ANNABI MUHAMMADU(SAW) NE FARKON WANDA YA FARA YIN KUKA AKAN KISAN IMAM HUSAIN(AS), [HASALIMA ANNABI(SAW) NE YA ASSASA SUNNAR JUYAYI, ALHINI DA KUKA AKAN KISAN IMAM HUSAIN(AS)]. - INJI AL-BANI, AHMAD IBN HANBAL, AT-TIRMIZI...




KIN YIN KUKA, JUYAYI DA NUNA ALHINI AKAN KISAN IMAM HUSAIN(AS) BIDI'AH NE, DORIYA AKAN RASHIN RUHIN MUTUNTAKA (HUMANITY : الإنسانية):

DUK WANDA YAYI KUKA AKAN KISAN DA AKA YIWA IMAM HUSAIN(AS) DA IKHLASI; DAN AL-JANNAH NE. INJI AHMAD IBN HANBAL, IMAM AS-SADIQ(AS), IMAM AR-RIDA(AS)...

UMMUL-MUMININ AISHA TA KARYATA DUK WANI HADISI DA YA HARAMTA YIN KUKA AKAN MUTUWAR WANI MUSULMI. INJI BUKHARI, MUSLIM...

HADISAN DA KE HANA YIN KUKA AKAN MUTUWAR MUSULMI SUN CI KARO DA AYOYIN QUR'ANI, DON HAKA BA YACCE ZA'AYI SU INGANTA KOMAI INGANCIN ISNADINSU:

Ahmad bin Hambal, Tabari, Al-bani, Ahmad Shakir, Abu Ya'ala, Al-Bazzar, Haisami, Tabarani... sun tabbatar da Annabi Muhammad(saw) ne farkon wanda ya fara yin kuka cike da alhini da juyayi akan kisan Imam Husain(as):

648 حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ عُبَيْدٍ، حَدَّثَنَاشُرَحْبِيلُ بْنُ مُدْرِكٍ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ نُجَيٍّ، عَنْ أَبِيهِ، أَنَّهُ سَارَ مَعَ عَلِيٍّ(ر) وَكَانَ صَاحِبَ مِطْهَرَتِهِ، فَلَمَّا حَاذَى نِينَوَى وَهُوَ مُنْطَلِقٌ إِلَى صِفِّينَ فَنَادَى عَلِيٌّ(رَ) : اصْبِرْ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ، اصْبِرْ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ، بِشَطِّ الْفُرَاتِ. قُلْتُ: وَمَاذَا؟ قَالَ : دَخَلْتُ عَلَى النَّبِيِّ(ص) ذَاتَ يَوْمٍ وَعَيْنَاهُ تَفِيضَانِ، قُلْتُ : يَا نَبِيَّ اللَّهِ، أَغْضَبَكَ أَحَدٌ؟ مَا شَأْنُ عَيْنَيْكَ تَفِيضَانِ؟ قَالَ : "بَلْ قَامَ مِنْ عِنْدِي جِبْرِيلُ قَبْلُ، فَحَدَّثَنِي أَنَّ الْحُسَيْنَ يُقْتَلُ بِشَطِّ الْفُرَاتِ، قَالَ: فَقَالَ : هَلْ لَكَ إِلَى أَنْ أُشِمَّكَ مِنْ تُرْبَتِهِ؟" قَالَ : قُلْتُ : نَعَمْ. فَمَدَّ يَدَهُ فَقَبَضَ قَبْضَةً مِنْ تُرَابٍ فَأَعْطَانِيهَا، فَلَمْ أَمْلِكْ عَيْنَيَّ أَنْ فَاضَتَا.

- مسند أحمد | مُسْنَدُ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ(رَ) : (648) : الجزء رقم : 2، الصفحة رقم : 77 : التأليف والنشر : الدار العربية لتقنية المعلومات : 2017 : المملكة العربية السعودية - شارع العليا العــام – الرياض – طريق الملك فهد - حي التخصصي. جمهورية مصر العربية – 49 شارع نوبار - باب اللوق - القاهرة.

