Girke-Girke: Yadda ake hada mint leaf juice (lemon na'a-na'a)@Ma'asumah  Nigerian News Update, tare da Sakina Ahmad kazaure

Assalamu alaikum warahmatullah, barkan mu da sake saduwa a wannan dan-dali namu na girke-girke, Wanda shafin ma'asumah Nigeria news update ta dauki nauyin kawo maku akowane mako.

Ayau zamu koyi yadda ake mint leaf juice (lemon na'a-na'a)

Idan Kika tashi hada wannan lemo na ganyan na'a-na'a, zaki samu abubuwan bukata kamar haka:-

1.  ganyan na'a-na'a ( yadda zai wadaceki)
2.  Tsamiya (madai-dai ciya)
3.  Suger

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

4.  Flavor

Yadda ake hadawa

DA farko uwar gida zaki wanke tsamiyarki, ki dora a wuta ki tafasa, sannan saiki wanke ganyen na'a-na'arki kiyi blending dinsa, sannan saiki duba tsamuyarki idan ta tafasa, saiki sauke ki tace. Idan Kika tace tsamiyar saiki tace na'a-na'ar akan tsamaiyar, saiki zuba sugar da flavor ki juyashi sosai, ki tabbatar sugar da flavor ya isa, sannan saiki sa afrij ko kisa kankara yayi sanyi.

Asha dadi lafiya, kuci gaba da kasancewa da shafin ma'asumah Nigeria news update,

Insha Allah zamu rika kawo maku yadda ake hada sabulu, gyaran gashi dadai abubuwa da yawa kodai Ku kasance da shafin ma'asumah Nigeria news update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post