Rusa Daular Shehu Dakafa Nigeria 🇳🇬 (2)



- Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) / @Bormi 2013

*BAMBANCIN ‘STATE’ DA ‘NATION’*

Akwai abin da ake ce ma al’umma, akwai abin da ake ce ma Kasa. Da Turanci ‘Nation’ da ‘State’. Wato akwai kasa (state), akwai al’umma (nation). Wadannan kalmomi wdand ake ‘idilakinsu’ a kan gungun mutane da kuma sashe na al’umma ya zama sanannen abu, don ana amfani da su yau da kullum domin bayyana al’ummu da kasashe.

Abin da ake ce ma al’umma sune mutanen da suka tara tarihi iri daya, da al’ada iri daya, suke Magana da harshe iri daya, suke da addini iri daya. Su ake ce ma al’umma (nation).

To, kuma kasa (state) yanki ne da yake da kan iyakoki wanda tana iya yiwuwa al’umma ta zama tana zaune a ciki. Har ma suna ba da misalin cewa ‘kasa ba lallai ta zama sun yi daidai da al’umma ba. Yana iya yiwuwa a samu kasa bata da al’umma, yana iya yiwuwa kuma a samu al’umma bata da kasa.’

Alal misali, akwai al’ummar Palasdinu wanda yanzu aka kwace kasarsu aka kafa Isra’ila. Yanzu kasar ana ce mata Isra’ila ne, ba a ce mata Palasdinu. Ko an ce mata Palasdinu to dai Isra’ilawa ne suka mamaye wajen su ke rike da wajen, saboda haka an mai da Palasdinawa al’ummar da bata da kasa.

To, ga wannan ‘ta’arifi’ na meye ma’anar kasa, meye ma’anar al’umma? Na san in muka ce kasa ba wani matsala dangane da gane me ake ce ma kasa, tunda yanzu ga sunannaki wanda ko mutum bai yi karatu ba ya sani ana cewa Nijeriya, Nijar, Kamaru, Chadi, Sudan, Misira da sauransu duk kasashe ne wanda suke da kan iyaka. Akwai kan iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar. Wannan kasa ce, wancan kasa ce.

*NIGERIA KASA CE MAI AL’UMMU*

To amma mece ce al’umma? Idan muka koma ta’arifin al’umma kamar yadda muka ce, sune ‘gungun mutane masu asali daya, harshe daya da addini daya.’ In wannan shine ‘ta’arifin’ al’umma to za mu ga cewa Nijeriya kasa ce me al’ummu. Amma akwai wata al’umma sunanta al’ummar Nijeriya?

Idan kace mutane masu asali daya, harshe daya, addini daya, in shine al’umma, Nijeriya al’umma ce? (A’a). Amma Nijeriya kasa ce? Eh kasa ce mai al’ummu. To, al’ummun nan sunansu al’ummar Nijeriya? In kace ‘Eh’, to ta’arifin al’umma ya wargaje. Ya nuna kace idan aka samu ksa koma yaya aka samu kasar to wadanda suke zaune a kasar sunansu al’ummar kasar.

ASALIN MA’ANAR KASA DA KUMA AL’UMMA

Wannan ‘ta’arifi’ na kasa da al’umma wani abu ne da ya yo asali daga Turawa, wanda su a kasarsu haka suke zaune. Sun zauna tun suna maguzawansu kafin addinin Nasara ya je musu, suna zama ne irin na ‘nizamin’ kabilanci, wanda yake kowace Kabila da inda take zaune. Har yanzu kuma Turawa basu rabu da wannan nizami na kabilanci ba, har yanzu akwai masu da’awar kyamar baki, da cewa su kasarsu tasu ce kawai.

Daga nan wannan abin ya yi asali, suka kafa al’ummarsu a kan asasin al’ummu, ko da yake basu da abin da suke ce mishi kabila, domin abin da ake cewa kabila sune mutanen da suka hada asali guda, suna cewa mu yayan wane ne, shine Kabila. Kabila tana zama Kabila ne in mutanenta suka zamo ‘ya’yan wane. In mutane suna cewa su ‘ya’yan wane ne, to sun zamo ‘yan kabilarsa.

