DAGA CIKIN DALILIN FITAR IMAM HUSSAIN A.S


 ✍️
RAHAMA ABDULMAJID


Wasu karin dalilan fitar Imam Husaini har da imani da Mu'ujiza da mutanen da suka ba Shi tabbacin fitowa da ma abubuwan bakinciki da ya tara wadanda suka kaishi bango.

A zamanin Imamu Husaini mutane sun fi tinani akan imani fiye da hankali zalla. Ba a fi shekara talatin da faruwar Yakin Badar da Ahzaab ba wanda Imamu Husaini ya ji Allah Ya turowa Kakansa AS (Junudan Lan tarau ha). Sannan an saukar da ayoyin (kam min fi'atin qalilatin Ghalabat Fi'atan kathirah)

Sayyidnal Husaini ya sami tasiri da kuma jiran wannan muujiza akan Zayaad la'ananne. Sai dai Allah Baiyi hakan ba saboda dalilai mabambanta

2 Tarihi ya nuna mana Sayyidnal Husaini an shirya masa gadar zare a wannan fita da makirci wanda tabbas basu sa ya zaci ba zai yi nasara ba. Maganganun wasiyya da yayi basu saba na kowane kwamandan yaqi ba ko zai dawo ko ba zai dawo ba.

3 Sayyidi ba kamar Imamu Hasan ba ne wanda ya rayu sosai a Kufa ba. Ya rayu a Madina ne Inda ake rara hadisin Tsarkinsu da laantar wanda ya tabasu. Hakika Mutanen Madina basa gigin mantawa da Ahlul Baiti kamar mutanen Kufa da Shaam, wannan ya sanya idan Jikan Annabi SAW na madina sai dai a kashe Shi da magani a lokacin amma ba takobi ba. Sannan ko a Karbala Wanda suka fito yakarsa sun tsorata sun girmami abinda zasu yi domin a tarihi mai zaman kansa (ba na Shi a da sunna ba) an ruwaito Imamu na nunawa wasu daga mayakan takobi duk da suna kewaye da shi amma su kauce, Sannan Shi kansa jagoran kisan bayan yayi abinda yayi an ganshi yana zagaye Kaaba yana cewa (Allah Na San ba zaKa yafe min ba)maimakon neman gafara
Wannan qisoshi idan har sun inganta suna nuna girma da kimar Imamu Husaini a lokacin Wanda zai yi wuya ya yarda akwai me iya sarar wannan tsarkakakkiyar tsoka da takobi. Eh an soki mahaifinsa da wuka, Amma a wajen sahabbai jininsa ya fi na mahaifinsa tsarki don sun ganshi kan gadon bayan Annabi SAW a sujjada kamar yadda sukan ga Annabi SAW na sunbatar har bakinsa a yayinda mahaifinsa na cikinsu ne yana cewa Annabi SAW bi abi Anta wa Ummi. Kenan shi VIP ne har akan mahaifinsa.

Inda nake so mu yi adalci shine Ittifaaqin musulmi na duniya basu ji dadin haadisar Karbala ba. Sunna dukanta ta yi kukan wannan danyen aikin da ummahaatun malamanta. Mu lura da kyau malaman sunnah sun kasa sanyawa yayansu suna Yazid duk da matukar maanar sunan a sassaukan larabci da tashensa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post