"... Abu Nujayyi (daya daga cikin Sahabban Imam Ali(as), yana cewa; wata rana muna tafiya tare da Imam Ali(as) akan hanyar mu ta zuwa (yakin) Siffin, da muka zo wani guri da ake kira Naunawa (tsohon sunan Karbala), sai Imam Ali(as) ya ke cewa: Ka yi hakuri ya Husain(as)! Ka yi hakuri ya Husain(as) da kogin Furat (Euphrates). Sai na ce; kamar ya? Imam Ali(as) ya ce; wata rana na je wajen Annabi Muhammad(saw) (na tarar da shi yana kuka, har) hawaye na zuba so sai daga Idonsa, sai ya ce da ni; yanzu Mala'ika Jibril(as) ya tashi daga gurina; yake gayamin cewa: za'a kashe Husain(as) a kusa da kogin Furat. Shin kana so na baka Kasar gurin da za'a kashe shi? na ce; Eh! Sai Jibril(as) ya mika hannunsa ya danko Kasar ya bani, wannan ne yasa na kasa mallakar idona daga yin kuka".

(ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ : ﻣﺤﻤﺪ ﻧﺎﺻﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ : ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻤﻌﺎﺭﻑ - ﺍﻟﺮﻳﺎﺽ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : 7 : حديث : 1171).

Sahihin hadisin da ya tabbatar da Annabi Muhammad(saw) ya yi kuka akan kashe Imam Husain(as); ya zo a littattafan Ahlus-Sunnah masu yawan gaske. Albani, Ahmad Shakir, Haisami... sun inganta wannan hadisin:

ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ، ﻭﺫﻛﺮﻩ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺑﺮﻗﻢ 1171 ﺛﻢ ﺫﻛﺮ ﻃﺮﻗﻪ ﺍﻷﺧﺮﻯ، ﺛﻢ ﻗﺎﻝ: ﻭﺑﺎﻟﺠﻤﻠﺔ ﻓﺎﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻟﻤﺬﻛﻮﺭ ﺃﻋﻼﻩ ﻭﺍﻟﻤﺘﺮﺟﻢ ﻟﻪ، ﺻﺤﻴﺢ ﺑﻤﺠﻤﻮﻉ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻄﺮﻕ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺣﻤﺪ 648 ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺣﻤﺪ ﺷﺎﻛﺮ ﻓﻰ ﺗﺨﺮﻳﺞ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻰ. ﻟﻢ ﻳﻨﻔﺮﺩ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻰ ﺑﺘﺼﺤﻴﺤﻪ ﻓﻘﺪ ﺳﺒﻘﻪ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺣﻤﺪ ﺷﺎﻛﺮ ﻓﻰ ﺗﺨﺮﻳﺠﻪ ﻟﻠﺤﺪﻳﺚ ﻓﻰ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ (ﻣﺴﻨﺪ ﺃﺣﻤﺪ - ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ ﺃﻭ ﺍﻟﺮﻗﻢ : 2/60). ﻭﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻤﺎ ﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻰ ﻓﻰ ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺰﻭﺍﺋﺪ (ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺰﻭﺍﺋﺪ - ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ ﺃﻭ ﺍﻟﺮﻗﻢ : 9/183). ﻓﻘﺎﻝ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺣﻤﺪ ﻭﺍﺑﻮ ﻳﻌﻠﻰ ﻭﺍﻟﺒﺰﺍﺭ ﻭﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻰ ﻭﺍﺳﻨﺎﺩﻩ ﺛﻘﺎﺕ.

