Ina Fatan Mika Mulki Ga Wanda Zai Gajeni Cikin Ruwan Sanyi, inji Shugaba Buhari

Kalaman Shugaban Kasar Nigeriya A Ranar Alhamis. Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos. Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa a kan zaben shekarar 2023, na ganin zaben ya gudana a cikin kwanciyar hankali ta yanda zai mika mulki a hannun wanda zai gaje shi lami lafiya. Buhari ya fadi hakan ne a wajen walimar cin abinci tare da wakilan tawagar Lauyoyi a zaben shugaban kasa da ya gudana a shekarar 2019, ranar Alhamis a Abuja. Mai Magana da yawun fadar ta shugaban kasa, Garba Shehu, ne ya jiwo Buhari na fadin haka a matsayin wanda ya amfana da gudanar da zabe a cikin lumana a bisa kuma turban adalci, yana mai cewa shi ma zai danka mulkin ta irin wannan hanyar ga magajin sa a shekarar 2023. Da yake tilawar yanda ya ga al’ummar kasar nan sun yiwo tururuwa a lokacin yakin neman zaben sa a shekarar 2019, sai ya aminta da cewa ba aringizo aka yi ba a wajen bayyana sakamakon zaben.” “Yawan mutanan da suka fito domin tarban mu a yakin neman zaben namu na 2019 a duk sassan Jihohin kasar nan 36, ba abu ne da wani zai iya tilasta masu yin hakan ba,” in ji Buhari. “Hakan ne ya kara ba nu tabbaci da yawan kuri’un da na samu a wajen zaben. Hakan ne kuma ya sanya na dage a kan cewa tilas ne zaben ya gudana lami lafiya domin a sarari yake cewa na amfana da gudanar da zaben a turbar gaskiya da zaman lafiya. A dabi’ance ina son zama mai hankalin kansa. Na yi rantsuwa da Littafi mai tsarki a kan cewa zan yi aiki a bisa dokokin tsarin mulkin Nijeriya. “Zan ci gaba da yin bakin kokarina, ian kuma sa ran ya zuwa shekarar 2023, zan muka mulki ne lami lafiya ga duk wanda ya kasance zai gaje ni, ina kuma mai yi ma shi fatan alheri.” Shugaban tawagar Lauyoyin wacce Wole Olanipekun, (SAN), ya jagorance su ya yi tilawar nasarorin da suka samu a kararrakin zaben na shugaban kasa. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post