Furucin Buhari da El-Rufa'i iri ɗaya ne dana fir'auna!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YADDA QARSHEN FIR'AUNA TA KASANCE SU MA HAKA ZA SU KASANCE.

Sunar Allah ce wacce ba ta canzawa, babu wani qarni da zai zo face sai an sami Fir'aunan wannan qarni da kuma Musan sa.

Aikin Fir'aunan kuma shine yaga ya yi rinjaye kan Musan wannan zamani/qarni ta hanyar halakar da shi don kada addinin Allah ya kasance shine mai rinjaye.

Wani abin farin ciki kuma shine, Allah (T )kan halakar da wannan Fir'aunan, sannan ya wanzar da Musan wannan qarni ya kasance shi ke yin rinjaye.

Karanta wannam furuci na Fir'auna, sannan ka nazarci furucin Buhari da El-Rufa'i ka gani ko akwai bambanci ?

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA FIR'AUNA YACE; ‘’ KU QYALE NI (kawai )NA KASHE MUSA, YA KIRAYI UBANGIJIN NASA (ko zai iya kare shi ), LALLE NI FA INA JIN TSORO (ne )KADA YA CANZA MUKU ADDININ KU (ta hanyar kawo muslimci ), KO KUMA YA BAYYANAR DA FASADI (ta hanyar kawar da azzalumai ) CIKIN QASA .

Jin wannan furuci da kuma mummuniyar nufi ta Fir'auna sai Musa (A.S )yace;

‘’ LALLE NI INA NEMAN TSARIN UBANGIJINA KUMA UBANGIJINKU DAGA (sharrin )DUKKAN WANI MAI GIRMAN KAI WANDA BAI YI IMANI DA RANAR SAKAMAKO BA .’’

Kamar dai yadda ba a rasa mutanen banza cikin mutanen kirki, haka ma ake samun mutanen kirki cikin mutanen banza.

Jin wannan furuci na Fir'auna (L.A )sai wani mumini daga mutanensa yayi nufin bada kariya ga Musa (A.S ). Shine Allah (T )ya bamu labarinsa kamar,haka;

‘’ SAI WANI MUMINI WANDA YA BOYE IMANINSA DAGA CIKIN IYALAN FIR'AUNA YACE;‘’ YANZU ZA KU KASHE MUTUM HAKA KAWAI DON YA CE ;‘’ UBANGIJINA SHINE ALLAH ALHALI YA ZO MUKU DA HUJJOJI (bayyanannu )DAGA UBANGIJINKU (Allah ba Fir'auna ba )? AI IDAN YA KASANCE MA QARYA YAKE YI, AI QARYAR A KANSA TAKE. KUMA IDAN YA KASANCE SHINE MAI GASKIYA, TO, SASHEN ABINDA YAKE YI MUKU ALQAWARINSA (na azaba )ZAI SAME KU. LALLE FA ALLAH BA YA SON WANDA YA KASANCE MAI YIN BARNA (kuma )MAI QARYATAWA !‘’

(Suratul-Ghaafir, aya ta 26-28).

Haba masu hankali , ku nazarci wannan furuci na Fir'auna da addu'ar da Musa (A.S )yayi , sannan ku nazarci furucin Buhari da El-Rufa'i akan Sayyid Zakzaky (H )da kuma addu'ar da Sayyid (H )ke yi a kullum .

Da kuma furucin wasu muminai masu ganin Buhari a matsayin shugaba, amma ba sa goyon bayansa kan wannan mummuniyar manufa ta su.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

     08137925034

~10th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post