DAN SHI:A BAYA KYAMATAN MUTUM KODAMA KAI KIRISTANE

ma'asumah nagerian news updateu

DAN SHI:A BAYA KYAMATAN MUTUM KODAMA KAI KIRISTANE

-Inji Halimatu Sunusi Udawa a hirar da wakilinmu Ammar Umar Udawa yayi da ita a Cikin kwanakkin nan asha karatu lfy

@Daga Ma'asumah Nigerian News Updates

Ma'asumah: Assalamu Alaikhum Zamuso muji cikakken Sunanki?

Halimatu Sunusi: Nidai Sunana Halimatu Sa'adiyya kuma ina da shekaru 22yr a duniya ina zaune ne a Udawa jihar Kaduna.

Ma'asumah; koya rayuwarki ta faro kafin ki tsunduma a 'Harka Islamiyya'?

Halimatu Sunusi:  Da farko ina yarinya na tasone a gaban iyayena, Wanda dukkansu Ahlul sunnah ne (Izalah) a lokacin ina zuwa makarantar Islamiyya a wani gari da ake cema Jibia can kusa da Nijar, rayuwata ta faro ne cikin tsafta Alhamdulillah.

Ma'asumah: To koh, menene ya baki sha'awar shiga (Shi'ah) duk da kuma gashi kince iyayenki ma'abota Ahlul Sunnah ne?

Halimatu Sunusi: Tausayi da jinkan ('yan shi'ah) da rashin nuna kyama ya sabbamin shiga Shi'ah. Akwai wani abun burgewa daya faru Wanda yayimin dadi sosai wallahi wani lokaci nakan ga 'yan shi'ah suna kaiwa kiristoci ziyara kuma su bisu har cocinsu batare da wani fargaba ba, kuma wallahi zai yi wuya kaga Dan shi'ah ya wulakanta ka sun san darajar mutum wannan abun ya sanyani Ina ta nazari akansu har nafahimci inda suka dosa, kuma nima nabisu domin a zahirin gaskiya sune irin mutanen farko muminai.

Ma'asumah; Ko akwai jarabawar da kika fuskanta bayan kin fahimci 'Harka' koda daga iyaye 'yan Uwa ko mutanen gari?

Halimatu Sunusi: Abubuwa dayawa sun faru dani, a halin yanzu bana tare da iyayena sun cireni daga cikin 'yayansu sun koreni daga gidansu, Amma yanzu Na auri Dan Shi'a Wanda shiya rikemin mutuncina harzuwa yanzu shekaru 4, kenan bana tare da iyayena duk da kuwa muna a gari daya amma saboda nazabi (shi'ah) mun raba hanya dasu harzuwa Yanzu.

Ma'asumah: Wani irin canjin yanayi kika samu na rayuwa bayan fahimtarki harka?

Halimatu Sunusi: Tun taso wata ban taba jin rayuwa kamar ta wannan ba wallahi (murmushi) kasancewata mabiyin iyalan gidan Annabi(s).

Ma'asumah: Mungode kwarai.

Halimatu Sunusi: Nima nagode Allah ya daukaka ku.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post