In Dai Ana Batun Iya Mu'amala Ne Daga Musulmi, To, Ka Samu Mabiyin Shi'a – Inji Fasto Yohanna Buru



INJI FASTO YOHANNA BURU

"In dai ana batun iya Mu'amala ne daga Musulmi, to ka samu mabiyin Shi'a.
"Shaikh Zakzaky ne ke rike da fitila, idan ya Haske za mu ga waje, idan bai haska ba kuwa za mu ga duhu ne. Muna rokon ka cigaba da haska mana. "Muna rokonka (Shaikh Zakzaky), ka 'Creating Christian Movement withing Islamic Movement'. Rokona kenan. Domin mutumin da duk inda ka ganshi manya da kanana suna girmama shi, ai dole ka bi biyansa."

"In sauran Malamai suna jin tsoro, ku Malam (Zakzaky) mun san baku jin tsoro, don Allah Malam ku sa baki, ku taimake talakawa wajen kawo musu yanci. "Na fadawa Barr Solomon Dalung cewa van taba ganin Organized Movement ba kamar Islamic Movement ba. "Allah bai yi kuskure ba da ya baka shugabancin al'umma (Malam Zakzaky), kuma mu za mu bika bisa hakan. Ka saka mana albarka Malam.

"Muna rokon ku (Musulmi), akwai abubuwa da yawa da bamu gane da addininku ba, kuma baku so mu gane addinin naku, kuma duk wanda ya jahilci addininka ya jahilce ka, duk wanda ya ki addininka zai ki ka, duk wanda bai so addininka ba zai ba zai so ba, wanda bai yarda da addininka ba, ba zai yarda da kai ba. Ba yadda za a yi mu yi rayuwa bisa kyakkyawar Mu'amala in har ba mu san juna ba, ba mu fahimci addinin junanmu ba.

— Inji Pasto Yohanna Buru, a wajen taron cin abincin Sallah, a shekarar 2013 a Husainiyyah Baqiyatullah, Zariya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post