Sunyi Shirin Kashe Annabi (S.a w.w) Ma, Sai Dai Allah Bai basu Sa'a Ba!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BA YA KASANCEWA GA RAI TA MUTU SAI DA IZNIN ALLAH

Kafirci da rashin gaskata Allah kan cewa rayuwa da mutuwa a hannunsa (T )take kan sa mutane su riqa riyawa ko tunanin za su iya kashe mutum ta kowacce hanya, sannan wasu kuma suga cewa eh lalle wadannan mutane na da ikon yin hakan.

Irin wannan tunani ba yau ko yanzu aka fara yinsa ba, a'a, anyi haka a baya, sai dai kawai muce tarihi ne ke maimaita kansa.

Yayin da kafiran Quraishawa su kayi yunqurin hana cigaban da'awar Manzon Allah (S.A.W.W )kuma suka ga al'amarin sai qara cigaba yake yi maimakon daqilewa , hakan yasa su kayi taron su na kafirai cikin sirri don sanin matakin qarshe da ya kamata su dauka a kansa (S.A.W.W ).


Allah (T )ya bamu labarin abinda wadannan kafirai suka tattauna a boye kamar haka;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ (Ka tuna yaa Muhammad )A LOKACIN DA WADANDA SUKA KAFIRTA SUKE YIN MAKIRCI GAME DA KAI, DOMIN SU TABBATAR DA KAI (a tsare )KO KUMA SU KASHE KA (don kada kayi nasara kan abinda kake yi ), KO KUMA FITAR TA KAI (daga qasar ), SUNA MAKIRCI (a kanka )KUMA ALLAH YANA MAYAR MUSU DA MAKIRCINSU, KUMA ALLAH NE MAFIFICIN (mayar da makircin )MASU MAKIRCI .‘’

   (ANFAL:30)

Kuma alqawarin sa ne (T )cewa zai taimaki bayinsa muminai akan kafirai da munafukai , sai dai su (kafirai da munafukan )ba su fahinci hakan ba.

Sannan kuma Allah (T )ya qara da cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ BA YA KASANCEWA GA RAI TA MUTU SAI DA IZNIN ALLAH...‘’

Wadannan ayoyi biyu kadai sun gamsar damu cewa babu abinda wadannan azzalumai za suyi akan Sayyid (H ). Duk wani abinda ya faru a kansa mun san haka Allah yaga dama bisa wata manufa tasa (S.W.A ), wanda mu kuma ba mu isa kawar da qaddarar Ubangiji ba.

DUK WANDA YACE AKWAI SAKACIN MU SAI NA TAMBAYE SHI CEWA;

SHIN, SHI MA ALLAH YANA SAKACI NE DA YA BARI AKA KASHE KO AKA CUTAR DA MANZANNINSA (A.S )?

Tare da Ado  Isah  Guda.

       08126385470

~13th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post