Bana yi muku fatan alkhairi (Shugabannin Nigeria) –Cewar Wani Matashi



© Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Bansan sanda zuciyata tazama haka ba, amma idan nayi la'akari da yanda zuciya ke son mai kyautata mata sai inga ba laifina bane, ashe an halicci zuciyar ne a haka.

Ni talakka ne mai shekarun da basu kasa Ashirin da takwas zuwa talatin ba, bisa ga ƙaddara na tsinci kaina a wata ƙasa da ake kira Nigeriya.

Ƙasa mai arziƙin ƙarkashin ƙasa, ƙasa mai arziƙin yawan'al'umma wadda akema kirari da uwar Afrika, ƙasar da turawan Ingilishi sukayi ma mulkin mallaka, suka azabtar suka bautar.

Kuma daga bisani suka bata 'yancin jeka nayika, badan sun gaji da bautar da 'yan ƙasar ba bakuma don ƙarfin mu ba sai don yarda da imani da manufofin su.

Yanzu sunkoma suna mana mulkin mallaka ta biro da takarda, saboda tsananin samun waje ma har takaiga gayyato wasu ƙasashen kawaye na kusa da Ita Ingilishi ɗin irin su Amurika da Isra'el suma su shigo ƙasata domin taya Ingilishi mulkarmu.

 Amma don rashi sanin minene 'yanci wai saikaga 'yan'uwana talakawa suma har biki suke idan ranar ɗaya ga watan goma na shekara bature yakama, wai wan'nan itace ranar 'yanci.

Haƙika talakkawan ƙasata suna da haƙuri kuma suna da saurin yarda, Inba haka ba, ta yaya za'azo ayimana Biriboko kuma munji mungani munyarda munyi imani da cewa shine mafita.

Alokacin da mai jan kunne yazo ƙasar nan ya ya Iskemu da Addini da tsarin gudanarwa (siyasa) irin ta addinin mu, kuma yalura sosai yaga cewa lallai namu tsarin yafi nashi.

Sai ya zo yayi mana baba rodo, gami da ƙarfin makami ya rabamu da addinin mu, ya cuso mana nashi, ya rabamu da siyasar mu ya cuso mana tashi, wadda har yanzu itace muke akai.

Agefe guda kuma mu musulmi sai yayi ƙoƙarin janye mana littafin mu na dokokin Allah, abinda Allah keso da abinda yayi hani da kuma yaya zamu rayu, yaya zamu mutu da imani, sai ya danƙara mana nashi, wanda ke cike da kusakurai saɓanin na rabbil'izzati.

Mu musulmi munada ilimin addini, munada hanyar da muke isar da saƙo ta hanyar rubutu da sauran su, bamu dogara da ilimin da bature yazo mana dashi ba dama munada namu.

Mai jan kunne yacimu da yaƙi ta kowane ɓangare, bama kamar wan'nan tsinanniyar matar da ya ɗaura mana Auren zobe da ita(Dimokuraɗiyyar) Ita wan'nan mata tayi tasiri sosai harma ga imanin mu.

Har ta kaiga muna ganin cewa idan baka yinta kamar kai ba musulmin ƙwarai bane, har ma malaman mu suna bada fatawa cewa yinta yafi sallah, sallah fa ita ce marabar kafiri da nusulmi.

Amma kayi, wan'nan tsarin da mai jan kunne yazo dashi yafi kayi Addinin da zaka tsira duniya dalahira, wan'nan wane irin tasiri ne, wagga mata tayi azuciyar ɗan ƙasata?

Duk'wan'nan burunguɗumar da hauragiyar, ta shiga zuciyar talaka ne da taimakon malaman da kai tsaye zaka iya kiransu da malaman turawan mulkin mallaka, waɗanda suka saida lahirar su da lahirar mabiyan su, sai tsiraru da Allah ya tsare.

Bature yabar ƙasata a zahiri Amma a baɗini yanzu yake cikinta. Banason in tsawaita da na kawo yanda bature ya shigo da yanda yafita azahiri da kuma irin abinda yadasa bisa yarjejeniya zaunanniya wadda kuma itace har yanzu jahilan 'yan siyasar mu kebi.

Kamar yanda na faɗi bature mai jan kunne ya kawomana matar da yakeso mu Aura kuma munji mungani mun aura, kuma muna tsananin sonta har gobe, Amma shin tambaya?

Ita wan'nan mata tacika shariɗɗan da yakamata mu musulmi mu Aura domin zama da ita?     

Hadisi ya Inganta daga Annabi ﷺ yace: "(Ana auren mace ne saboda abubuwa hudu,don dukiyarta ko Nasabarta ko kyawonta ko addininta, Annabi(S) yace Na horeku da ma'abociyar Addini, (za ka wadatu da ita)

Shin ita wan'nan matar(Dimokuraɗiyyar) da muka aura shin munbi shawarar ma'aiki? S.A.W

Babu mai morewa rayuwar aure sai wanda ya bi umarni da shawarar Manzon Allah wajan zabar matar aure,wato ka zaɓi mai halin kirki

Ma’abuciya addini mai halin kwarai mai tarbiya,mai sonka saboda Allah.