Tabari, a ZAKHA'IRUL-UKBA, ya ruwaito daga Ummul-Muminin Ummu-Salmah(r) tana cewa;

"Wata rana ina cikin gida sai na ji kukan Annabi Muhammad(saw) a cikin dakina, sai na je na leka don naga me ke faruwa, sai na taradda Husain(as) a kan cinyar Annabi(saw) ya na shafar kansa yana kuka, sai nace: ya Rasulallah(saw)! me ya sa ka ke yin irin wannan matsanancin kukan? sai Annabi(saw) ya ce da ni: Hakika Jibril(as) ya ba ni labarin cewa wannan dana (Husain(as) za'a kashe shi a wata kasa a Iraki, ana kiran ta KARBALA. Ummul-Muminin Ummu-Salma(r) ta ce sai Annabi(saw) ya miko min Kasar a cikin tafin hannunsa, ya ce da ni: Wannan ita ce kasar filin da za'a kashe shi a kanta, kuma ki ajiye ta duk sanda ki ka gan ta ta zama jini; to ki sani hakika an kashe shi. Ummul-muminin Ummu-Salma(r) ta ce sai na ajiye wannan kasar a cikin wata kwalba, ina cewa: Hakika wunin da wannan kasar zata juya ta koma jini wuni ne mai girman Musiba".

Tirmizi ya riwaito cewa bayan an kashe Imam Husain(as); Ummul-muminin Ummu-Salma ta yi kuka sosai, har take cewa; Annabi(saw) ne ya gayamata a mafarki an kashe Imam Husain(as), kuma ta ga Annabi(saw) a mafarkin cike da alhini, damuwa da juyayin (akan kisan Imam Husain(as):

3771 حَدَّثَنَا أَبُو سَعِيدٍ الْأَشَجُّ، قَالَ: حَدَّثَنَا أَبُو خَالِدٍ الْأَحْمَرُ، قَالَ: حَدَّثَنَا رَزِينٌ، قَالَ: حَدَّثَتْنِي سَلْمَى قَالَتْ: دَخَلْتُ عَلَى أُمِّ سَلَمَةَ وَهِيَ تَبْكِي، فَقُلْتُ: مَا يُبْكِيكِ؟ قَالَتْ: رَأَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ(ص)َ - تَعْنِي فِي الْمَنَامِ - وَعَلَى رَأْسِهِ وَلِحْيَتِهِ التُّرَابُ، فَقُلْتُ: مَا لَكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ : "شَهِدْتُ قَتْلَ الْحُسَيْنِ آنِفًا".

- سنن الترمذي أبواب المناقب عن رسول الله(ص) | باب : مناقب الحسن والحسين(ع) (3771).

- مسند أحمد ( 26524 ).

- التأليف والنشر : الدار العربية لتقنية المعلومات : 2017 : المملكة العربية السعودية - شارع العليا العــام – الرياض – طريق الملك فهد - حي التخصصي. جمهورية مصر العربية – 49 شارع نوبار - باب اللوق - القاهرة.

Kadan daga cikin manyan malaman Ahlus-Sunnah da suka riwaito Ingantattun hadisai akan tabbatar da Sunnancin yin kuka, alhini da juyayin kashe Imam Husain(as):

1. Tabari, a ZAKHA'IRUL UKBA, s 147.

2. IBN HAJAR, a AL-MADALIBUL ALIYA, j 4, s 73.

3. HAKIM NAISHABURI, a MUSTADRAK, j 4, s 389.

4. IBN KASIR, a AL-BIDAYA WAN NIHAYA, j 3, s 230.

5. BAIHAQI, a DALA'ILUN NUBUWWA, j 6, s 467.

6. HAISAMI, a MAJMA'UZ-ZAWA'ID, j 9, s 192.

7. DABARANI, a MU'UJAMUL-KABIR, j 3, s 114. Da sauran manyan malaman Ahlus-Sunnah masu yawan gaske.

Kenan yin kukan kashe Imam Husain(as) Sunnah ne; tunda Annabi Muhammad(saw) ne ya fara yi? kuma kin yin kukan Bidi'ah ne?

DUK WANDA YAYI KUKA AKAN KISAN DA AKA YIWA IMAM HUSAIN(AS) DA IKHLASI; DAN AL-JANNAH NE. INJI AHMAD IBN HANBAL, IMAM AS-SADIQ(AS), IMAM AR-RIDA(AS)...

