Covid-19: Asiri Ya Fara Tonuwa Game Da Corona

 A wata murya da ake dangantata da Shugaban Kasar Ghana Maici yanzu, ya yi bayani dalla- dalla a gameda makarkashiyar da wasu manyan Masu bautar Shedan dake da kudi tare da kungiyoyin dake mara musu, suka kashe makudan kudi don ai musu wasu muggan aiyuka akan Dan Adam a duk inda yake Yau a duniya.

 Shugaban ya fara ne da fadin cewa wadannan bayanan da zai kawo ya samo su ne daga wata Qasidah da Gidauniyar Rokefeller ta saka a yanar-gizo, inda ta yi hasashen yadda duniya za ta kasance a wannan shekarar ta 2020.

 Wani lokaci yakan kara da fashin bakI daga gareshi.
Wannan qasida ta yi bayanin yadda aka kirkiro wata cututtuka da yadda za a yada su domin su game duniya gaba daya.

 Ta kuma yi bayanin matakan da za abi domin a tabbatar da hakan ya faru, domin su cimma burin da suka dade suna shiryawa don rage yawan al'ummar duniya.

 Matakan kuwa sune kamar haka:

Hanyoyin da za abi
Tsawon lokacin da za a yi
Sakamakon da a ke son a cimma
A mataki na farko

  Abinda za ku yi shine samar da wasu kwayoyin cuta masu saurarin yaduwa da kashe mutane a cikin sauki. To, saboda haka sai suka samar da kwayoyin cututtuka irinsu SARS da HIV da makamantan su.

 Wadannan kwayoyin cututtuka ne wadanda aka kirkirosu a tsakanin shekara 2008 zuwa 2013.

 A mataki na biyu kuwa, shine su yiwa kwayoyin cutar da suka gabata kwaskwarima ta yadda za su zama da yanayi kamar makamin kare dangi, yadda za su sabbaba mace- mace fiye da na farko.

 Kuma su ne dai za a kara yiwa kwaskwarima a mataki na uku na gaba.
Way’annan kwayoyin cututtuka sun kasance a wani dakin gwaje-gwaje da bincike ne a kasar Canada.

 Daga bisani ne wai! China ta sace su saboda wani manufa tata, inda ta kai su wani shahararren dakin bincike da gwaje-gwaje da ke garin Wuhan na China (Wuhan Istitute of Biology). Daga nan sai shine ake zargin China da cewa ita ce ta kara musu karfi sannan ta sake su amma ba da gangan tayi hakan ba.

 Sun biya duk wadanda za su fito su yi magana a duniya, don su taimaka yadda ya kamata ayi kamar dai yadda aka tsaro abin tun farko, irinsu Pauchi da Pedros, da kungiyoyi irinsu Kungiyar lafiya na duniya (W.H.O).
Sun bada damar cewar a kashe kudi sosai don samar da allurar riga kafi (vaccination) a kuma tabbatar da cewa an yi wa kowa a fadin duniyar nan.

 *Bill Gates yana gaba wajen aiwatar da wannan manufa. Ya kuma ba da umarni*
*A kashe kudi a samar da hanyoyi da tsare-tsaren da ya kamata, saboda a tabbatar da cewa kowane mutum a duniya dole ne – yana so ko ba ya so- a yi mashi abinda ake kira “Digital Id” sanya na'urar da za a rika sarrafa dan Adam kamar waya, nan da karshen shekara 2020.*

Sunsa ayi wa mutane kulle (Quarantine) domin hakan shi ne zai kai ga cimma abinda ake so.

 Sun sa an saki kwayoyin cutar daga dakin bincike da gwaje-gwaje na Wuhan, China, sa’annan suka ce a daura lefin yaduwar cutar akan kasuwar dabbobi ta Wuhan a watan November 2019.

 Sun ce kar a sanar da mutane cewa cutar wanda ake iya daukarta ce, a bari a dauki lokaci mai tsawo tukun na don cutar ta yadu sosai a fadin duniya kafin a fara tunanin yin kulle, domin kar jama’a su kaucewa yaduwarta tun da fari.

Hakika wannan shi ya sa kungiyar lafiya ta duniya ta dinga rufe-rufe, inda ta dauki lokaci mai tsawo tana nuna cewa cutar ba wanda mutum kan dauka daga wani ba ne, ba don komai ba sai don cutar ta yadu sosai tukunna a fadin duniya, kafin wata Kasa ta fara tunanin yin kulle.

 Kuma da zarar cutar ta isa wata Kasa, to agaggauta sa ma mutanen kasar kulle a hana su yin tafiye- tafiye, amma a tabbatar da cewa cutar ta ci gaba da yaduwa a wannan kasar lokaci mai tsawo.

 Alokacin da mutane masu yawa suka kamu da cutar sai a tilastawa mutanen yankin sai sun killace kansu, daga nan sai a hankali- a hankali a fadada lamarin, ta yadda za a tilastawa kowa yin kulle.