Larabawa kafin bayyanar Manzo (S) sun dauro a nizamin kabilanci, suna da gidaje. Kalmar ‘Hai’ a Larabci ana nufin unguwa kenan, to su suna ce masa Kabila, har ma in kana karantawa a littafai za ka ga ana cewa Masallacin Kabila kaza, domin su kowane ‘Hai’ ‘ya’yan wani ne suke zaune a cikinsa, don haka ma ake ce musu ‘Banu wane da banu wane.’ Domin kowace shiyya daya (unguwa) duk ‘ya’yan mutum daya ne kan zauna, don haka ana iya ce musu Kabilar wane. Haka kuma in ka samu kauye a lokacin, za ka samu duk yan kauyen sun hadu a kan su ‘ya’yan wani mutum ne, kuma da yawa ma suna amsa sunansa ne. Larabawa banda kananan kabilu suna da manyan kabilu, wadanda suma asalinsu mutanen da suka gangaro ne daga ‘ya’yan wane da ‘ya’yan wane.

To, kuma har ila yau kafin bayyanar Musulunci Kabila ita ce asasin zama, don akwai abin da ake ce ma ‘Badan’, akwai abin da bai kai Badan ba, akwai kuma abin da ya fi shi. Karamar kabila wacce ake ce ma ‘Hai’, akwai kuma wcce ta kan hada kabiloli su zama babba a karkashin wata kabila, kamar aka ce a cikin Larabawa akwai ‘Mudar’, Kabilar Mudar suna da yawa sosai, kusan mafi yawan Larabawa sune, to kuma a tsakaninsu a kan ce wadannan suna ‘manazira’ wadancan sune ‘Gadfa’ wadannan sune ‘Gassan’ da sauransu, duk suna da irin wadannan.

To, kuma a lokacin Jahiliyyar Larabawa Kabila shine asasin komai. Idan ana rigima kaga mutum biyu na fada, to kai kana goyon bayan dan kabilarku ne. Inda mutum biyu za su yi fada, daya dan kabilarku ne, dayan dan wata kabilar daban, to z aka goyi bayan dan Kabilarku ne, da ka zo z aka bigi dayan ne, baka tambayar ma me yasa ake fada, kai dai kawai dan kabilarku za ka kare.

Kuma lokacin nasu in ana fadan kabilanci, in dan wata Kabila ya ma wani abu, to za su iya ramawa a kan koma wane dan kabilar wannan mai laifin, don haka ne ma aka samu yakokin Kabilu. To wannan shigen rayuwar iri daya ne da wanda Turawa suke da shi, kusan shima a kan wannan asasin suka doru. A kansa kuma suka kafa kasashensu na Ingilishi da Faransawa da Jamusawa da sauransu, har suka kafa al’ummu dore a kan jinin kowanne.

To, kuma lokacin da suka bazu suka fara mamaye kasashen duniya sun zo da wannan zimmar na karfafa al’ummarsu ne. Don kowace kasa tana neman ta bunkasa arzikinta ne ta mamayi wadansu wurare, don haka sai ya zama irin fadan dokan daji, fadan dabbobi, wanda ya fi karfi shi zai mangare kawai. Kuma a kansu sukan hadiye juna, in karamar Kabila ta dan yi karfi sai ta hadiye wata, sai ta je ta mamaye wata ta kwashe matan da mazajensu a matsayin bayi, ta kashe mazajen a rushe kabilar gaba daya, a kwaso matansu da yara a maishe su bayi shikenan sai su zama yan wannan Kabila din, shikenan Kabila ta habbaka.

To, kusan na Turawa ma ya wuce hakan, su ana share mutanen ne gaba daya kawai. A kan kawar da su ne ya zama babu Kabila ma sam-sam. Don da wannan zimmar suka taso suka basu suna nemawa kowace kasa tasu daukaka. Akan wannan asasin Kabila suka kafa kasashe.