Ahmad bin Hambal, Tabari, Kanduzi Al-Hanafi... sun ruwaito cewa:

1118 - ﺣﺪﺛﻨﺎ: ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﻗﺎﻝ: ﺭﺃﻳﺖ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ(ر) ﺑﺨﻂ ﻳﺪﻩ: ﻧﺎ: ﺃﺳﻮﺩ ﺑﻦ ﻋﺎﻣﺮ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ، ﻗﺜﻨﺎ: ﺍﻟﺮﺑﻴﻊ ﺑﻦ ﻣﻨﺬﺭ، ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻗﺎﻝ: ﻛﺎﻥ ﺣﺴﻴﻦ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ ﻳﻘﻮﻝ: ﻣﻦ ﺩﻣﻌﺘﺎ ﻋﻴﻨﺎﻩ ﻓﻴﻨﺎ ﺩﻣﻌﺔ، ﺃﻭ ﻗﻄﺮﺕ ﻋﻴﻨﺎﻩ ﻓﻴﻨﺎ ﻗﻄﺮﺓ، ﺃﺛﻮﺍﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ.

"Imam Husain(as) yana cewa; duk wanda ya yi kwalla ko idonsa ya cika da hawaye akan kisan da aka yi mana; to tabbas Allah zai shigar da shi Al-Jannah":

(ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ - ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ - ﻭﻣﻦ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﻋﻠﻲ‏(ﻉ). ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ عبدﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ - ﺫﺧﺎﺋﺮ ﺍﻟﻌﻘﺒﻰ - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 19. ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻴﻮﻣﻲ - ﺍﻟﺴﻴﺪﺓ ﻓﺎﻃﻤﺔ ﺍﻟﺰﻫﺮﺍﺀ‏(ﻉ) - ﺭ ﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 49. ﺍﻟﻘﻨﺪﻭﺯﻱ ﺍﻟﺤﻨﻔﻲ - ﻳﻨﺎﺑﻴﻊ ﺍﻟﻤﻮﺩﺓ - ﺍﻟﺠﺰﺀ : 2 - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 117، 373. ﺍﻟﺤﻀﺮﻣﻲ - ﻭﺳﻴﻠﺔ ﺍﻟﻤﺎﻝ - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 60 - ﻧﺴﺨﺔ ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻈﺎﻫﺮﻳﺔ ﺑﺪﻣﺸﻖ...).

Tabari ya ruwaito cewa:

ﻋﻦ ﻣﻮﺳﻰ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺮﺿﺎ ﺑﻦ ﺟﻌﻔﺮ، ﻗﺎﻝ: ﺳﺌﻞ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ، ﻋﻦ ﺯﻳﺎﺭﺓ ﻗﺒﺮ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻓﻘﺎﻝ: ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﺃﺑﻰ: ﺇﻥ ﻣﻦ ﺯﺍﺭ ﻗﺒﺮ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ‏(ﻉ) ﻋﺎﺭﻓﺎًً ﺑﺤﻘﻪ ﻛﺘﺐ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﻓﻲ ﻋﻠﻴﻴﻦ، ﻭﻗﺎﻝ: ﺇﻥ ﺣﻮﻝ ﻗﺒﺮ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺳﺒﻌﻴﻦ ﺍﻟﻒ ﻣﻠﻚ ﺷﻌﺜﺎً ﻏﺒﺮﺍًً ﻳﺒﻜﻮﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ. أﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺍﻟﻌﺘﻴﻘﻲ.

"Imam Ali Ar-Rida(as) yana cewa; duk wanda ya ziyarci kabarin Imam Husain(as) tare da sani da tabbatar da muhimmancin (Imam Husain(as); to Allah zai bashi Al-Jannah. A kabarin Imam Husain(as) akwai mala'iku dubu saba'in; suna juyayi da kukan kashe Imam Husain(as) har a tashi Qiyama":

(ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ - ﺫﺧﺎﺋﺮ ﺍﻟﻌﻘﺒﻰ - ﺭ ﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 151).

