@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TA BAYYANA ABINDA TA KE JIN TSORO GAME DA KISHIYA
Magana ta gaskiya ita ce, da ace mata na da tunani irin na wannan sister da ba za a riqa jin su yayin da mijinsu yayi nufin qara wata mata ba.
Tana da tunani mai kyau wanda ya kamata ace an jinjina mata, domin irin wannan tunani ya kamata ace kowacce mace na da shi, musamman ma sistoci .
Cikin hirar ta su take ce masa;
‘’ NI FA NA RASA TUNANI IRIN NA WASU SISTOCI DAGA CIKINMU, A DUK LAKACIN DA BURAZA YA TASHI QARIN WATA MATA SAI KA JI ANA FAMAN RIGIMA DA SU.
TO, WAI A MATSAYIN MU NA 'YAN'UWA 'YAN GWAGWARMAYA WADANDA A KULLUM JIRAN SHAHADAH MUKE, ITA MATAR DA TAKE QIN AYI MATA KISHIYA TANA TUNANIN CEWA BURAZANTA BA ZAI IYA YIN SHAHADA BA KENAN?
IDAN KUMA AKA CE YA YI SHAHADA, TANA TSAMMANIN SAURAYI ZA TA SAMU MARAR MATA WANDA ZAI AURE TA KO KUMA ZAMA ZA TAYI BA AURE TUNDA BA TA SON KISHIYA?
GA SHI KUMA ALLAH YANA MANA ARZIQIN 'YA'YA MATA, TO, SUNA TUNANI NE CEWA IDAN 'YA'YANSU MATA BA SU SAMI MARAR SA AURE BA SAI SU ZAUNAR DA SU KENAN A GABANSU BABU AURE?
GASKIYA WANNAN BA TUNANI NE ME KYAU BA (in ji ta ).’’
Mijin nata yace, bayan ta gama wannan bayani sai kuma ta nuna abinda ta ke jin tsoro game da kishiya. Ta ke cewa;
‘’ NI DAI KAWAI ABINDA NAKE JIN TSORO GAME DA KISHIYA SHINE, IDAN AKAYI RASHIN SA'A AKA AURO IRIN MATAN NAN MARAR SA SON ZAMA DA KISHIYA, TO, A KULLUM QOQARINTA SHINE TAGA TA FITAR DA KE DAGA GIDAN DON TA ZAUNA ITA KADAI. WANNAN SHINE KAWAI ABINDA NAKE JIN TSORO GAME DA KISHIYA, AMMA AI ITA ABOKIYAR ZAMA CE.‘’
Idan muka nazarci tunanin wannan sister za muga cewa lalle akwai darusan dauka daga ciki.
(1)- Ya kamata ace sistoci su zauna da shirin cewa sunan burazunsu shahidai , to, idan hakan ta faru menene makomarsu? Suna gani in burazu masu aure ba za su aure su ba don sistocinsu ba sa son kishiya, hakan zai iya zama, alkhairi gare su?
(2)- Duk sister da suke zaman lafiya da burazanta sannan kuma tasan cewa za a shigo da wacce za ta fitar da ita daga gidan, za ta so wannan aure?
Da gaske ana samun irin wadannan mata masu fitar da matar da aka tarar cikin gida. Hakan zai iya kasancewa ta bin wasu hanyoyi ne da suka sabawa shari'a, ko kuma yawan rigima da wacce aka tarar cikin gidan.
Idan hakan ta faru ga wacce ba ta son tashin hankali , sannan kuma ta hadu da sakaren namiji marar sanin cewa kare mutuncin kowacce a kansa yake, to, sai kuwa kaga ta fitar da ita daga cikin gidan.
Amma fa duk da irin wannan tunani ko hange na sister ba zai taba zama hujja kan cewa idan burazanta ya tashi neman qari ta fake da wannan hujja na abinda take tsoro ba, domin ba kowacce mace ce me irin wannan halayya ba.
Kamata yayi ta kasance mai tawakkali da kuma fatan alkhairi cikin kowanne al'amari.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
~31st January , 2020.
Tags:
Taskar Ma'aurata