@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
FITARSA ZUWA IRAQ RANAR TARWIYYAH
Bayan shawarwarin da wadannan Sahabbai suka
bawa Imam (A.S) kan cewa kada ya fita zuwa
Iraq, da kuma amsar da ya bawa kowa
gwargwadon matsayin sa, sai ya fita daga garin
Makkah zuwa Iraq.
Ya fita ne ranar talata 8th Zul-Hijjah, 60 (B.H)
tare da dashi akwai mutane 82 daga iyalan gidan
sa (A.S), da mabiyansa da kuma masu tarayya
da shi. Cikin tafiyar tasu sun riqa samun jama'ah
masu yawa da suka kasance tare kan wannan
manufa tasa.
Akan hanyarsu labari ya zo musu cewa an kashe
Muslim Bn Aqeel (A.S), kuma a rinjayi mabiyansa
da ke Kufah, sannan shima akwai barazanar rasa
ransa. Saboda haka aka ba shi shawarin cewa su
canza hanya da kuma manufar inda suka dosa.
Imam (A.S) yayi jawabi ga jama'ar da ke tare da
shi kan hatsarin da ke gabansu, saboda haka
wanda yaso zai iya juyawa babu wani zargi a
kansa.
Su kuma iyalan Aqeel suka ce ba za su juya baya
ba har sai sun isa ko kuma su ma su dandani irin
abinda dan'uwansu Muslim ya dandana. Jin
wannan kalmomi na jajircewa da sadaukarwa
yasa Imam (A.S) yace;
" LALLE NI BABU WATA RAYUWA TA ALKHAIRI
GARE NI MATUQAR BABU KU!"
Daga nan suka cigaba da tafiya har suka hadu da
wani da ake kira Hurri Bn Yazeed. Bayan ya
tambayi cewa su suwaye da kuma inda suka
dosa, da kuma amsar da Imam (A.S) ya ba shi
sai yace;
" To, gaskiya ni an turo ni ne don sanya ido a
kanku kan cewa kada ku bace min har sai anzo,
amma yanzu ku canza hanya, zan tafi na basu
labarin cewa kun bace min ban ganku ku."
Da Imam ya tabbatar cewa ba su da nasara a
Kufah sakamakon aikin da Ibn Ziyad (L.A) yayi
na kisan mabiyansa da kuma tsoratar da wasu
bisa umarnin Yazeed Bn Mu'awiyyah (L.A) tasa
Imam ya canza hanya.
Za mu cigaba insha Allahu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda
08137925034-08126385470
Tags:
MUNASABAR ASHURA