Tsare Sheikh Zakzaky : Ibrahim Musa Ya Mayar Wa El-Rufa'i Martani.

Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.

Kotu ta ba da umarnin sakin El-Zakzaky tun a shekarar 2016 amma a na ci gaba da tsare shi shafin Jaridar BBC Hausa sun gana da Ibrahim Musa ga kuma yadda ganawar ta kasance;

Najeriya, 'yan kungiyar IMN ta mazhabar Shi'a ta mayar da martani ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i. Wannan na zuwa bayan da ta zargi gwamnan da yin kalaman cewa Shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim Elzakzaky ba zai taba fita daga gidan yari ba matsawar yana mulkin jahar. A cewar Ibrahim Musa, kakakin kungiyar a Najeriya, El-Rufa'i ya yi kalamin ne a hira da wani gidan rediyo a ranar Juma'a.


Ibrahim Musa ya ce ga alama gwamnan na da wani dalili na kashin kansa na ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. Ya kuma kara da cewa kotu ta ba da umarnin sakin El-Zakzaky tun a shekarar 2016 amma gwamnati ta ci gaba da tsare shi babu gaira babu dalili. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam na yawan sukar gwamnati kan ci gaba da tsare Sheikh Ibrahim El-zakzaky, suna cewa gwamnatin ba ta mutunta umurnin kotu kuma tana karan tsaye ga dokokin kasar.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post