LOKACIN DA KANANAN HALITTA SUKE FIN MU KUSAN TA DA ALLAH.Wani lokacin Allah ya kan buga misali da kananan halittu da ba su kai dan Adam ba don ya motsar da hankalin dan Adam zuwaga lura alokacin da ya rafkana:

1-mutum yafi saniya daraja a wurin Allah,to amma lokacin da dan Adam ya zamo yana cutar da dan uwan sa mutum saboda bacin zukata sai wannan dabba tafi mutum daraja da  karama wurin Allah.

Allah zai iya cema wani daya daga Banu Isara'ila ya bigi ko ya shafi wannan mutum da aka kashe acikin su don ya rayu ya fadi wanda ya kashe sa,amma saboda matsalar su akace su nemo shanuwa saboda tsarkakar ta, wannan mutum zai rayu idan suka shafe sa da wani bangare na namanta ba ma ita shanuwar baki daya ba,anan andaukaka darajar wannan dabba saboda yadda halin dan Adam mara kyau.

wannan shi ya nuna mana tsarkakar Annabi Isa ce عليهالسلام yasa Allah ke raya matattu da zancen sa kadai.

maana lokacin da zukatan mu suka lalace babu abun da zai iya rayu ta hanyar mu.

2-mafi yawan mutane suna dakko labarin da ba su tabbata ba kuma ba su gani ba ko ba su fahimta ba ko su ke zato, amma duk da haka suita watsa shi yar wata karamar manufar su ta wannan duniya mai karewa.

Allah ya buga mana misali da Alhudada alokacin da zai kawo ma Annabi SULAIMAN labari baice:ina zato ba, baice naji labari ba,baice na karanta ba, baice haka dai aka ce min ba,baice babban mutum bane yaban labari,a'a ya ce ne:
وجئتك من سبإ بنباء يقين
na zoma da labari na nagaskiya ina mai sakankancewa da haka daga garin Saba, lallai na same su suna bautar abun da ba Allah ba.

wannan ya nuna da mutane za su zama kamar Alhuda huda,to da karya da gulma da munafurci da kiyaiya da kazafi bai watsu acikin su ba.

ana bada misali da dabbobi ne saboda wata kila mutum idan akace Annabawa ko wasu bayin Allah sukai haka sai yace: ai su manya ne mu ba za mu iya ba.

3-idan mutane suna da masu mulki,sai ya zama masu mulkin ba su damu da kare rayuwar talakawan su daga hadari ba sai a nuna mu su cewa:lallai kwaron tururuwa ya fi su ki shi kuma ya na da kyau hankalin su ya girma ya zama irin na shi.

domin kwaron tururuwa da taji Annabi sulaiman zai wuce da sojojin sa tace kowa ya bar wannan hanya don ya tsira da kan saلا يحطمنكم سليمان وجنوده وهم لايشعرون.
wannan ya nuna tsananin kishi daga jagora na dabba, to inaga mutum da yake tunanin ya wuce dabba?

sai jagora ya dauki rayuwar talakan sa kamar rayuwar sa da matan sa da yayan sa sannan zai iya amsa sunan shugaba ko jagora.

4-wani lokaci mutum zai iya turaka ka aikata aiki mara kyau saboda kana ganin girman sa ko dan yana dauke da nauyin ka.

akwai wasu mutane suna bukatar ka bi su acikin daidai da kuskure ta yadda zaka zama kamar katako sai yadda aka juya shi.ka mance akan karyar su hakan shi ne biyaiya.

wataran mutum yakan manta shi mutum ne alokacin da yake aikata mummunar manufar wani mutum ba tare da yai wani tunani ba.

acikin haka za muga Allah na ba mu misali da Giwa mai turjiya aduk lokacin da Sarki Braha ya nuna mata dakin Kaabah da nufin ta rushe shi.

saboda tsarkakar wannan Giwa Allah ya kira wanda suke turata zuwaga sharri da أصحاب الفيل ba ace أصحاب أبرهة ba.
domin ita tana nuna musu rashin daidai kamar yadda bayin Allah da Annabawa suke dora Sahabban su akan daidai da nisantar matsala.
كم رأينا ماليس يعقل قد أُل
     هما ما ليس يلهم العقلاء

ma ana' duk lokacin da ake tura ka zuwaga aikata wani sharri, to kai kokarin zama kamar giwar Abraha wurin turjiya ko kafita turjiya saboda zamowar ka mutum da Allah yafi girmamawa a cikin halitta.
sharri na magana,sharri na aiki,sharri na nuni duk abun nisanta ne.

Akwai misalai da yawa wanda idan mutum yaje Alqura'n zai same su, ta yadda  zaiga idan dan Adam ya kaskantar da kan shi akan son ran shi sai Allah yaba dabba fifiko akan sa.

sannan kuma ta wani bangaren ana so mutum ya bude tunanin sa ta yadda zai samu ilmi da tunani ta hanyar kowace halitta a wannan duniya.

Ibnu Araby yana cewa: ni Almajiri ne ga kowa ne abu a duniya domin idan na lura ina karuwa da abin da ke tare da shi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post