Shaikhul-Mufid, Shaikh Ad-Dusi... sun riwaito cewa:

ﻭﺧﺒﺮ ﻣﺤﻤّﺪ ﺑﻦ ﻋﻤﺎﺭﺓ، ﻋﻦ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ(ع‏)، ﻗﺎﻝ: ﻣﻦ ﺩﻣﻌﺔ ﻋﻴﻨﻪ ﻓﻴﻨﺎ ﺩﻣﻌﻪ ﻟﺪﻡٍ ﺳُﻔﻚ ﻟﻨﺎ، ﺃﻭ ﺣﻖّ ﻟﻨﺎ ﻧﻘﺼﻨﺎﻩ، ﺃﻭﻋﺮﺽٍ ﺍﻧﺘﻬﻚ ﻟﻨﺎ، ﺃﻭ ﻷﺣﺪ ﻣﻦ ﺷﻴﻌﺘﻨﺎ، ﺑﻮّﺃﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺑﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﻨّﺔ ﺣﻘﺒﺎً.

"Imam Ja'afar As-Sadiq(as) yana cewa; duk wanda yayi kuka saboda kisan gillan da cin zarafin da aka yi mana, ko aka yiwa wani dan Shi'armu; to Allah zai saka shi Al-Jannah".

(ﺃﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﻤﻔﻴﺪ : 175. ﺍﻟﻤﺠﻠﺲ : 22. ﺣﺪﻳﺚ : 5. ﺍﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﻄﻮﺳﻲ : 194. ﺍﻟﻤﺠﻠﺲ : 330 : ﺣﺪﻳﺚ : 32).

An ruwaito Imam As-Sadiq(as) yana cewa;

ﻭﺧﺒﺮ ﺃﺑﻲ ﻫﺎﺭﻭﻥ ﺍﻟﻤﻜﻔﻮﻑ, ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ(ص‏)... ﻭﻣﻦ ﺫُﻛﺮ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﻨﺪﻩ ﻓﺨﺮﺝ ﻣﻦ ﻋﻴﻨﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻣﻮﻉ ﻣﻘﺪﺍﺭ ﺟﻨﺎﺡ ﺫﺑﺎﺏ ﻛﺎﻥ ﺛﻮﺍﺑﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ, ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺽَ ﻟﻪ ﺑﺪﻭﻥ ﺍﻟﺠﻨّﺔ.

"Duk wanda yayi kuka har ya zubar da hawaye ko da kwatankwacin fiffiken Sauro ne; akan kisan da aka yiwa Imam Husain(as), to Allah zai bashi Al-Jannah".

(ﻛﺎﻣﻞ ﺍﻟﺰﻳﺎﺭﺍﺕ : 208 : ﺍﻟﺒﺎﺏ : 33 : ﺣﺪﻳﺚ ‏: 297).

Shaikh As-Suduq ya riwaito Imam Ali Ar-Rida(as) yana cewa da Sahabinsa Shabib:

ﻋﻦ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺮﺿﺎ(ع‏)، ﻓﻲ ﺣﺪﻳﺚ: ﻳﺎ ﺑﻦ ﺷﺒﻴﺐ! ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺑﺎﻛﻴﺎً ﻟﺸﻲﺀ ﻓﺎﺑﻚِ ﻟﻠﺤﺴﻴﻦ ﺑﻦ ﻋﻠﻲّ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ(ع) ﻓﺈﻧّﻪ ﺫﺑﺢ ﻛﻤﺎ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻟﻜﺒﺶ، ﻭﻗﺘﻞ ﻣﻌﻪ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ ﺛﻤﺎﻧﻴﺔ ﻋﺸﺮ ﺭﺟﻼً، ﻣﺎ ﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﺷﺒﻴﻪ، ﻭﻟﻘﺪ ﺑﻜﺖ ﺍﻟﺴﻤﻮﺍﺕ ﺍﻟﺴﺒﻊ ﻭﺍﻷﺭﺿﻮﻥ ﻟﻘﺘﻠﻪ... ﻳﺎ ﺑﻦ ﺷﺒﻴﺐ ! ﺇﻥ ﺑﻜﻴﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ‏(ع) ﺣﺘـّﻰ ﺗﺼﻴﺮ ﺩﻣﻮﻋﻚ ﻋﻠﻰ ﺧﺪّﻳﻚ، ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻛﻞّ ﺫﻧﺐ ﺃﺫﻧﺒﺘﻪ، ﺻﻐﻴﺮﺍً ﻛﺎﻥ ﺃﻭ ﻛﺒﻴﺮﺍً، ﻗﻠﻴﻼً ﻛﺎﻥ ﺃﻭ ﻛﺜﻴﺮﺍً.

