Matsaloli, cututtukan Sheikh El-Zakzaky da zaman sa a gidan yarin Kaduna


DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 



0/2/2020

Tun bayan rikicin da ya afku a Zariya tsakanin Sojoji Najeriya ƙarƙashin Janar Tukur Buratai da 'yan Shi'a mabiya El-Zakzaky wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban yan Shi'a ciki har da ƙarin wasu 'ya'yan El-Zakzaky'n na cikinsa guda uku a 12-14 Disamba, 2015. Inda shima Sheikh El-Zakzaky da matarsa Zeenatu suka samu munanan raunuka a jikinsu saboda harbin da Sojojin suka yi masu a lokacin suka kai hari gidansu dake unguwar Gyallesu a Zariya. Harbin da ya haddasa masu cututtuka da matsaloli a jikinsu masu yawan gaske.
Tun bayan rikicin a 2015 El-Zakzaky da matarsa ke fama da ciwuka a sakamakon rashin samun isasshiyar kulawa daga ƙwararrun likitoci a hannun hukumar DSS. A shekarara 2018 bayan shigar da su ƙara a gaban wata kotun jihar Kaduna El-Zakzaky da matarsa ta hannun lauyoyinsu sun buƙaci kotu ta basu beli don neman lafiyarsu kafin a cigaba da shari'ar, buƙatar da alƙali bai aminta da ita ba a wannan lokacin. Inda a wajajen ƙarshen 2019 alƙali ya basu beli domin neman lafiyarsu a ƙasashen waje wacce take ta tabarbarewar a hannun hukamar DSS ɗin, duk da irin maƙudan kudaden da DSS din ke iƙirarin kashe masu. Bisa ga dogaro da binciken da likitoci suka yi masu, inda kuma likitoci suka tabbatar lallai baza'a iya masu maganin matsalolinsu ba a nan Najeriya.

Sakamakon binciken guda biyu wadanda na karanta 'preliminary report' da na biyun 'final report'. Ya nuna tabbas suna buƙatar kulawa ta musamman da gaggawa daga wajen ƙwararun likitoci.

Binciken ya nuna matarsa Malama Zeenatu na dauke da matsaloli ɗai-ɗai-ɗai har guda shida, waɗanda suka hada da matsalar hanta ta 'Hepato-Biliary Complications', matsala gwuiwowinta na ƙafafu 'Bilateral Osteoarthritis', matsalar idanu wanda ke haddasa mata yanar ido 'Mature Cataract', da matsalar ƙasan maƙogoranta wacce likitoci ke kira da 'Hyperthyroidism'. matsalolin da ke haddasa mata tsanin ciwon-ciki, ƙwarnafi, da matsalar ƙafafunta (abinda ke haddasa mata kasa tsayuwa a kan ƙafafun).

Inda shi kuma Sheikh El-Zakzaky'n ke fama da matsaloli a zuciyarsa 'Cardiac Ischemia' da 'Ventricular Hypertrophy', matsalar wuya 'Cervical Spondylitis' sannan da matsalar idanunsa 'Progressive Glaucoma' da na biyar 'Anophthamia' wanda sune mafi girma a idanunsa duka biyun wanda aka harba da harsashi da wanda ba'a harba ba, ɗayan har ya mutu ɗayanma ya kama hanyar mutuwar. Inda daga baya da likitocin ƙasashen waje suka zo ƙarkashin wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙin Musulmi 'Islamic Human Rights Commission' (IHRC) wacce ta ke da mazauni a birnin London. suka zo suka buƙaci lallai ayi masa gwajin guba, inda daga baya rahoton gwajin gubar ya nuna lallai akwai gubobi guda biyu, gubar 'lead' (gubar dalma) wacce har ta kai matakin (Average Level) da kuma gubar 'Cadmium'. wanda duka wadannan gubobi ne masu hadari wanda ana buƙatar ayi aikin kwashe su cikin gaggawa, kuma ana buƙatar ƙwararrun likitoci ne 'Clinical Toxicologist' waɗanda zasu yi aikin da isassun kayan aiki wanda za'a dinga yin gwaji akai-akai har a kwashe gubobin gabadaya. Domin su gubobin ko anyi maganinsu inda ba'a kwashe su daga jikin mutum ba aikin banza ne. Ita wannan gubar dalmar ita kadai tana haifar wa mutum da hawan-jini, rashin jin sauti (a kunne), matsalolin tsayar da ayyukan ƙwaƙwalwa 'Neurological Issues' wanda kuma in ba'a ai gaggawar kwashe gubar ba takan yi damejin ƙodar mutum. Takan balle sinadarin 'Calcium' kuma ita bata aikin 'Calcium' ɗin (wanda hakan ke jawo matsala sosai ga ƙashin mutum) . Ita kuma gubar 'Cadmium' din tana jawo matsalar 'Cancer' a ƙoda da huhu, wanda ke jawo riƙewar numfashin mutum. ita ma da sauran matsalolin ƙashi.

