Ko Ka San: Kwatankwacin Banu Isra'ila Da Wannan Al'ummar?




Kamar yadda tarihi yazo mana, lokacin da Annabi MUSA zai tafi ganawa da Allah yasa annabi harun ya a matsayin wakilinsa kuma magajinsa har yazuwa lokacin da zai dawo, shin menene ya faru? Shin banu israel subi annabi haruna? Sanin kan mune banu Israel sun juyawa annabi harun baya sukabi samari inbanda yan kadan da suka rage tare da Annabi Haruna, to hakama wannan al'ummar annabi (sawa) ya sa imam Ali a matsayin Wanda za'abi a bayansa Amman aka sauya. A matsayi Ka name tunani bamusu ya kamata kayiba, a'a bincikawa ya kamata kayi shin hakan da gaskene?

 Mu dauka cewar annabi MUSA shine annabin karshe, kuma tafiyar nan da yayi mukaddara mutuwa yayi, yadda ya sa haruna mutane suka kujeshi sukabi samari, to na tabbata da yanzu addinin samari muke ba addinin musaba to haka ya faru da wannan al'ummar wajibine kai a matsayinka na MUSULMI karka daka ta maluma kayi bincike da kanka domin taskace gaskiya domin wasu daga maluma na cewa e GASKIYA ne Amman fadar hakan karawa shi'a karfine shiyasa suke Jan baki suyi shiru, wasu kuma idan sun rasa yadda zasuyi sai suce ai MAULA na nufin MASOYI, Tambaya shin wanene yace MAULA na nufin MASOYI shin antambayi Annabi ya ce MAULA Ina nufin MASOYI, ko kuma ansami wata ruwaya guda daya tak da aka rawaita da Ga wani sahabi ya ce ANNABI na nufin MASOYI? Ko kuma ansami wata ruwaya daga shi Aliyu bin abi talib ya ce ANNABI yana nufin MASOYI ba shugaba? Haba maluma kuji tsoran Allah anya kuwa mun yi imanin da wannan annabin kuwa? Mubishi a wani waje muki binsa a wani waje? Ya rage gareku yan uwana MUSULMI KUYI bincike Dan gane gaskiya

©Habibu Rabiu Nasrallah.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post