COVID-19: NECO ta karyata rade-radin cewa za ta dage jarrabawar BECE da SSCE

- Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) ta musanta labarin dage jarabawoyin daliban aji uku da na aji shida na sakandire - Kamar yadda shugaban fannin yada labaran hukumar ya sanar, suna lura da halin da kasar ke ciki ne kafin daukar mataki

- Hukumar ta bayyana cewa ta dage jarabawar masu kammala karatun firamare don shiga sakandire ta shekarar 2020 Hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ta musanta rade-radin dage jarabawoyinta da ake yadawa sakamakon barkewar annobar coronavirus a kasar nan. A wata takarda da shugaban fannin yada labarai da hulda da jama'a, Malam Azeez Sani ya fitar,

ya ce hukumar ta bayyana cewa jarabawar masu kammala firamare kadai ta dage. Ya ce labarin dage jarabawoyin da suke yawo a kafafen sada zumuntar zamanin duk na bogi ne kuma ba gaskiya bane.

Ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da labaran marasa tushe balle makama. Ya ce, "Hukumar ta duba sauran jarabawoyin masu kammala aji uku da kuma aji shida na sakandare amma tana tantamar dagesu a halin yanzu." Ya kara da cewa, "Ana kira ga daukacin jama'a da su yi watsi da labaran bogin don hukumar na lura da abinda ke faruwa a kasar nan, kuma za ta sanar da matsayarta idan da bukatar hakan."

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NECO ta dage rubuta jarabawar kammala firamare na 2020 a ranar 24 ga watan Maris. "NECO na sanar da masu rubuta jarabawa, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki cewa ta dage jarabawar NCEE har sai yadda hali yayi," A cewar takardar. "Wannan hukuncin ya biyo bayan kokarin gwamnatocin tarayya da na jihohi ne wajen ganin an shawo kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, in ji hukumar.
KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post