"Idan har da akwai wani abu da zai iya saka kuka; to ba zai kai kisan gillan da aka yiwa Imam Husain(as) ba, saboda an yanka kan Imam Husain(as) kamar yanda ake yanka kan Rago. An yiwa Imam Husain(as) kisan gilla tare da Ahlinsa 18; a lokacin babu tamkar su a Duniya kacokaf. Duniya da Sammai 7 sun yi kuka akan kisan da aka yiwa Imam Husain(as). Hakika Shabib! Idan har ka yi kuka, ka zubar da hawaye; akan kisan da aka yiwa Imam Husain(as), to Allah ya gafarta maka zubanka kacokaf".

(ﺃﻣﺎﻟﻲ ﺍﻟﺼﺪﻭﻕ : 192. ﺍﻟﻤﺠﻠﺲ : 27 : ﺣﺪﻳﺚ : 202. ﻋﻴﻮﻥ ﺃﺧﺒﺎﺭ ﺍﻟﺮﺿﺎ(ع‏) :2 / 268 : ﺣﺪﻳﺚ : 58).

An ruwaito Imam Husain(as) ya na cewa:

ﻭﺧﺒﺮ ﺍﻟﻔﻀﻴﻞ ﺑﻦ ﻳﺴﺎﺭ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ(ع): ‏ﻣﻦ ﺫُﻛﺮﻧﺎ ﻋﻨﺪﻩ ﻓﻔﺎﺿﺖ ﻋﻴﻨﺎﻩ، ﻭﻟﻮ ﻣﺜﻞ ﺟﻨﺎﺡ ﺍﻟﺬﺑﺎﺏ، ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﺫﻧﻮﺑﻪ، ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻧﺖ ﻣﺜﻞ ﺯﺑﺪ ﺍﻟﺒﺤﺮ.

"Duk wanda yayi juyayin kisan gillan da aka yi mana har ya zubar da hawaye; ko da kwatankwacin fiffiken Sauro ne, to Allah ya gafarta masa zunubansa; ko da zunubansa sun kai yawan Ruwan Duniya".

(ﺍﻟﻤﺤﺎﺳﻦ :1 63. ﻛﺘﺎﺏ ﺛﻮﺍﺏ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ، ﻛﺎﻣﻞ ﺍﻟﺰﻳﺎﺭﺍﺕ : 207 : ﺍﻟﺒﺎﺏ : 32. ﺣﺪﻳﺚ ‏: 293).

Tabbas kuka tare da ikhlasi da khushu'i yana kara kusantar da mai Imani zuwaga Allah(swt).

Allah(swt) yana cewa:

ﻭَﻳَﺨِﺮُّﻭﻥَ ﻟِﻸَﺫﻗَﺎﻥِ ﻳَﺒﻜُﻮﻥَ ﻭَﻳَﺰِﻳﺪُﻫُﻢ ﺧُﺸُﻮﻋﺎً.

"...(da cikin sifar masu Imani shine) sun kasance masu yawan yin Sujada, sannan kuma kukan da suke (yawan yi) yana kara masu tsantsar ikhlasi".

(ﺍﻻﺳﺮﺍﺀ : 109).

UMMUL-MUMININ AISHA TA KARYATA DUK WANI HADISI DA YA HARAMTA YIN KUKA AKAN MUTUWAR WANI MUSULMI. INJI BUKHARI, MUSLIM...

