Yan uwan Juna da Basu Rubuwa..!!



IMANI DA AIKI
 ーーーーーー
@Ma'asumah nigeria News Updates

➝Yazo a cikin Kanzul Ummal, Manzon Allah (S) yace; "Imani da aiki 'yan uwan juna ne guda biyu dake damfare cikin inuwa guda. Allah baya karban daya ba tare da dayan dan uwansa ba".

➝Manzon Allah ya kara fada a wani hadisi, cewa; "Zunubi baya fitar da mutum cikin mu'minai, kuma kyakkyawan aiki shike tabbatar da imanin mutum."

➝Manzon Allah (S) yace; "Imanin dayanku baya cika, har sai ya soma dan uwansa abinda yake soma kansa. Kuma saiya ji tsoron Allah a dukkan ayyukansa".

➝Imam Ali (As) yace; "Mai cikakken imani a cikin ku, shine wanda yake da kyawawan dabiu".

➝Imam Ali (As) bai gushe ba yana fadi a wata ruwaya, "Imanin mutum bai kammala saiya siffantu da abubuwa uku. 
1- Hankali
2- Hakuri
3- Da iIimi".

Allah ya kara mana imani da aikata aiki na gargaru.

    ᕙ(⇀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ↼)ᕗ

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post