YADDA MAKIYA SUKE KOKARIN BICE HASKEN MANZO(S):

Daga Gefen dama Wakilanmu haruna shu'aibu ne ke karbar kyauta ga mlm Musa Hassan shinkafi wajen tarin karawa juna sani na wakilan ma'asumah a katsina


_inji SaSayeed Ibrahim Zakzaky  (h)
Daga Shafin [M.N.N.Updates]

To,da yake shaksiyyah ce ta Manzon Allah (S),Wanda yake
shahsiyyah ce bariza wanda a tarihin bil'adama ba a yi kamarta
ba.Kuma duniyar makiya sun yi iya kokarinsu wajen bice
wannan haske, Makiya na gida da na waje, Makiyan gida ta
hanyar kokarin bayyana shi wannan manzo a matsayin kamar
wani mutum ne 'Aadi', Makiya na cikin gida saboda sunyi
amfani da sakon da Annabin yazo da shi wajen kafa
mulki,to,amma kuma ba shahsiyyar Annabin suke so ba zai
yiwu ba .Don suna ganin ba zai yiwu su kafa mulkin da sunansa
su yi koyi kuma da shi ba.Saboda hanyar ce ta riko da gaskiya
,Wanda kuma sun san ba zai yiwu ba. Na farko; ba sune
Ahliyar su rike wannan al'ummar da sunan wannan Annabin da
kuma sunan wannan Addini ba.Sun san da hakan!
Na kuma ga mulki a hannun su,ba kuma zasu rabu da mulkin
ba.Ba za suba ma'abotan wannan addini riko da abin ba,su
kuma bazasu iya kamanta abin ba,ko da wai.Saboda haka
basuda wani abin da ke gabansu illa su rika nuna Annabi a
matsayin shi ma mutum ne kamar kowa,wanda yake kafa
daula,yake mulki.Don ham wadansu abubuwa da suke so su
yi,sai su samu ace musu shi ma Annabin ya yi.To haka nan
suka dinga bayyana shahsiyyar Annabi a wani irin
kamannu.Kamar na wani mutum da ya kafa daula(Mutum
'Aadi').Kamar yadda sarakan duniya da suke kafa Dauloli suke.
Alal misali;Kamar Janjiskan.Janjiskan ya kafa daula,ko da
yake shi bayan da dadewa ne.Ya kafa daular da ta mamaye
duniya,Don ya dauka kamar ya zo ne da wani 'Mission' na
duniya.kamar yadda suke cewa (a tatsuniyarsu);wai ya zo da
wani abu a hannunsa a dunkule haka,aka bude aka ga ko
wadansu abubuwa ne suka ce?To ana tsammanin dai wannan
wani jariri ne na musamman.To,sai shi kuma ya dauka (Ko
masu duba) suka ce masa;Ai zai mallaki duk duniyar nan ne.

To sai ko ya sa gaba wajen mallakar duniya.
A wani wuri nake karantawa suna fada dangane da
janjiskan,ana cewa;shi Janjiskan mutum ne wanda yake mai
kakkausar zuciya wanda ya ci garuruwa da muguwar barna da
ta'asa.Murkushe gari ake yi.To,amma sai wurin su ake ganin
cewa;Inda ba don shi mutum ne wato wanda yake hazaki
ba,ya aka yi ya iya kafa(Mulki)daula da ta ci kusan fiye da
rabin duniya?

Na'am,Janjiskan ya kafa daula,kuma bayansa ya'yansa sun
cigaba da wannan.Dansa ya cigaba har ya zuwa 'Dawr' din
daya kawo har ga jikansa ma Holako, wanda yake ya ci gaba
da irin wannan ta'asa irin ta kakansa. Salon al'amarin shi ne
;Idan suka ci gari da yaki,sukan kashe duk jinin sarauta ne,don
kar wata rana wani ya dago ya sa rai.A nizamin da wanda yake
jinin sarauta ne ke mulki.Idan ba gidan sarautan,shi kenan.
To,daga baya a lokacin Holako ma sai ya zama ma (ko lokacin
janjiskan),ba su barin gari . Don Birnin Beijing wannan da yake
babban Birnin Kasar sin,Janjiskan ya rabdu shi (gaba daya), ya
kona shi yayi watanni yana cin wuta .Bai bar duk mai rai ba
,hatta ko kwaro ne.Bayan ya rutsa da garin ,sun kulle garin sun
hanashi shiga, ya ce;To ai kuwa za Ku mutum da yunwa .Ya
rutsa da su ta ko'ina ,har abincinsu ya karanta,sannan daga
baya ya cinna wa gari wuta,ya baje shi,ya kashe kowa da
kowa.Da mutane da dabbobi da tsuntsaye da kwari!
To,haka shi ma Holako ya yi.shi ma yana rubde garuruwa ne
gaba daya.Ya ma rubde Birnin Baghdad,ya ce;kar a bar Tubali
a kan Tubali.Aka rubde garin, kuma shi sarkin musulmi nq
wannan lokacin,Al-Abbasiy,ya ce; bai kamata a ainihin shekar
da jinin sarki ba,sai aka nannade shi a darduma aka dinga
tattakewa,sai da ya mutu aka wurga a kogin futat.

To,ta haka nan suka kafa Daula, wanda lokacin Holako ainihin
Misra suka taka mishi birki,mulkin Bamalik, su suka taka mishi
birki, banda haka ma da ainihin ya shiga duniyar Turai ma.Taka
burkin da Misra suka yi mishi sai ya zama mulkin su bai kai ya
ci Turai ba.Amma ya ci mafi yawan Asiya har da China. Su a
wurin su tunda ya iya kafa daula babban mutum ne. Kamar
wani 'Genius' ne. Amma alhali a tarihi an nuna shi Janjiskan
ma baya kaunar karatu,ba ruwanshi da rubutu,yana gaba da
rubutu. Daga baya amma wasu sun ce ya ce mutanensa suma
su koyi rubutu da karatu.Amma dai shi bai ga amfanin karatu
ba. Sam bai iya rubuta sunansa ba ma.

Daga wakilin Ma'asumiya Nigeria News Updates Auwal M
Tukur

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post