🇮🇪Ma'asumah Nigerian News update
Daga Wakilinmu Na Kano
MJ Matashi Ibrahim
_Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai suna Mrs Udeme a kan laifin kashe mijinta tare da tsinke mazakutar shi
_Wadannan laifukan kuwa abin hukuntawa ne a sashi na 165 da 223 na dokokin laifukan jihar Legas na 2015
_Wannan ne lauya na biyu da lauya mace ta taba kashewa a jihar bayan zarginsu da cin amana da lauyoyin matansu suka yi
_Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai suna Mrs Udeme mai shekaru 47 a kan zargin kisan kai da kuma tozarta gawa.
_Duk da matar ta musanta zargin da ake mata, dan sanda mai shigar da kara, Sunmonu Babatunde, ya sanar da kotun cewa wacce ake zargin ta aikata abinda ake zargin ta da shi ne a ranar 3 ga watan Mayu a rukunin gidaje na Diamond, Sanotedo dake Lekki a jihar Legas.
_Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya
Ya ce wacce ake zargin ta soki mijinta da wuka kuma ta lalata gawar shi ta hanyar yanke mazakutar shi.
_Wannan laifin ya ci karo da tanadin sashi na 165 da sashi na 223 na dokokin laifuka na jihar Legas na 2015.
_Sashi na 165 ya tanadar da shekaru 5 a gidan gyaran hali inda sashi na 223 ya tanadar da hukuncin kisa.
🇮🇪Ma'asumah Nigerian News Update.
Tags:
Labaran Duniya