Wasu bama-bamai sun tashi a kauyen Yammama, dake a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina kuma mutane da dama sun rasa rayukansu.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne a yau Asabar a gonar wani mutum mai suna Alhaji Hussaini Mai Kwai, in da mutane
5 suka rasa rayukan su yayin da aka garzaya da 6 zuwa asibitin Malumfashi da ke jihar.
Wani da abun ya faru a gaban sa kuma ya nemi a sakaya sunan sa yace wadanda suka mutu leburori ne dake yin noma a gonar.
"Na kirga gawawwaki 6 kuma an garzaya da wasu 5 asibiti. Jami'an tsaro sun killace wajen yanzu." Majiyar ta ce.
Da aka tuntubi jami'an yansanda akan lamarin, Jami'in hulda da jama'a na Rundunar Yansandan Jihar, SP Gambo Isaha , yace sun tura jami'an su a wurin da abin ya faru domin gudanar da bincike.
Allah shi kyauta ya kuma kawo mana zaman lafiya mai dorewa
Tags:
Labaran Duniya