MENENE SO

MENENE SO

Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto

To shi so wani tsarkakakken abu ne Wanda ba'a ganinsa da idanu sai dai alamomi su tabbatar da samuwarsa


Sannan shine gundarin saƙon Addinai
Da kiran Manzani

Idan kaso kace shine rayuwa ko kuma sirrin dake sa rayuwa ta cigaba

Duk inda kaga wata matsala ta faru to so baizo gurin bane

Wannan yasa manazarta ke ƙoƙarin ɗora rayuwarmu mutane akansa

Saidai kasancewar sa me tsarki sai yazama baya karɓar datti

Babban abinda yake hanamu ganin tasiri da natija ta so shine datti da muke baibayeshi dashi

Annabi Yusuf (As) ya gayawa zulaikha cewa:(kidena kiran kina so na domin shi so me tsarki ne abinda kike nufi kuma datti ne Wanda so baya karbarsa)

Amma yayinda Zulaikha ta riski so na gaskiya saigashi har aure ya hadata da Annabi Yusuf

To irin dattin da muke gogawa so sun haɗa da

Yaudara
Qarya
So saboda wani dalili
Kamar kyau ko dukiya ko muƙami

Domin asalin abinda zuciya take yiwa so shine (jamalul mutlaq)

Sannan duk abinda kaga zuciya ta dimauce da sonsa to ta hango tajallin wannan jamalar ne a cikinsa

Saboda haka da zamu dinga kallon Allah a cikin komai da kowa sannan musami narkewa da zagwanyewa a cikin Allah da mun zauna lafiya.

Allah kabar mu da Soyayyar Manzo Da Ahlinsa

Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Allah ta'ala ka gafartawa mawallafin rubutun nan, ka sada shi da ceton fiyyayen halitta (saww).
    Har yau muna kewar rashinka a tare damu ya shaheeed.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post