Kuzo Kuji Wani Abin Mamaki Yan Uwa Musulmi: Sunce Wai Annabi Bai Sa Halifa Ba A Bayan Sa (S.A.W.W)


Mukace da su ku kawo nassi guda daya tak Wanda annabi ya Nada Abubukar da Umar da usman abainar jama'a kamar yadda annabi ya Nada imam Ali a bainar jama'a, haryau shiru kukeji babu.Su kazo sukace wai annabi ya Nada Abubukar.

Mukace dasu mu dauka cewar annabi ne ya Nada Abubukar, shin a Ina annabi ya nadashi? A wanne waje? Da yaushe ? A wacce shekara? Idan har annabi ne ya Nada Abubukar shin ya akayi wasu gungun sahabbai, daga ciki akwai Abubukar da Umar suka tafi sakifa a matsayin wakilan muhajarun, a fannin ansaru, Ga su sa'ada domin gudunar d zabe tunma kafin abizne manzan Rahama (sawa) sai imam Ali suka bari akan gawar annabi alhali wai ance duk sunfi Ali daraja, Amman su Ka tafi sukabar gangar jikin annabi. suka rasa yadda zasuyi su bizne wannan barna sai suka kirkiri karayrayi, wai annabi bama abinneshiba sai bayan kwana uku darasuwarsa.

Maluma suka kara da cewar wai sukace sahabbai su suka hadu akan hilafar Abubukar tare da cewar sun manta sunce annabine ya nadashi halifa, suka Kara da cewar wai duk Wanda ma bai yarda da kilafa Abubukar bama wai ya kafirta, tare da cewar ko sun manta YAR annabin mu batayi Wa Abubukar bai aba? Da wasu ba arin gungun sahabbai da sukace su ba zasu saba umarni annabi ba? Domin su sunce Ali annabi ya NADAMANA?
Kar da ku manta da farko sunce annabi wai bai nafasata kowa ba a matsayin halifansa ba, shin zai yiwu annabi ya yakoma Ga Allah batare da ya nasafta halifansa ba? Banjin mutumin da ya ke da cikeeken hankali zai iya wannan maganar, suka rasa yadda zasuyi sukace wai annabi ya Nada Abubukar tare da cewar babu hadith daya tak Wanda duniyar musulinci suka hadu akan annabi ya Nada Abubukar tambayar ya akayi suka tafi zabe sukifa? 

Tambayar shine, shin annabi zai Nada mutum a matsayin halifansa tare da cewar KUR'ANI baisan kur'aniba? Hasalima bai hadacceba? Shin zai iya yiwa annabi yanada halifa a tambayeshi dangane da wata mas'ala ta fikihu ya kasa ba da amsa? Shin zai yiwu annabi ya na da halifa a rasa yadda za'ayi a amsa Tambaya sai dai anemu kanin annabi duk inda yake,? Sannan ya masa tambayar? Tare da cewar duk duniyar musulinci an hadu ba'a taba tambayar Ali ba, yace bai saniba, yakan ba da amsa tamkar fitar kibiya daga cikin maharbarta.

Duk wannan kwalekwalen da wasu daga maluman musulinci sukai shine Dan bawa wadannan bayin Allah kariya na irin kuskuran da bayin Allah nan sukai sai suka kirkirar masu hadith Dan basu kariya.

Tare da cewar da suka rasa yadda zasuyi, da hadith ghadir KUM, da sai suke musantawa suke cewa wai karairayin yanshi'ane, da sukaga uwar bari sai suka ce wai annabi bayana nufin shugababa yana nufin MASOYI, domin duk sukara rikitar da al'umma Dan karsubi hakikaninin wasiccin ANNABI (sawa) tare da cewar a matakin farko shin MAULA ta takaita da Kalmar MASOYI kadai? Baya Ga haka a Ina aka tambayi annabi yace MAULA da nace akan Ali Ina nufin MASOYI? A Ina a wanne waje? Karin tambayar shine shin da Annabi ya umarci SAHABBAN sa da sukawo masa abin rubutu ya rubuta musu abin da idan sun rike bazasu taba bata abayansa ba? Me sukace dashi, sanin kowane UMARU ne yace KUR'ANI ya ishesu suka kama hauragiya annabi yace kutashi ku barni, wannan kawai ya ishi duk wani me hankali ya gane cewar hakikanin abin da yafaru a addinin musulinci wai kuma wadannan sune halifofin annabi kai me hankali ya isheka ishara, kasan cewar annabi yadda ya bar addininsa, bahaka yakeba, an sauya abubuwa da daman gaske, me kuke tunani Wanda zai dubi annabi ya ce su littafin Allah ya ishesu har annabi ya ce su tashi su bashi guri, kuma ace su zai Nada halifofin sa? Tare da cewar annbi yana halin rashin lafiya. Kuma wai wadannan sune halifofin annabi? Tare da cewar babu wani hadith da Annabi ya Nada wadannan bayin Allah a abainar jama'a kamar yadda ya Nada Ali (as) a abainar jama'a kimanin dubu 100 wasu ruwawoyin dubu 120.
Ya rage gareku yan uwa MUSULMAI KUYI bincike Dan gane hakikanin wasiccin manzan Rahama (sawa).
Happy gadir KUM to all musulum umma.
©Habibu Rabiu Nasrallah


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post