Amma dukkan wanda yabi son ransa da kwadayin duniya da son ƙawar duniya wajan zabar macen aure yaƙi bin shawarar Manzon Allah,to yayi Asara kuma zai ga sakamakon abinda ya zaba na wulaqanci da nadama.

Mun aje saƙon Allah da ma'aiki munbi ƙawa zuci mun Auri Dimokuraɗiyyar ba ingiliya, wadda mai jan kunne ya ƙawata da zalunci ƙeta tauye haƙƙi, da danne raunana tayaya bazamuga zilla da ƙasƙanci da wula ƙanci ba?

Bayan tsarin Dimokuraɗiyyar a ƙasar nan munbi, wani tsari na na mulkin mulukiyyar soji mun ɗanɗana azaba kuma munyi danasani. Amma maimakon mujuya ga shawarar Ɗangata Mohammad rasulillahi(S.A.W) sai mukace a'a musake komawa mu auri bazawarar nan da muka saki, ƙila yanzu tayi hankali ta ɗanɗana zaman gida.

Abinda muka kasa ganewa shine? Shi hali zanen dutse ne, bayan haka kuma zamanta gida yasanya ta ƙara ɗaukar sabon salo na cutatawa 'ya'yanta agefe guda kuma jawarci ya samu ƙarɓuwa tayi mai tayi bilicin zawarawa(manema) sunganta duk sun ruɗe sun manta da mugun halin ta.

Ƙarshe dai kafin subada sadaki a ɗaura Aure saida tasake azamasu miyagun sharuɗɗa kuma sukaji suka gani suka karɓa, suka Aureta lokaci ɗaya ta canza masu hali suka zama iri ɗaya, dama wani mawaƙi yace idan so ya daɗe yana aiki, kamanne sai suzam iri ɗaya ne.

Kuma lokaci bayan lokaci Dimokuraɗiyyar tana Updating ɗin mazajen nata da mugun halin da take ta naɗa a kullu yaumin daga bature mai jan kunne, shi yasanya duk sanda zatayi sabon ango sai yazo da nashi sabon salo, na mugunta ƙeta da cutatama 'yan ƙasa mabiya. San'nan kuma su waɗanda suka halittata zata kwashe kakaf arzikin da ta tarar ƙasar da take Aure ta kaimasu tabar 'yan kasa da yunwa.

Wan'nan muguwar bazawara a ƙarƙashin jagoranci sabon angonta, ta cutatama talakka, cutatawar da tunda maijan kunne ya halicce ta bata taɓa yimasa irinta ba, kuma ankai maƙura su kansu angunan nata sunrasa wace irin ƙeta yakama suyima talakka?

Hanya ɗaya shine taci gaba da kisan talakkan, ta kowace hanya, kama daga kisan kai tsaye, idan nace kisan kai tsaye ina nufi akasheka da bindiga ko da bom,ta hanyar ƙirƙirarrar ƙungiyar Boko Haram, dakuma kisan ƙarƙashi ƙasa, shikuma yanada hanyoyi dayawa, kama daga karya tattalin arziƙin talakawa ta hanyar jefa masu talauci da gangan, shima ta hanyar ƙirƙirar haramtattun ƙungiyoyin garkuwa da mutane domin amsar kuɗin fansa, da sauran su.

Bugu da ƙari kuma ga cututtukan da suka ƙirƙira kuma suka shiga cikin inwar cutar suna ƙaƙabama talakawa takunkumi kala kala, a yayinda suda 'ya'yan su suke yanda sukaga dama saboda takunkumin bai shafesu ba.

Duk'a ƙarkashin inwar Dimokuraɗiyyar sun kulleni gida sun hanani abinci, suna azabtar dani da yunwa, gashi ban ajeba ban bawani ajiya ba, ballantana insiya da kuɗina, inma inada kuɗin sunhana ɗan uwana talaka ya fito ya kasa ɗan dankali ko rogo balle in siya insama bakin ambaton ma'aiki.

Wallahi bani ƙaunarku banayi maku fatan Alheri bakuma yin kaina bane kune kukaja zuciyata ta zama haka haka, saboda bakwa kyautata min, kasheni kuke, yunwatar dani kuke, kunhana ni nafito na nemi abinci, kun sakar mani cuta.

Amma Alhamdulillah tunda ƙaiƙai yana komawa kan masheƙiya, fatana anan shine Allah yasanya cutar taita kasheku.

Kaikuma talakka tunda kajaraba tsarin mulkin soji, azaba, An ƙaƙabama mu Dimokuraɗiyyar shima azaba, mizaihana kakomoma tsarin Allah da manzon Allah, tsarin da zai 'yantar daki daga bauta, tsarin da zai sa kasan ciwon kanka, kagane macucin ka da macecin ka?

Dafatan Allah(T) ya ganar damu, ya taimakemu Allah ya nuna mana ƙarshen zalunci da Azzalumai. Wasallahumma Ala rasulillahi wa'ahlibayt.
 
© Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post