YADDA IMAM ALI YA SAMO SUNANSA!!!!!

YADDA IMAM ALI (A.S)YA SAMO SUNANSA !!!

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Wakilnmu ::Ammar Abubakar shadow

ALLAH NE YA RADA MASA SUNA DA KANSA (S.W.A)

Yayin da mahaifiyarsa ta fito da shi daga dakin ka'abah bayan kwana 3, sai ta hadu da mijinta Abu 'Dalib (A.S). Ya karbi dan nasa cikin farin ciki , sannan yake tambayarta cewa akwai sunan da tasa masa ne?

Sai tace, ‘’ ASAD ‘’ (sunan mahaifinta kenan). Sai ya nuna rashin amincewa da wannan suna, maimakon yardar sai yace su nemi taimakon Allah kan wannan,suna na jaririn da suka samu.

Sai suka tafi zuwa dutsen Abu Qubais, a wata riwaya kuma zuwa Masjidil-Haram, wato (Ka'abah). Yayim da suka isa wannan guri dare ya riga yayi, sai shi Abu 'Dalib yayi addu'ah yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ YAA MAHALICCIN WANNAN DUHUN DARE DA WATA MAI HASKE, KA SANAR DAMU NUFINKA AKAN SUNAN WANNAN 'DA .‘’

Sai suka ji murya daga sama, sai Abu 'Dalib (A.S)ya daga kansa sama, sai yaga wani korem,abu zagayayye da rubutu,layi hudu (4)a kai, sai ya dauka,ya duba ya karanta, sai yaga wasu kalmomi kamar haka;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ NAYI MUKU KARRAMAWA TA MUSAMMAN DANA BA KU TSARKAKEKKEN 'DA, AN BA SHI SUNA ‘’ ALI ‘’ DAGA UBANGIJI , WANDA AKA SAMO DAGA ALI .‘’

Daga nan sai Abi 'Dalib (A.S)ya fadi qasa yayi sujadah yana godiya ga Allah (T), kuma ya yanka Raquma 10 a matsayin walima ta lokacin nasu.

Wannan koren abin kuma ya lanqaya shi a jikin ka'abah , har zamanin Hajjaj Bn Yusuf da suka yi yaqi da Abdullahi Bn Zubair sannan aka bata shi.

-YANABI'UL-MAWADDA, BABI NA 56.

-KIFAYATUL-'DAALIB.

MADALLAH DA WANNAN ZABIN SUNA DAGA ALLAH !

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        08137925034

~28th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post