Duk 'Dan Adam Yana da Wasu Nagarta Guda Biyu ...!!!


-Ruwaya mai inganci yazo tatsan-tatsan daga Abu Abdallah Ja'far Bin Muhammad (As) a cikin littafin Aamali na Sheik Al-Mufid cewa;
"Ɗan Adam yana da wasu nagarta guda biyu...
1- Nagarta a garinsu
2- Da kuma a yayin tafiya
-Nagartar da yake da a garinsu sune: Samun dammar Karatu daga Al-Qur'ani mai girma, Samun damar halartar Masallaci, Zama cikin mutane na kirki, da kuma samun yin tunani akan al'amarin addini.

-Nagarta da yake da yayin tafiya: Ya haɗa da tallafawa abokan tafiyarsa da kayan masarufi, Gaggaisawa ba tare da yin wasa da abubuwan da Allah maɗaukaki baya so ba, Da barin abubuwan da Abokan yafiyansa basu so iya iyawarka, Kuma kada ka bada labari akansu bayan kun rabu a tafiyarka dasu".
-Fatan Zamu amfana da wannan yazam mun ɗauki ɓangarorin mun saka su cikin rayuwarmu, yayin kasantuwa a gidane ko lokacin tafiya.
_____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
September 16 at 9:06 A

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post