Daga Wakilin Mu --Idishia Jos.
A jiya Lahadi guguwar Zanga-Zanga ta barke a garin Jos wanda al'umman Kirista suka yi ta. Wannan zanga-zanga ya biyo bayan kashe wani matashin Kirista dan asalin jihar Pilato. Wannan matashi mai suna Ropvil Daciya 'Yan Kungiyar Boko Haram ne suka kama shi a hanyar komawansa Maiduguri daga Garin Jos.
Ropvil Daciya asalin sa 'dan karamar hukumar Garin Pankshin Lankang dake Jihar Pilato ne. Kuma shi 'Dalibi ne a Makarantar jami'ar Maiduguri University Of Maiduguri (Unimaid). A hanyar dawowan sa daga hutun makaranta Kungiyar Boko Haram suka kama motarsu inda suka musu kisa na farar daya.
Abinda ya tayar da hankalin mutanen Jihar baki daya, ganin yadda aka turo Bidiyo na Ropvil Daciya da karamin yaro a bayansa ya nade fuskar sa hannun sa da bindiga tana cewa "Sune Kirostocin Pilato wanda suka kashe musulmai a lokacin yaki" sai ya damfara mai harsashi a kansa ya kara mai daya a bayansa.
Iyalai da 'Yan'uwa na wannan mutumin sun nuna damuwansu da gazawar gwamnati wajen taimakawa 'dan'uwansu a yayin da aka kamasu. Sannan al'umma Jos sun yi ta Allah wa dai a kan wannan mummunan abu da ya faru.
Sabida kiranye kiranye da al'umma Jos din ta yi a Gwamnatin Jihar Pilato Simon Lalong daya duba wannan mummunan abu da ya faru hakan yasa fadar gwamnan ya tura da takardan rashin jin dadinsa yana mai Allah wa dai akan kisan da aka ma wannan matashi.
A kafar sada zumunta na Facebook akwai wani group na saka sakonni, da ya kunshi al'umma Jos wanda ake kira da "Come To Jos" zallan mutanen Jihar ne kuma an tattauna batun kashe wannan Matashi. In da suka cimma matsayan cewa ala dole ayi Zanga-Zanga mai take "Candlelight Procession".
An yi zanga-zanga ne cikin bakaken kaya dauke da Postocin matashin da kuma Kendir a kunne da wuta a cikin sa. Daruruwan Al'umman Kiristoci ne suka gudanar da wannan zanza-zanga, kuma anyi ta ne kashi Biyu daya an dauko daga Car Park Plateau State zuwa Secretariat Junction.
Nan wasu daga cikin Hotunan Zanga-zanga ne
Nan kuma Hoton matashin ne Ropvil Daciya ne wanda Kungiyar Boko Haram ta kashe ne.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.