A Facebook:- Kamar Wannan Ake Kira Yaudara !!!



-Da yawanmu bamu san mecece Zuciya ba shiyasa muke badata ga kowa a kuma ko ina, amma da zamu san muhimmacinta a rayuwarmu da sirrorin da take adanawa bazamuy wasa da nema mutumin da ya dace mu mallaka mai ita ba.

-Mafi yawan lokuta ƴan mata da samarimu sukan tsinci kansu a soyayya irinta 'Social Media' amma da yawa saika ga suna maganar yaudara, ko wani ya fito yana nuna alhinin abinda ya faru dashi bacin shi ya jawa kansa.

-Mallaka zuciya wani abu ne mai buƙatar nazari da bincike ga wanda ya kawo ƙoƙon barar zuciyarmu, amma bamu ɗaukar hakan da muhimmanci sakamakon rauni irin namu, yana da kyau muke ɗaukar darasi.

-Bai kamata wani ya ɗana 'Tajriba' a gabanka ba, kaima kuma kazo ka ƙara hawa kan hanyar da ya hau, wannan aikin shirme da rashin tunani ne, mu kiyaye faɗawa Soyayya da ko wanni/wacce mutum a ko ina ba tare da sanin ainihin wanene shiba, shiyasa zurfafa bk cike keda gayar muhimmanci.

-Zaifi kyau, mu gina soyayyarmu ɗa tubalin da bazai saurin ruguje wa ba, domin zuciya wata abace da bata da kashi, tana da rauni da kuma saurin taɓuwa a lokacin data rasa muradinta kuma bu mafi soyuwa a gareta.

-Adon haka yakamata muɗau matakan gyara, kar idanuwanmu suke rufewa yayin neman abokan rayuwarmu, wanda muke burin gina rayuwa dashi ta dun-dun-dun domin aure abu ne da ake fatan ya ɗore sanadiyyar tarayyarku ya zam ƙarshe shine ɗauwamarku tare a gidan Aljanna.

-Duniya da lahira gaba ɗayansu an ginasu ne akan so, to, mai zaisa muyi wasa da abinda muke so? Kuma muyi wasa da neman wanda ya dace a so?.
-Facebookers a kula da ƴan ƙwangwaren soyayya domin ka iya soyayya da namiji mace kuma tayi da mace ba tare da sani ba, me zakaji inka fahimci wanda kake so bama ɗayan jinsi da yakamata kaso bane?

-Abu ne na tunani da hankali, mai ilimi da hankali shi zai gane......

┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post