TAMBAYA DA AMSA A BISA FIQIHU NA MAKARANTAR AHLULBAIT [A.S]

mlm zakzaky (h)

Hujjatul Islami Walmuslimina Sheikh Ibrahim Abdullahi.

Tambaya: An Ce Kura Mai Kauri Idan Ta Shiga Makogwaro Tana Karye Azumi, To Shi Kuma Hayakin Tiyagas Fa (Teargas) Musamman Ga 'Yan'Uwa Masu Muzazahara ?

Amsa: A fatawa ta Sayyid Qa'id shi ne cewa, idan Hayaqi ya kai mustawa da kuma kauri wanda yake bata Azumi, to idan ya shigarwa mutum a maqogwaro to shima yana karya Azumi kamar Qura, saboda haka dangane da abin da ya shafi masu yin Muzahara,  kai koma a wane irin yanayi ne, idan mutum ya ga cewa ga hayaqin Tiyagas nan kuma zai iya shigar masa maqogwaro, to yakan iya samun dan Hankicif ko wani tsumma da zai toshe bakinsa ko hancinsa.

Mai wannan tambayar ya qara da cewa, misali masu Muzaharar suna sane da cewa idan suka tafi Muzahararnan za a harba musu Tiyagas, to idan suka fita wannan Muzaharar kuma ya zamana an harba musu Tiyagas din, shin sun karya Azuminsu dagangan kenan ? 

Ba haka bane, domin su basu fita da don a harba musu Tiyagas ba, su sun fita ne domin neman haqqinsu, shi kuma wannan da ya zo ya harba musu Tiyagas shi ne ya kawo musu takakkiya, ba sune suka je suka dibi Tiyagas din ko hayaqin suka zuba a maqogwaronsu ba, ballantana ya zama daganganci kenan, wannan mujarradin zato ne, cewa za a iya harba musu Tiyagas din ko ba za a harba musu ba, saboda haka idan aka harba musu kuma ya zamana cewa ba su suka ga damar su shaqi wannan Tiyagas din ba, ba kuma su suka kai kansu ya zamana sun debi Tiyagas din sun shaqa ba, to basu karya Azuminsu daganganci ba.

Azumi yana karyewa ne idan mutum ya shaqi wadannan ababen qura ko hayaqi dagangan. Amma idan a'a mutum kawai ji ya yi bada nufi ba an harba masa Tiyagas har ya shigar masa maqogwaro, to inde yana Azumi a wannan lokaci to Azuminsa yana nan domin ba da ganganci ya yi ba, Allahumma sai dai idan ya zama Muddar ne. Abin da ake nufi da Muddar shi ne cewa, an harba Tiyagas ga hayaqin Tiyagas din mutum yana kallo ya turniqe amma kuma dole sai ya bi ta cikin wannan hayaqin, to yanzu da ya bi ta cikin hayaqin, idan ya shigar masa maqogwaro to Azuminsa ya karye, amma kuma ramuwa kawai zaiyi.

         Daga. Zauren Al-ahkam.
Rbtw: Bilal Nasir Umar Sakkwato.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post