Bayan kammala rantsar da shi a filin taro dake garin Gusau ranar Laraba sabon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle PDP ya kaddamar da shirin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana kyauta a jihar.
Matawalle yace gwamnatin sa za ta yi amfani da kwararru da masana domin samar da ci gaba a jihar.
” Mata da yara kanana na fama da rashin samun kiwon lafiya na gari a saboda haka lokaci da za a canja haka.
Ya kuma ce gwamnatin sa za ta maida hankali wajen kawo karshen matsalolin rashin tsaro da ake fama da shi a jihar.
” Za mu tabbatar mutane basu daukar doka a hannunsu, sannan zamu yi kokarin kawo karshen yin garkuwa da mutane, kisa, takura wa mutane da sauran su.
” Za kuma mu inganta fannin ilimi, samar da aikin yi da kawar da tallauci ganin cewa rashin su na daga cikin matsalolin dake haddasa miyagun aiyukka a jihar mu.
” Sannan kuma nan da wasu makonni masu zuwa zamu tsara shiri ba wa ya’ywn ilimi kyauta a jihar Zamfara.
Matawalle yace gwamnatin sa za ta hada hannu da gwamnatin tarayya da sauran hukumomi domin inganta rayuwar mutane a jihar.
Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP da su rika girmama na gaba da yi wa dokar kasa biyayya.
Idan ba a manta ba Hukumar Zabe mai zaman kanta ta bayyana Bello Matawalle na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar.
Shugaban hukumar ne ya sanar da haka a doguwar jawabi da yayi wa manema labarai a hukumar a Abuja.
Mahmood Yakubu ya ce bisa ga hukuncin da kotun koli ta yanke, Jam’iyyar PDP da ta zo na biyu a zaben ne za ta dare kan kujerun mulki a jihar.
An haifi Bello Matawalle a garin Maradun ranar 12 ga watan Disamban 1969.
Ya yi aiki a ma’aikatar Lafiya a tsohuwar jihar Sokoto, ya yi malamin makarantar Sakandaren mata dake garin Moriki da na garin Kwatarkwashi da ma’aikatar albarkatun ruwa, Abuja.
A 1998 Matawalle ya shiga harkar siyasa a karkashin inuwar jam’iyyar UNCP.