Me yasa Ake Mana Aure A Makare ????



- Wannan dukkan matsalarmu ce kesa ba'ayi musu aure da wuri, shiyasa suke samun matsaloli. Wasu kuma hakan ke saka su kaucewa hanya. Mune waɗanda muke haifar da matsololi akan aure, mun saka yanayi daban-daban akai, bacin Manzon Allah (S) ya koya wa Musulmi su aurar da ƴaƴansu in suka kai minzalin shekara 10.

-Kamar yadda kowa ya sani, ƴar Manzon Allah (S) Fatima Azzahra (S.a) Manzon Allah ya aurar da ita tana ƴar shekara 10, ta gama shekara 9 ta shiga na 10, lokacin Manzon Allah (S) yayu mata aure. Manzon Allah (S) ɗin da kansa ya auri wasu daga cikin matansa a wannan shekarun, idan muna ganin shekara 10 sun gaza to a ƙalla12, 13 ko 14.

-Amma iyayensu sunce sai sun je Makaranta, ko sai sun koyi yadda zasu riƙe gida, wannan maganar banza ne. Allah yana faɗa cikin Qur'ani "Talakawanku zamu jinkirta arziƙinsu", kuma Allah (T) a ko wanni lokaci shi mai faɗar gaskiya ne. Ya ƙara cewa; "Idan suna da buƙatu, Allah zai azurtasu da alkairansa" Sutatun Nor aya ta 32, wannan daga cikin Qur'ani ne, kuma kunji abubuwa da yawa makamantan wannan.

-Madina tana da ƙarancin yawan jama'a, lokacin da Manzon Allah yazo, sun zama mazauna 10,000, duk da haka Manzon Allah (S) ya aurar da dukkan matan, kuma idan mace mijinta ya rasu ko aka kashe shi a Yaƙi, Manzon Allah zai ƙara shirya mata wani auren, idan na biyun shima ya rasu ko aka kashe shi, zai ƙara shirya mata aure na uku, ta yadda ba wata mace da zata zauna ba a miji.

-Asmaa tana gauruwa mijinta Jafar Ibn Abu Talib bayan an kashe shi a Mu'ta wani waje a Ƙasar Jordan, don haka ta auri wani mijin, wannan miji shima ya rasu ta ƙara aure na uku. Dukkanku kowa yaji labarin Hamza, shugaban Shahidai , bayan shahadarsa matarsa ta auri wani mijin, da mijinta na biyun ya rasu ta ƙara aure na uku.

-Muslunci yana koya mana bin hanyar Manzon Allah ne, kowa a cikinmu dole yayi biyayya wa Manzon Allah ba tare da shakku ba, Manzon Allah (S) ya fimu sanin abinda ya kamata. Duk da cewa Muhammad ɗan aiken Allah ne, idan wani Krista ko Bamajushe yaƙi yarda da wannan, a ƙalla zai yarda Manzon Allah wayayyen mutum ne.

-Dole mu hanzarta aurar da ƴaƴanmu mata da gaugawa, wannan shirmen maganganun ba daidai bane. Haka ma yaranmu maza, suma dole yazam munyi musu aure da wuri, koba komi zasu gujewa aikata abinda Allah ya haramta. Dukkanmu munji dangane da Salman, Shi'a da Sunnah sun yarda dashi, harma yana da kushewar da Sunnah, Shi'a ke zuwa ziyartasa suyi salloli, kuma yana da muhalli irin na Sayyada Fatima Ma'asooma .

-Kuma suna bashi muhimmanci sabida ya bada gudunmawa, Salmanul Parisi, shi dan Parisa ne ya haɗu da Manzon Allah kuma ya karɓi addinin Muslunci, bayan Manzon Allah yayi wafati yayi tafiya zuwa wurare guda 4.

Ɗaya daga ciki shine Isfahaan.
-Akwai wani waje a Isfahaan ana kiransa da 'Jey', nan ne kuma har yanzun Salman yake, kuma shine Gwamnan Damaska, daga baya kuma ya zama Gwamnan Baghdad a wancen lokacin ana kiran wurin 'Mada'in'. Shine Gwamna a wannan waje har yai wafati, kuma Ƙabarinsa yananan a wurin da zakuso kuje ku ziyarta. lokacin da Salamn yazo Mada'in ya auri wata mace, sun zauna a wani gida da suke tare da wasu iyalan (kamar gidan haya).

-Ba kamar yanzun ba da ko wacce take son ta zauna da kanta ita kaɗai, wani lokaci Salman ya shiga gidan yaga wata yarinya tana wasa a wani sashi, ya tambaya: "wannan yarinyar wanene? Suka ce: "ita ƴar ɗaya daga cikin mazaunan gidan nan ne" ya ƙara tambaya:

"wanene Mijinta?" Suka ce; "bata da miji" Sai yace Naji Manzon Allah (S) yace, "Idan mace takai lokacin balaga, ba'ai mata aure ba duk wani zunubi data aikata za'a rubuta akan iyayenta". ya tambayi iyayenta, "Me yasa baku aurar da ita ba?"

-Wata rana wani Namiji yazo wajen Manzon Allah, mai suna Ak'kaf, a wannan lokacin mutane basu saka irin wannan sunan. Manzon Allah (S) ya tambayeshi "kayi aure?" kamar yadda yake tambayar dukkan saurayi majiyin ƙarfi. ya tambayeshi; "kanada mata? sai yace, "A'a". Manzo ya ƙara tambayarsa, "kuma jikinka lafiya lau?" yace, "eh".

-Yace, "kana da ikon yin aure?" yace, "eh", Manzon Allah (S) yace, "kai ɗan uwan shaidanu ne, kuma ɗan uwa ruhbanawan nasara", ma'ana kai ba Musulmi bane. Don haka kai ruhubanin Nasara ne, kuma ɗan uwa ga Shaiɗanu" nan ya harzuƙa yace, cikin lokaci zan nemo mata, kuma ya aikata hakan.

-Kuyi tunani abinda yake faruwa a tarihin abinda ya shafi aure, kamar mallakar gidane ko cin abinci ko tafiya, kowa yakan aikata su, amma in aka koma magannar samari saimu maida abin mai wahala garesu. muna cewa sai sun gama karatu ko sabis ɗin aikin soja, da wasu matsalolin da kai ka sansu.

-Waɗannan matsaloli ne da mu muka ƙirƙiresu, Ko yaya ne muka rage matsaloli aure zai zama mai sauƙi. Imam Ali (As) yana faɗa cikin Nahjul Balaga, "Idan kabi a hankali zaka cimma buƙatunka". Idan zakai tafiya daga nan zuwa Tehran, matuƙar ka dauki kayan da yakai Kilo 100 baza ka taɓa kaiwa iran ba, amma idan ka ɗauki Kilo 5 cikin sauƙi zaka isa cimma manufarka. dole mu bawa aure muhimmanci.

Da fatan iyaye zasu farka daga barci su dawo hayyacinsu.

-Ayalullah Sayyid Muhammad Shirazi
Fassara daga
┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post