Kuka saboda mutuwar wani musulmi; halas ne da ittifakin dukkan malaman Mazhabobin Musulunci:

ﻓﺎﻟﺒﻜﺎﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴّﺖ ﻧﻔﺴﻪ ﻣﺒﺎﺡ ﺑﺎﻻﺗّﻔﺎﻕ؛ ﻓﻔﻲ "ﺍﻟﻔﻘﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ ﺍﻷﺭﺑﻌﺔ" : "ﻳﺤﺮﻡ ﺍﻟﺒﻜﺎﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴّﺖ ﺑﺮﻓﻊ ﺍﻟﺼﻮﺕ ﻭﺍﻟﺼﻴﺎﺡ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻤﺎﻟﻜﻴﺔ ﻭﺍﻟﺤﻨﻔﻴﺔ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻴﺔ ﻭﺍﻟﺤﻨﺎﺑﻠﺔ : ﺇﻧّﻪ ﻣﺒﺎﺡ, ﺃﻣﺎ ﻫﻄﻞ ﺍﻟﺪﻣﻮﻉ ﺑﺪﻭﻥ ﺻﻴﺎﺡ ﻓﺈﻧﻪ ﻣﺒﺎﺡٌ ﺑﺎﺗّﻔﺎﻕ". (ﺍﻟﻔﻘﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ ﺍﻷﺭﺑﻌﺔ : 2 / 533 : ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻣﺒﺤﺚ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻴّﺖ. ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ : 2 /410 : ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻨﺎﺋﺰ ﻓﺼﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻌﺰﻳﺔ).

Ko da yake akwai wani hadisi da yake nuna rashin halaccin yin kuka saboda mutuwar wani musulmi, har hadisin ya nuna hakan zai iya jawowa mamacin azaba.

Amma Ummul-Muminin Aisha ta karyata wannan hadisin, ta ce Umar da dansa da suka riwaito hadisin sun samu demuwa ne ko mantuwa akan abinda Annabi(saw) ya fada. Ta ce; abinda ya faru shine, Annabi(saw) ya wuce wasu masu jana'izar wata Bayahudiya, suna ta kuka, sai ya ce; ko da suke mata kuka ana mata azaba (kenan ba kukansu ne yasa ake mata azabar ba; ana mata azabar ne saboda laifin da ta aikata ne):

928 ( 23 ) حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ رَافِعٍ، وَعَبْدُ بْنُ حُمَيْدٍ، قَالَ ابْنُ رَافِعٍ: حَدَّثَنَا عَبْدُ الرَّزَّاقِ، أَخْبَرَنَا ابْنُ جُرَيْجٍ... قال عمر: قال رسول الله(ص): "إِنَّ الْمَيِّتَ يُعَذَّبُ بِبَعْضِ بُكَاءِ أَهْلِهِ عَلَيْهِ"

فَقَالَتْ عَائِشَةَ: يَرْحَمُ اللَّهُ عُمَرَ، لَا وَاللَّهِ مَا حَدَّثَ رَسُولُ اللَّهِ(ص)َ : "إِنَّ اللَّهَ يُعَذِّبُ الْمُؤْمِنَ بِبُكَاءِ أَحَدٍ". وَلَكِنْ قَالَ : "إِنَّ اللَّهَ يَزِيدُ الْكَافِرَ عَذَابًا بِبُكَاءِ أَهْلِهِ عَلَيْهِ". قَالَ: وَقَالَتْ عَائِشَةُ: حَسْبُكُمُ الْقُرْآنُ (وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَى)، قَالَ : وَقَالَ ابْنُ عَبَّاسٍ عِنْدَ ذَلِكَ : وَاللَّهُ أَضْحَكَ وَأَبْكَى...

- صحيح مسلم كتاب : الجنائز. | باب : الميت يعذب ببكاء أهله عليه (928 (23), 927, 928, 930, 932).

- صحيح البخاري ( 1286, 1290, 1292, 1304, 3978 ).

- سنن أبي داود ( 3129 ).

- سنن الترمذي ( 1002, 1004 ).

- سنن النسائي ( 1848, 1850, 1853, 1855, 1857, 1858 ).

- سنن ابن ماجه ( 1593 ).

- مسند أحمد ( 180, 247, 248, 264, 268, 288, 294, 315, 334, 354, 366, 386, 4865, 4959, 5262, 6182, 24302, 25079, 25754, 26409 ).

