Sistoci:- Bakujin Kunya Komai Ace Maza Ne...???


Kudau Alkaluman ku Yan Uwa Sisters...

-Baku jin kunya komi ace maza? Ni abin nasu ma har bani mamaki yake, taya zaku zam haka?Sisticinmu sun maƙale alƙalumansu sun kuma kasa fitar da ilimummukan da suke da don ganin sun bawa addini gudunmawa.

-Yana da gayar muhimmanci sistoci su lizimci rubuce-rubuce da ƙoƙarta wa wajen shirya 'programs' a tsakankaninnsu domin wayar dakan ƴan uwa mata da ƙara musu ƙwarin guiwa.

-Akwai naƙasu sosai a tafiyar addini in ya zamana mata sun gaza a irin waɗannan tafiya, addini bai ware kowa ba mace ko namiji ko wanne  wajibinsa ne ya sauke nauyin da yake kansa.

-Amma sistoci sun tsaya a baya wajen sauke nasu haƙƙin ba kuma don basu da dama bane, rubutu nada muhimmancin gaske, a ƙalla in baki samu damar yin rubuce-rubucen littafai da zasuke warware matsalolin addini ba, akwai na warware matsalolin zammantakewar gida, kina da damar amfani da kafar sadarwa.

-Domin a wannan zamani namu kafar sadarwa ta haɗa komi wanda marubuci ke buƙata, amma sun maƙale alƙalumansu saidai suke kallon ana yi suna 'like' ko 'Comment' ƴan uwa na mata ku farga ku gane dole tafiyar nan fa bazata tafi yadda ya dace ba saida gudunmawarku.

-Komi zakai kana buƙatar sanin daidai da ba daidai ɗinsa ba, in kina da shakku akan abinda kika ga zaki iya na bada gudunmawa akwai Malamai saiki nemi sanin dacewar sa da akasin haka, maimaikon ki barshi baki ɗaya

-Da yawan lokuta in mata suna 'programs' ba ko wacce mace bace zaka gan ta iya fiskantar ƴan uwanta mata tanai musu jawabi, ko warware musu wata matsala da kwarin guiwa, wannan ma wata babban naƙasu ce, misali wata Sister ta shirya maulidin Fatima (S.a) na mata zalla, sai a ɗauko namiji kenen yayi jawabi?

-Su sisters ɗin me sukeyi, basu da ilimi ne? A'a hasali ma sunfi mu, mu maza samun ilimi da cikakken lokacin neman ilimi, domin da yawan lokuta mu muna wajen sana'a, zai bada citta ƙwarai yazam ana basu damar fitar da ilimummukan da suke dashi a cikin al'umma.

-In kina ganin ayyukan gida da kulawa da iyali yana hana miki samun lokaci, shin kinkai Sayyada Fatima (As) ne ita take komi na daga aikin gida saiɗan taimaka mata da Fiddah keyi, itace wacce ta fara rubuta littafi a tahiri @Mushaf Fatima, baya ga abubuwan da suke gabanta na ayyukokin gida, balle ma ku yanzun matan wannan zamanin kuna huce, kuke da damar yin komi cikin sauƙi.

-Ƴan uwa mata ku kara tunani ku gyara, domin ba wani aikin ibada da Allah (T) ya ware yace wannan banda mata, wani lokaci ma in Zaiyi magana yakan kira ko wanni ɓangare, ko kuma yayi maganar a jimilla, lallai ya wajaba garemu baki ɗaya kambama wannan kira da ƙara nunawa mutane ainifin wanene wannan Manzon da iyalan gidansa (As).

NASIHA CE, FATAN ZAKU GAFARCENI INDA WACCE MAGANA TA BAI MATA DAƊI BA.

         ┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post