﻤﺎ ﻗﺘﻞ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻭﺃﻫﻠﻪ . ﺑﻌﺚ ﺑﺮﺅﻭﺳﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﻳﺰﻳﺪ، ﻓﺴﺮ ﺑﻘﺘﻠﻬﻢ ... ﻭﺣﺴﻨﺖ ﺑﺬﻟﻚ ﻣﻨﺰﻟﺔ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ...

- ﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ : ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ، ﺝ ٣، ﺹ ٣١٧ . ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻮﻓﺎﺓ : ٧٤٨ . ﺗﺤﻘﻴﻖ : ﺇﺷﺮﺍﻑ ﻭﺗﺨﺮﻳﺞ : ﺷﻌﻴﺐ ﺍﻷﺭﻧﺆﻭﻁ / ﺗﺤﻘﻴﻖ : ﻣﺄﻣﻮﻥ ﺍﻟﺼﺎﻏﺮﺟﻲ . ﺍﻟﻄﺒﻌﺔ : ﺍﻟﺘﺎﺳﻌﺔ . ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻨﺸﺮ : ١٤١٣ - ١٩٩٣ ﻡ . ﻣﺆﺳﺴﺔ ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ ﺑﻴﺮﻭﺕ .

- ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ : ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ، ﺝ ٤، ﺹ ٣٨٨ . ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻮﻓﺎﺓ : ٣١٠ . ﺗﺤﻘﻴﻖ : ﻣﺮﺍﺟﻌﺔ ﻭﺗﺼﺤﻴﺢ ﻭﺿﺒﻂ : ﻧﺨﺒﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻷﺟﻼﺀ . ﻣﻨﺸﻮﺭﺍﺕ ﻣﺆﺳﺴﺘﻪ ﺍﻷﻋﻠﻤﻲ ﻟﻠﻤﻄﺒﻮﻋﺎﺕ ﺑﻴﺮﻭﺕ - ﻟﺒﻨﺎﻥ .

Az-Zahabi ya riwaito; Wani mutum ya zo wajen Yazid Ibn Mu'awiya, sai ya ce masa albishirinka! Allah ya doraka kan Husain(r), ga kansa an kawo maka, sai Yazid ya dora kan Husain(r) kan durduma, aka bude kan, Yazid ya dinga wasa da hakoran Husain(r), an aje kan Husain(r) a fadar Yazid har tsawon kwana 3.

Daga baya aka dauki kan Husain(r) aka aje a dakin aje makamai, kan Husain(r) ya cigaba da zama a dakin aje makamai har lokacin khalifancin Sulaiman, daga baya aka fito da kan; ya yi fari fyas, aka binne shi, amma wasu mutune sun tono kan; ba'a san inda su ka kai shi ba.

Isnadin wannan riwayar ya inganta - inji Az-Zahbi:

ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ :

ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﺃﺑﻲ ﺣﻤﺰﺓ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post