- التأليف والنشر : الدار العربية لتقنية المعلومات : 2017 : المملكة العربية السعودية - شارع العليا العــام – الرياض – طريق الملك فهد - حي التخصصي. جمهورية مصر العربية – 49 شارع نوبار - باب اللوق - القاهرة.

HADISAN DA KE HANA YIN KUKA AKAN MUTUWAR MUSULMI SUN CI KARO DA AYOYIN QUR'ANI, DON HAKA BA YACCE ZA'AYI SU INGANTA KOMAI INGANCIN ISNADINSU:

Abinda zai kara tabbatar mana da cewa kukan mutuwar mamaci baya jawo masa azaba; fadar Allah(swt):

 "ﻭَﻻ ﺗَﺰِﺭُ ﻭَﺍﺯِﺭَﺓٌ ﻭِﺯْﺭَ ﺃُﺧْﺮَﻯ".

"Laifin wata Rai; baya shafar wata Ran". (baya daga cikin adalcin Allah; wani yayi laifi sai kuma ya azabtar da wani daban ba wanda yayi laifin ba).

(ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ : 15. ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ : 164. ﻓﺎﻃﺮ : 18. ﺍﻟﺰﻣﺮ : 7).

A wata ayar Allah yace;

"ﺃَﻟَّﺎ ﺗَﺰِﺭُ ﻭَﺍﺯِﺭَﺓٌ ﻭِﺯْﺭَ ﺃُﺧْﺮَﻯ".

"Sam! Laifin wata Rai baya shafar wata Ran"

(ﺍﻟﻨﺠﻢ : 38).

Sannan kuma Allah ya ce;

"ﻭﺃﻥ ﻟﻴﺲ ﻟﻺﻧﺴﺎﻥ ﺇﻻ ﻣﺎ ﺳﻌﻰ".

"Aikin da mutum ya aikata ne za'a masa sakamako akansa (ba aikin da wani mutum daban ya aikata ba)".

(ﺍﻟﻨﺠﻢ : 39‏).

Wadannan ayoyin sun tabbatar mana da cewa; babu yadda za'a azabtar da mamaci saboda ana kukan mutuwarsa.

Attakaice, kukan juyayin Shahadar Imam Husain(as) Sunnah ce da Annabi Muhammad(saw) ya assasa da kansa. Kuma ladan yin kukan shine Al-Jannah.

اللّهُمَّ العَنْ قَتَلَةَ الحُسَيْنِ (عَلَيْهِ السَّلامُ)!

السَّلامُ عَلى الحُسَيْنِ وَعَلى عَلِيِّ بْنِ الحُسَيْنِ وَعَلى أَوْلادِ الحُسَيْنِ وَعَلى أَصْحابِ الحُسَيْنِ!

أَعْظَمَ الله اُجُورَنا بِمُصابِنا بِالحُسَيْنِ عَلَيْهِ السَّلامُ وَجَعَلَنا وَإِيَّاكُمْ مِنْ الطَّالِبِينَ بِثارِهِ مَعَ وَلِيِّهِ الإمام المَهْدِيّ مِنْ آلِ مُحَمَّدٍ عَلَيْهِمُ السَّلامُ!

بِحَقِّ يس وَ الْقُرْآنِ الْحَكِيمِ وَ بِحَقِّ طه وَ الْقُرْآنِ الْعَظِيمِ يَا مَنْ يَقْدِرُ عَلَى حَوَائِجِ السَّائِلِينَ يَا مَنْ يَعْلَمُ مَا فِي الضَّمِيرِ يَا مُنَفِّساً عَنِ الْمَكْرُوبِينَ يَا مُفَرِّجاً عَنِ الْمَغْمُومِينَ يَا رَاحِمَ الشَّيْخِ الْكَبِيرِ يَا رَازِقَ الطِّفْلِ الصَّغِيرِ يَا مَنْ لَا يَحْتَاجُ إِلَى التَّفْسِيرِ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ افْعَلْ بِنا ما انت أهله بمُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ!

➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post