Tsana da Tsangwama da karyar da Akeyiwa Yan Shi'a yasa Na Fahimci Shi'a !!!

Inji Naseer Yababa Malunfashi

Tun muna yara muna zuwa makarantar allo tare da Islamiyyar dare nake jin ana magana a kan yan shi'a da fadar miyagun maganganu a kan yan shi'a.To ni a tunani na wadan su miyagun halittu ne masu kashe mutane dake zaune a wata kasa.AKwana a tashi har aka fara nuna min ai wancan dan shi'a ne ko in suna taro ace ai taron yan shi'a ne ni kuma daga nan nace Insha Allah sai na gano manufar wadannan mutanen.

Ance basu yarda da Qur'ani ba sai naji suna cewa tsarin turawa ba Addini bane Qur'ani ne littafin da ya dace abi.sai nayi mamaki da jin haka.sai kuma na tuna ance wai basu yarda da manzancin manzon Allah ba amma sai naji duk sanda malaman su zasu fara magana sai sunyi ma manzon Allah salati da yayan gidansa.

Sai naga yadda matan su ke fita ba tare da fita irin ta sauran matan gari ba,wannan ne ya kara bani yakinin mutanen nan fa suna da gaskiya,A yayin da kuma naga yadda yan Izala a karatun su kullum da'awar su cewa yan Darika kafirai ne suna bautawa kyale da makamantan su.Hakika ba zan manta ba wata rana Allah yayi ma wani Direban mota rasuwa mai suna LAWAI DOGO a nan cikin garin malumfashi sai a kaxo sallah sai wani liman malam Lawal na bayan gidan minister Nasiru zai ja sallah sai yan Izala suka ce basu yarda Dan Darika yayi ma gawar dan Izala sallah ba.

Daga nan mahaifin bawan Allah din nan ya fito yace ai Dana ne ko to malam lawal zai masa sallah wannan abun ya kara bani mamaki akan yan Izala matuka,kuma shi ya kara bani kwarin Gwiwar bincike a kan shi'a har Allah yasa na fahimci inda aka dosa.

Wanda gashi yau sune ake kashewa,a rusa masu gida da makarantu da shaguna,a daure su bisa zalumchi laifin su daya don sunce Allah ne abin bin su kuma littafin Allah ne littafin da zasu bi a matsayin littafin tsarin rayuwarsu.

Hakika ina godewa Allah da wannan kyauta da yayi min da ban kasancin masu korar wasu daga da'irar musulumci ba!Allah nagode maka da baka sani cikin masu kyamar Annabi da iyayensa da yayansa da jikokinsa da matansa da sahabban sa nagargarun ba!

Ina rokon Allah ya amshi rayuwa a kan wannan tafarki kamar yadda ya amshi rayuwar yan uwana sama da dubu a wannan tafarki a cikin kasa da shekara daya.Lallai sun bar duniya cikin yanci da yayi ma Azzalumai da munafukai bara'ah!
ALLAH ZAI CIKA HASKEN SA KO BUHARI DA SU BALA LAU DA SU EL,RUFA'I DA TUKUR BURUTAI DA I.G NA KASA BASA SO!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post