Dokar Zaman Gida :- Akwai yiyuwar su fara bude wuta a Katsina


sheikh yakubu yahaya katsina


_Inji Shaikh Yakub Yahya Katsina, a wani takaitaccan jawabi da yayi bayan Kammala karatun Tafseer na jiya Litinin 19/10/1414, 11/05/2020 kan makircin azzalumai a Katsina da ma kasa baki daya, asha karatu lafiya..._
"Wadannan mugayan mutanan da ke addabarmu suke addabar mutane a gari marasa hikima, marasa basira wadanda Allah ya dode basirar su da sunan yaki da wata corona ko wani abu mai kama da haka. Ina jin dan tsakanin nan zasu kara kaimi, ko ma sun fara dan abinda nake ji kenan cewa; zasu fara shiga lunguna inda ake sallar tarawihi sun ma ambaci irin Masanawa da sauran wurare cikin lunguna inda ake yin tarawihi, saboda suna ganin cewa an raina gwamnati saboda haka akwai yiwuwar ma su bude wuta, Eh! akwai yiwuwar su bude wuta.
Zasu dauki tsattsauran mataki tun da an raina gwamnati, ance a zauna gida an ki zama. Wani daga cikin su na cewa; yanzu wadannan motocin da aka basu da alawus din da suke samu fa kudadan mai da sauransu... Shi ke nan yanzu sai a koma ace ba wannan babu to a kashe mutane in yaso... Kuma duk gasu zaune wasu na shan giya wasu na cin naman kaji babu mai azumi, amma suna bugun masu azumi, ga mutane ana kashewa kasa da kilomita 15 da Katsina, wasu kilomita 20, wasu kasa da haka nan wajen bakiyawa dinnan... Ana kashe mutane ana kwashe dabbobi nan kuma suna bugun mutane a cikin gari.
Watau kamar ita wannan corona ta Najeriya ta daban ce, ita akwai wani abu karkashin ta (akwai abinda ake so a cimmawa karkashin ta). Sannan sunji labarin a kauyuka ana yin juma'a, mutum yakan biya 100, 200 a dauke shi kan babur a kaishi wani kauye yayi sallar juma'a ya dawo, shima zasu dauki mataki a masallatan juma'a din. Saboda haka zasu shiga lunguna kuma akwai yiwuwar zasuyi kisa.
Yawwa da kuma taron jana'iza da taron zaman gaisuwa, shima zasu hana har sun kawo misali da rasuwar Allahaji Mai Nasara, sun ce; Matan Fada ya rasu kuma anyi taro mai yawan gaske to ba zasu kara bari ayi irin wadannan tarukan ba. Dama ina gaya maku shi kafirci bai bari akan abinda yake so, saranda kawai yake so, yace eh! Kace eh! Yace a'ah! Kace a'ah! Shi ke nan kawai kai baka da maslaha sai shi. Alhali Kuronar nan har yanzu bata kashe mutum 100 anan ba (har yanzu) to amma da alama kafin a gama kuronar nan sai sun kashe dauruwa saboda suna samun kudi, magana ce ta a samu kudi illa iyaka.
In da gaske ne ana kare jama'a ne kuma ana son mutane kuma na son lafiyar su wanda duk aka maida gida a kai masa abincin da zai ci na tsawon kwanukan da aka hana sa fitowwa neman abincin sa wannan shi ne adalci, kuma shi ne dai-dai. Sannan ya zamana mutane suna da 'yanci na walwala bakin gwargwado amma sai na ga kamar ko an fi karfin shi gwamnan ne? Ni haka nake fahimta kamar ma'aikar tsaron kasa ta kwace 'program' din. Saboda haka zasu yi ba sani ba sabo kuma zasu yi hauka saboda haka mutane su taka a hankali kuma suyi abinda ya kamata, kada su bada dama aci mutuncin su aci zarafin su ko wulakanta su illa iyaka, sai kuma addu'a, abinda zamu fada kenan.
Mutane su dukufa da addu'a yanzu mu muna bala'i kala 3 ne ga bala'in mahunkunta, ga na kurona ga kuma na yunwa. Ko da yake ita Najeriya (yadda ni na fahimta...) duk kasar da zata biya bashin kurona to Najeriya sai taa nunnunka sau ukku, Kun san dalili?... Awwalu shai'in sai an cire wa Malam Zakzaky (H) hakkin sa (Alhakin Malam) duk abinda zai samu al'ummar nan sai alhakim Malam ya biyo baya akan mahunta da kan masu murnar abinda akayi ma Malam, wanda suka yi farin cikin abinda akayi Malam (H) da wadanda suke ganin ba laifi bane abinda akayi ma Malam da almajiran sa wannan alhakin ba zai barsu ba (1) kenan.
Abu na (2) madarar zalinci da ake yi, Ah! Ai Nijar, Kamaru, Gana, Chadi...ba tsarin zalinci ke hukunci ba? Shin sun kashe talakawan su? Sunje sun bude wa Malamai wuta? Sun kashe bayin Allah? Sun kashe wata harka ta Addini? Sun rushe makabarta, Masallaci, sun tono kaburbura? Sun kwashi maza da mata sunje sun rufe da rai sun masu jana'izar bai daya? Duk sun yi haka? Shi yasa kurona kawai suke da matsala da ita. Nan kuwa sai an biya farashin zalintar Malam, za a biya tsabar zalinci sannan za a biya fandare ma Allah da yaudarar Allah da akayi. Saboda haka ya kamata dan Najeriya ya shirya ne ya biya farashi...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post