Tambaya: Wacece tafi kowa yawan hadisai cikin Ummuhatul-Muminin???



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Da shike tarihi ya kawo cewa fiyayyen halitta (S.A.W.W)ya auri mata 12 a rayuwarsa, wasu daga cikinsu sun riga shi yin wafati, wasu kuma sunyi wafati shekaru kadan bayansa, yayin da wasu suka dade kafin suyi wafati a bayansa.

Za mu ambaci 4 ne daga cikinsu, domin su suka fi nisan kwana yadda za a ruwaito hadisai daga gare su.

(1) Ummul muminina A'isha:- Ta zauna da Manzon Allah (S.A.W.W)tsahon shekaru 14, kuma ta rayu bayansa tsahon shekaru 35 ta rasu tana da shekaru 58.

An ruwaito hadisai 2210 daga gare ta.

(2)- Ummul-muminina Hafsat:- Ta zauna da Manzon Allah (S.A.W.W)tsahon shekara 7 da wata 6, ta rasu bayan wafatin Annabi (S.A.W.W)da shekara 38, wato A'isha ta riga ta rasuwa da shekara 3 kenan.

Cikin tsahon rayuwarta an riwaito hadisi 60 ne kadai.

(3)- Ummul-mumina Ummus-Salama:- Ita kuma ta rayu da Manzon Allah (S.A.W.W)tsahon shekaru 8, kuma ta rayu tsahon shekaru 50 bayan wafatin Ma'aiki (S.A.W.W), kenan ita tafi sauran nisan kwana.

Sai dai tare da wannan tsahon rayuwar da tayi an iya riwaito hadisa 328 ne kacal daga gare ta.

(4)- Ummul-muminina Zainab Bnt Jahash, ta rayu da Manzon Allah (S.A.W.W)ne tsahon shekaru 5 ko 6 ko 7 bisa bambancin riwaya.

Kuma ta rayu bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W.W)tsahon shekaru 11.

Amma tsahon wadannan shekaru 11 da tayi kafin wafatinta an iya ruwaito hadisai 10 ne daga gare ta.

          TAMBAYA

Idan aka ce tsahon shekaru bayan wafatin Annabi (S.A.W.W)ke taimakawa wajen samun yawan hadisai daga wanda ya rayu da shi, to, me yasa hadisan wacce ta shekara 50 ya taqaita iya 328, yayin da aka samo 2210 daga wacce ta rayu tsahon shekaru 35?

Kada ku manta, idan dadewa tare da Annabi (S.A.W.W)kuma ke sa afi yawan hadisai, to, me yasa aka ce Abu Huraira ya fi kowa yawan hadisai alhali shekaru 2 kacal yayi tare da Ma'aiki (S.A.W.W)?

‘’ FAS-ALUU AHLUZ-ZIKRI IN KUNTUM LAH TA'ALAMUUN.‘’

Tare da Ado Isah Guda.

         09039791509

~11th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post