Jinjina ga ƴan Struggle, mabiya Malam Zakzaky na haƙiƙa – Abba Gano








ai hausawa sunce yaba kyauta tukuici, to tabbas muna jinjinawa ƴan Abuja struggle bisa irin dakewar da sukai wajan sauke wajibin kansu.

Tabbas duk wanda ya taɓa zuwa Abuja ko sau ɗaya ne ya cancanci a jinjina masa, saboda cire tsoro, yayi ya tun kari azzalumai har matattarar su!!!

To idan anyi jinjina ga waɗanda suka je sau ɗaya' to yaya wanda kuma can yakoma yatare!! Shin akwai wata kalma dazaka iya faɗa ta yabo da jinjina gareshi ? Tabbas komi zaka faɗa ya huce Wannan!!!

Duk dayake, idan muka duba matsayin haƙƙin Sayyid akan mu, to lalle muna iya cewa basu yi abinda yada ceba, domin da'ace akwai abinda yake sama da bada rayuwa to da itama ƙila bata kai matsayin haƙƙin jagora akan mabiyan saba.

Amman sauraron yadda su Sayyid da kansu suke jinjinawa waɗan nan tsayaiyuwan da suka dake, yasa muma zamu samu bakin dazamu jinjina musu, kodan ƙara musu ƙarfin gwiwa.

Tsayuwar su akan abinda yadace akan lamarin jagora tabbas ya cancanci ayi musu jinjina!!!

Shiru da hakuri da sukai na Maganganun mutanen gari shi kansa hakan jarumta ce, kuma sun cancanci jinjina.

Sannan sukai burus da surutun wasu wanda basu fahimta ba daga cikin ƴan uwa' kuma sukai musu uzuri, har suka fahimta yanzu,nasan wannan ma abin jinjina ne!!!

Cire tsoron da sukai wajan tunkarar azzalumai, tabbas wannan babbar jarumta ce da sun cancanci jinjina mai girma.

Haka nan sun bada lokacin su da dukiyar su duka akan Sayyid wannan ma' abin a jinjina musu ne.

A struggle mutum yana iya wuni, batare dayasa wani abu Abakin saba.

A struggle matum yana iya kai azumi, yasha ruwa kaɗai batare da yasamu abin shan ruwa ba.

A struggle mutum yana iya share kwanaki batare da kuɗi wanda zai biya bukatar sa.

A struggle mutum yana iya rasa sabulun wankin dazai wanke kayan sa, amman haka suka dake.

Maganar gaskiya sun cancanci jinjina.

 وَالَّذِينَ آمَنُوا وَهَاجَرُوا وَجَاهَدُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ وَالَّذِينَ آوَوا وَّنَصَرُوا أُولَٰئِكَ هُمُ الْمُؤْمِنُونَ حَقًّا ۚ لَّهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka yi hijira, kuma suka yi Jihãdi, a cikin hanyar Allah, kuma da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi tamiako, waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya, sunãda gãfara da wani abinci na karimci.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post