Kasar Faransa ta Faransawa ce. Faransawa mutane ne wanda suke da harshe da al’ada da addini guda. Ingilishi, wadanda suka kafa England, ko da yake sun mamayi wasu Kabilun sun danne su da karfin tsiya (Kabilar Irish da Scot) da karfin tsiya aka ci karfinsu aka mai da su suma Ingilishi, ko da yake har yanzu England daban ne, Scotland daban ne, Irish daban ne, Island daban ne, amma dai suna karkashin sarauniyar Ingila ne, an danne su da karfin tsiya. In kai ba dan kabilar Ingilishi bane baka zama komai a Ingila, ko ka zama wani abu sai dai a matsaki ne biyu. Har yanzu mugun Kabilanci ke gudanar da al’ummar Ingilishi na yanzu, kamar yadda yake gudanar da rayuwar Turawa.

To da wannan ne kuma suka zo nan. Sun zo nan ne ba don su maishe mu Kabilarsu ba. Sun zo nan don su daukaka kasashensu ne, sun zo neman dukiya ne wanda za su diba don su bunkasa nasu al’ummomin don haka mutane basu zama a bakin komai ba.

Na’am, Faransa suna da wani tsari da suke ce ma ‘assimilation’ hadiya kenan. Su sun debi bakaken Afirka sun mai she su Faransawa. Amma sai sun zaba, sai wanda suka koyar suka raine shi, suka yaye shi ya zama ya tabbata a wajensu ya kai mustawan su karbe shi a matsayin Bafaranse, to sai a bashi matsayin Bafaranse, ya zama Dan Faransa. Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka irin Boili da Songo duk sun samu wannan cigaban na zama Faransawa. Galibansu kuma yakan zama sun auri Bafaransiya. Kuma har ma akan zabe su suje majalisar dokoki na Faransa daga Afirka na Kudu.

Wannan (tsarin nasu) ya taso ne sakamakon ‘i’itikadin’ Faransawa na cewa kabilarsu tafi kowacce, kuma hanyar rayuwarsu ya fi kowanne hanyar rayuwa kyau a duniya, saboda haka suna ganin kowane mutum wayayye ya kamata ya zama Bafaranse. Ya rika yin sutura irin na Faransawa, haka ma abincinsa, da sassafe in ya tashi ya sha coffee, ya dan zuba masa wiski a ciki, (da yake shi Bafarance ya cigaba, bai ma damu da wanke baki in ya tashi ba, wai kansa ya waye). Da ya tashi da safe zai antaya coffee ne ya zuba masa wiski, sai ya tafi wajen aiki. In can 12 na rana ta yi, sai a jibga masa himin abinci yai ta ci, sunan wannan abincin ‘lunchou’ (lunch kenan), to lunchon din nan za ka ga akwai wani Buredi ya kai tsawon yaro dan shekara bakwai da himin macaroni, ya ci gashin bakinsa na motsi, ya yi kusan awa guda yana cin abinci, sannan ya je ya kwanta. Ya yi kamar awa biyu ko uku yana bacci sannan ya dawo aiki. Don haka har yanzu kasashen Faransa 12 na rana ake tashi aiki, kowa ya tafi gida, can bayan an ci abinci an huta sai a dawo kuma karfe hudu a tashi 6 na yamma.

To wannan suka bazu suna koyar da shi. ‘Ofcourse’ da addinin Bafarance da Harshensa da kuma tunaninsa shine ke kokarin ya sa maka. To su Faransa akalla sun yi wannan. Su a wajensu akalla sun Faransantar da mutane ne. Amma daga baya sai ya zama kyamar bako ya fi tsanani a tsakanin Faransawa, domin su yanzu suna bugun kirji, wadanda suka canza musu kama din ma suna kyamarsu kan cewa har yanzu ba su zama cikakkun Faransawa ba.

To, wannan ina muku shimfida ne don a gane mene ne makasudin zuwan Bature kasar nan?

Za mu cigaba…

Rubutawa:  Daga cibiyar wallafa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post