Da ilimi da Jahadi ne Addini Yake Tsayuwa Abinda Yakai Musulmin Yau ga Kaskanci Shine Yin Ilimi Da Rashin Jahadi!!!@Ma'asumah Nigerian News Update@

Jahadi Kariya ce Ga Musulunci da Kuma Musulmi da Hakkinsu da Kuma Martabarsu,

Ilimi Kuma kariya ce zuwa ga rashin barin addini ya lalace saboda duk mutanen da jahilci yayi yawa a cikinsu zakaga hauka da zalunci da fasikanci yayi yawa a cikinsu,

Mutanen da Kuma ilimi yayi yawa a cikinsu matukar ilimin Mai amfani ne wannan ilimin nasu zai jasu zuwa ga sanin Allah da Kuma bauta Masa bauta ta hakika,

Kaga anan ilimi Mai amfani tare da ayyuka na gari idan Suka hadu su zasu Samar da Wanda ake Kira malami Mai daraja kaga kenan duk wata daraja a duniya ta Kare ne ga abu biyu neman ilimi da Kuma aiki dashi da Kuma Jahadi,

Dan haka Kira ga dukkan Yan uwa musulunci shine kuyi kokari kuzama daliban ilimi dai dai gwargwado Kuma kuyi aiki dashi da Kuma bada kokari da tsayuwa kyam a harka ta Jahadi domin samarwa addinin musulunci da musulmai izzah a duniya da Kuma gobe kiyama.

Abba Bature.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post