Menene abin burgewa cikin saɓawa mahalicci??


Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bin Haroun Sigau.

Sau da yawa mukan ɗauki wani abu ko kuma wata dabi'a ta banza a matsayin abin burgewa, musamman a wannan zamani da muka tsinci kanmu, muka kuma tarbiyyantar da gangunan jikin mu da dabi'u na irin na yahudawa, masu yakar imanin mu.

Banga wayewa kan ɗora hoton sister a Social Media ba, wani riba ce zamu samu a ciki?? Daukar hankalin mazaje ko kuma, janyo su zuwa saɓawa mahalicci bisa mummunan kallo da zasu yi wa, wanda ke cikin hoton?

Da yawan Sister's sukanyi hakan kuma da sanin cewa; ya saɓawa Shari'a suna yine kawai don nishaɗi ko neman 'fans' wanda hakan zubar da kima ne a matsayin ki na musulma mai kiran kanki kina addini.

Wasu kanyi hakan ne don ayi musu like, comment da sauran su. Amma bansan ko kudi ake tura musu ba, in akai masu like ko comments da yawa. Ya kamata mu bambanta da sauran mutane mu kiyaye abinda zai jawo fitina a ibadun mu. Inke kin shirya ɗaukar alhakin waɗan da zasu saɓawa Mahallicci shi kuma ya zai ji inya tsinci kansa tsundun cikin saɓo ba tare daya shirya ba? Ki sani lallai, zai iya qalubalan tarki a gaban Allah (T).

A matsayin ki ta uwa, waccce nan gaba kike shirin rike yara har yazam kin basu tarbiyyar da za'ai alfahari dasu bisa kyawawan dabi'u, sai gashi kina bata dabi'un manya. A haka ne zaki tarbiyyan tar da yara kenen? Ko ko zaki lalata musu tarbiyya ne? Social Media fa kaman duniya ce baki daya ke kallon ki, kina yin wani abu wata ko wani yayi sha'awa shikenen zai zam cikin masu koyi da ilimin da kika watsa na alkairi ne ko sharri.

Yanzu duniya ta llaace, akanyi amfani da hotunan mata a shafukan batsa ko nishadi, ya abin zài kasance in mahaifin ki ko wani dan uwanki yaga hotonki na yawo cikin irin wadannan wurare koda ko ba'a munana shi ba? But yanzun akasarin abinda ake ma na batanci akan sami hoton wacce bata ji ba bata gani bane ayi editing din wani hoton batsa a hada ake watsawa don nishadi.

Shin wannan ne irin ribar da kike son samu bisa dora hoton ki???

Lallai, abin takaici ne kwarai kana tutiyar kana kan hanyar gaskia, a bangare guda kuma kana 'saddu an sabilillah'.

Wannan dai tunatar wa ce banyi don wata ko wani ba, nayi ne domin kawo gyara, da fargar damu kan abinda ka iya jawo mana sabawa Allah mazam mu da matan mu.

Allah ya bamu ikon gyara munanan ayyukan mu, da musanya su da kyawawa alfarmar Sayyada aɗɗahira (SA)...

@Bin Haroun Sigau

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post