Cikin sanarwar da yaron El-Zakzaky a fitar ya nuna tun bayan mai da su gidan yarin Kaduna lafiyarsu ta ida tabarbawarewa a chan. Jiya 19/2/2020 IMN ta fitar da sanarawar cewa kwantirolan gidan yarin Kaduna ya hana likitocin El-Zakzaky su ma gana da shi, don su ƙara jin matsalolinsa.  duk da cewa kotu ta bada umarnin a barsa ya gana da kowa. Ni na san gidan yarin Kaduna yake da yadda dan asibitin da ke cikinsa yake. asibitin da ke 'Kaduna Prison' bai ma kamata a kira shi da asibiti ba, saboda rashin ƙwararrun likitoci, rashin kayan aiki da rashin magunguna. wani 'chemist' ɗin ma ya fishi amfani da kayan aiki. Ɗan ƙaramin ciwo ko zazzabi in yayi zafi ba'a iya magance shi a asibitin, sai an fita da mutum. ballantana su waɗannan bayin Allah'n da ke fama da manya-manyan matsaloli da lalurori ga takura da rashin sakewa da ake fama da ita a wannan gidan yarin.

Amma duk da haka da waɗannan tarin matsalolin da suke ciki, gwamnatin kama-karya ta APC ta na cigaba da tsare su a duk da umarnin da kotuna suka bayar na sakinsu da belinsu don neman lafiyarsu, inda take tuhumarsu da wasu laifuffuka. banda rashin adalci da zalunci na APC a ina ne ake tuhumar mutumin da bai ma da laifiyar da zai iya kare kansa ? Ta yaya hankali zai yadda mutumin da aka kashe yaransa da dubban mabiyansa ka zo kana tuhumarsa da kashe wani Soja ƙwara daya ? Me yasa tun farko ba a kai su ƙara kotu ba ? duk duniya babu dokar da ta ce kaje ka kashe mutane wai don sun tare hanya, indai ba dokar Shedan ba. (Gwamnatin APC kama karya kawai ta ke yi da sunan dimukrdiyya). Banda zaluncin gwamnatin APC a ina ne ake jiran umarnin alƙali kafin a nemi lafiyar mutum ? Ballantana ma alƙalin ya yanke hukuncin a barsu su sami lafiyar jikinsu. amma abin baƙin ciki gwamnatin da ke iƙirarin bin doka da oda, da kawo chanji ta ƙi basu damar samun lafiyarsu. indai ba so gwamnati ta ke su fadi su mutu ba to lallai ya kamata gwamnati ta bi umarnin kotuna ta saki El-Zakzaky da matarsa ko ta basu beli don neman lafiyarsu. kamar yadda suka ce yanzu sun fara bin umarnin kotuna har sun bada belin Kanal Sambo Dasuki da Omoyele Sowore. suma waɗannan a tabbatar anbi umarnin kotu an basu damar neman lafiyarsu domin zaman lafiyar kasa da ɗorewar dimukradiyya ingantacciya. suma 'yan Najeriya ne kuma suna da yanci kamar kowa-da-kowa. domin sam-sam babu adalci da bin doka a cigaba da tsare El-Zakzaky da matarsa da gwamnati ke yi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post