Akoyi Zama da Matsala ba Maganinta ba! Sheik Yaqub Yahaya 26/10/2019.

Kadan daga cikin Jawabin Sheik Yaqub Yahaya wakilin 'yan uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky na garin Katsina wanda yayi a yau Asabar 26/10/2019 a wajen Mu'utamar na Dandalin Sharifai a Markaz Katsina.

Idan Mutane sunkai dari (100), acikinsu (20) nada matsala sauran (80) sukoyi zama da masu wannan matsalar kaga baza'ayi saurin gane akwai masu matsala acikin (100) ba domin sunfisu yawa sosai.

Zama da Matsala tamkar gano Allura cikin duhu ne, kowa zai bada tasa gudumuwar domin ganin angano wannan Allurar, wani zaizo da fitilar Caza, wani da fitilar hannu, wani da fitilar wai, wani da acibal-bal, wani zaizo da kyandir, wani zaizo da fitilarda ko Fura bata haskawa ya kunna domin bada tasa gudumuwar dan ganin shima ya taimaka da irin tasa gudumuwar wajen gano wannan allurar.

Idan kowa ya haska aka gano wannan allurar kaga kenan kowa ya bada tasa gudumuwar, haka yakamata ace ankoya domin magance matsalarda ke cikinmu har zuwa lokacinda Allah zai bayyana komi domin Allah ba sauri yake ba!.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post