 A yi ta kanbama yawan mace-mace da ke faruwa, ta yadda duk mutuwar da aka yi a wannan lokacin, to kawai a ce cutar Covid 19 ce. Ba don komai ba sai domin a jefa firgici a cikin zukatan mutane.

 A tabbatar da an bar mutane a cikin kulle na lokaci mai tsawo, domin a rugurguza tattalin arzikinsu.

 A samar da rashin kwanciyan hankali ga mutane, da karancin kayan abinci, kuma a raunana tsarin garkuwan jikinsu ta hanyan hanasu haduwa da juna.

 Hakan na nuna cewa in dai muna son garkuwan jikinmu ya yi karfi to ya kamata mu fita mu rika haduwa da mutane.

 An tsara cewa aci gaba da yiwa mutane kulle bayan kulle. A takura yadda mutane za su yi fito na fito da jami'an tsaro donsu kalubalance su.

 A lokacin da mutane suka kai bango, sai ku kai karshen matakin farko na kullen a wuraren a cikin watan shida (june 2020).

 A lokacin da mutane suka dawo rayuwarsu yadda suka saba a baya, a jira su kadan ‘yan satuttuka sai aci gaba da kanbama yawan mace- mace da ke faruwa a wuraren watanni na takwas da na tara (August-Sept).

Ku ma hada harda mace-macen daba na Covid 19 ba ace shi ne.

 Daga nan sai a kara dawo masu da kulle ta yadda za a takura su sosai fiye da yadda a takura su a baya, kuma a daura laifin faruwan haka akan taurin kan da mutane ke yi, wanda hakan ya sa a ka kara dawowa halin da ake ciki.

 Sa’annan a kara tsanantawa, wurin ladabtar da masu fito na- fito da dokar kulle.

  A bar mutane a cikin kulle na lokaci mai tsawo fiye da kowanne lokacin da ya gabata a matakin farko na kulle.

 A ci gaba da rugurguza tattalin arzikin kasashen duniya da jama'a.

 Ayi maganin duk wanda ya yi taurin kai ya ki bin abinda aka ce, ta yadda za a nuna shi a matsayin makiyin al'umma wanda yake son yaduwar cutuka a cikinsu.

 Bayan kullen ya yi tsawo, sai a zo da tsarin Allurar rigakafi/Vaccination, ta yadda za a maida shi ya zama dole akan kowa da kowa.
Duk kuma wanda bai yadda an yi mashi wannan allurar ba, to ba shi ba shiga sabon tsarin duniya New World Order.

 Idan mafi yawancin mutane suka yadda akai musu rigakafin to ‘yan kadan din da ba su amince ba sai a hana su damar yin aiki ko yin tafiya wani wuri ko wata kasa a duniya.

 *Amma idan mafi yawan mutane suka ki amincewa a yi masu allurar, to anan, sai a sakar musu da kwayoyinn cututtuka wadanda aka maida su makaman kare dangi dinnan ta yadda za su iya gamawa da kashe sama da talatin bisa dari na mutanen duniya, domin ya zama shine abu na karshe da za a tsorata mutane da shi.*

 *Daga nan, sai a shiga sabon tsarin duniya, da sabon tsari na kudi wanda zai rika amfani da bayanai da aka saka a jikin mutum.*

 *Daga nan shike nan duk wanda ya mika kai ya yi biyayya ga sabon tsari sai a sakar mashi a yi da shi, wanda kuma ya yi taurin kai a kashe shi.*

Wannan shine takaitaccen sakon da wannan murya yake take dauke da shi tare da fatan wanda ya sami wannan sakon zai tura wa sauran ‘yan uwa don sanin sharrin da aka kullo musu ta hannun hukumominsu da kungiyoyin sharri iri iri na duniya.

 Sai a nemi mafita a wajen Allah ta hanyar dena cin kudin da bai halatta ba da yawaita istighfari wato tuba da shirin fuskar duk wanda ya nemi yiwa mutum allurar maida mutum tamkar na'ura a hannun makiyan Allah. Muna gargadi ga jami'an tsaro da shuwagabanni cewa su sani in sun gama biyawa iyayen gidansu bukata suma za a dawo kansu.

 Allah ya rayar da mu a cikin imani ya azurta mu da mutuwar shahada don rahmarshi da jikanshi. Amin amin.

 Note! Mafitar mu anan Nigeriya shine Amsa Kiran Sayyid Zakzaky (H) ne! Kiransa don tabbar da adalci da zaman lafiya ne! Ba yana qira akan aqida bane ba! Mu amsa Masa kowa ya samu damar yin aqidar da yake so cikin nutsuwa da kariya! Mu kori 'yan koren Turawa Azzalumai da suke zaluntarmu!

 Amsa masa shine mafita garemu! Wallahi za a dabbatar da adalci kowa za'a bashi hakkinsa Kuma za a zauna lafiya! A samu rayuwa mai kyau! Da zaman lafiya!!!

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post