Sheikh Zakzaky: Lokacin samartaka, lokaci ne na Ibada



@Ma'asumah Nigerian News Update@


"Kar wani ya rudu da cewa sai ya tsufa zai yi addini. Da yawan mutane suna tunanin nan gaba zasu yi addini. Su yi ta karatun Alkur’ani da sallar dare, da addu’o’i idan sun Tsufa. To idan ka ji wannan na shiga a ranka, Shedan ya yi maka wahayi. Lokacin da ake da karfi ne ake ibada. Idan ka Tsufa ba zaka iya ba. Lokacin da kake jin karfi lokacin Mujahada ke nan. Lokacin sallar dare ke nan. Lokacin karatun Alkur’ani ke nan. Lokacin da zaka iya yi ke nan. Idan ka Tsufa ba zaka iya ba. shi ne kuma zai sa a rubuta maka ladan abin da kake yi lokacin da kake da karfi. Don rashin karfi ya hana ka yi. Amma dama idan baka yi, sai ka Tsufa ka kasa, shi ke nan baka da wani lada. Amma dama idan kana yi lokacin da kake da karfi, sai Tsufa ya kama ka baza ka iya ba, shi ke nan sai ladanka ya ci gaba. Yanzu lokaci ne na Mujahada.”*

-Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) a taron matasa da aka gabatar a shekarun baya.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post