DAGA KALLO DAYA!!!


@Ma'asumah Nigerian News Update@, tare da Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ.

Fita na Daya (1)

MASOYIYATA TA GASKIYA.

-Lokacin dan fara ganinta, na kasa saita hankalina, ta hadu don haka ta sace zuciyata. Bansan na tsunduma cikin kogin sonta ba saida naje makwanci na.

-In manta da kalar fuskarta, hotunan sunki goguwa a zuciya ta, ban ankara naji barci ya kauracewa idanuna, tunani nake a ina zan sake ganinta ko don na sauke hakkin idanuna.

-Matsuwa nai gari ya waye inje in kai gareta. Saidai tunanin da nake bansanta taya zan fara nemanta ba. Haka dama so yake? Ta dauke hankali na.

-Washe gari, ranar Juma'a naci kwalliya zani majilasa tare da abokaina, kamar daga sama naji an kirawo sunana. In waiga saina gan kamar a mafarki, itace amma ya ai tasan sunana.

-Tunda nake ban taba jin wata ta kira sunana da daddadan sauti kamar yadda ta furtaba. Kai sautin muryarta yafi ce ayo misali.

--Irin zakin sautin nata kama yake dana tatatcen sauti daga computer mai dadin saurare. Mamaki ya rufe ni in amsa mata abin ya gagara, waige-waige nake in gani shin dagaske ni take kira?

-Tabbas, ashe nidin ne, da zuwa na gabanta, naji zuciyata na dukan talatin-talatin ashe haka so yake don ta tafi da qalbi na.

-Anan na saita natsuwata, na amsa mata da barka da war haka ya Ma'abociya kyawu da daddadan sauti, tayi murmushi mai kayatarwa wanda saida 'Dimple' dinta suka fito.

-Abin ba'a cewa komi domin ta hada komi, zan kara magana. Saita tari Numfashi na sautin da ya fito shine hakika ka sace zuciyata. Nayi kokarin na danne in ki bayyana wa, amma hakan daidai yake da hana wa kaina jin dadi da muradin zuciyata.

-Taya akai haka lokaci guda ka sambade zuciya ta? Na kasa gane sirrin dake dauke cikin fiskarka kallo daya nai maka, amma sam na kasa manta kalar fiskarka.

Wanna yasa nace bazan kasa a guiwa ba wajen gabatar maka da bukatar zuciya ta. Dalili kuwa nasan samun irinka abu ne mai wuya da a karnoni sau daya ake samu.

-Ina Sonka sauti da ya faranta rai da zuciya, naji dadin firta min So da tai wannan ya tabbatar zata kula da miskinin masoyinta.

-Banyi kasa a guiwa ba na amsa mata da karbar sakonta, musmushi take mai kashe a film din yan India......


Muci gaba ne ko mu tsaya???????

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post