SHARI'A NA SA ALBARKA A QASA __


[_FILIN JAGORAN GASKIYA_]

SHARI'A NA SA ALBARKA A QASA
__Inji Jagoran Gaskiya [Sayyid Zakzaky (h)]
_Kamar yadda ya zo cewa idan Annabi Isa (AS) ya dawo bayan qasa (duniya) zai tabbatar da shari'ar Musulunci, wanda a sanadiyyar wannan, mutane da yawa za su iya ci daga itacen Ruman guda.
In ka taba ganin itacen Ruman bai yi tsawon mutum guda ba, ba kuma yana da tsowo ne ba, kuma yana iya yin 'ya'ya kamar guda goma zuwa sha biyar, to aka ce kamar mutum arba'in za su sha inuwar itacen Ruman qwara daya, kuma za su ci su qoshi.
Kuma mutum arba'in za su iya shan nono daga Tunkiya guda ko Akuya. Wannan kuma aka ce ba wani abu bane illa (sakamakon) tabbatar da shari'ar addinin Musulunci, wanda yake sai Allah Ta’ala ya yalwata arziki ya yadu, a ci Kaji da qwayaye. Kuma 'ya'yan itatuwa, mutum idan ya yi yawo da kwandonsa a qasan itaciya sai ya cika kwandon da 'ya'yan itaciya, saboda albarkacin tabbatar shari'a.
Kuma ya zo a hadisi cewa, duk ran da fajiri ya mutu, to da mutane da dabbobi da tsire-tsire suna hutawa. Domin fajirci yana sa albarkar arziki ya ragu. Wato in wani fasiqi ne yake ta
fasiqanci, to wannan fasiqancin nasa na cutar mutane, tunda yake cutar tana rage tsatso na haihuwa, kuma tana sa 'ya'yan itatuwa su daina 'ya'ya, ko kuma su daina albarka.
Kuma yana sa Shanu su daina Nono mai yawa, sai Kaji su daina qwai. In fajirci ya yi yawa sai arziki ya rinqa raguwa, kamar yadda in adalci ya yi yawa sai arziki ya qaru.
Wannan ya nuna ashe yalwatan arziki da quntatuwansa Damfare yake da ibada ta Allah Ta’ala. Wato kenan kar mutum ya ga cewa mutane sun shiga wani mawuyacin hali ya dauka cewa kamar ko rashin iya sanin tattalin arziki ne ko ma manene.
A'a ba wannan bane, al'amari ne daman na Allah wanda yake shi ke yalwatawa, ya kuma takura.
Kamar yadda yake cewa: “duk abin da ya shafe ku na musiba, to abin da hannuwanku ne suka aikata.” Da, da kowane abin da kuke yi zai kama ku, to da ba a ji dadi ba. Da ko kofin ruwa ba za ku samu ba, amma don yana afuwa da dama ne har kukan samu.
__________________________________________
Ma'asuma Nigerian News Updates,
[Jawabin Sayyid Zakzaky daga Littafin Nigeria Ina Mafita]
Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post