_RABON DUKIYA NA ALLAH NE_ __Inji Jagoran Gaskiya[Sayyid Zakzaky (h)]



[FILIN JAGORAN GASKIYA]


__RABON DUKIYA NA ALLAH NE__

__Inji Jagoran Gaskiya[Sayyid Zakzaky]


_Halitta da tafi da halitta duk na Allah ne. Allah Ta’ala ba ya halicci mutane da dabbobi ya zuba arziqin daji da na ruwa ya ce; to ga shi nan ku je ku raba yadda ya yi maku ba ne. A'a,halitta da tafi da al'amarinta nasa ne.

 Har wala yau ya ce ga yadda za a yi rabon. Saboda haka sai Allah Ta’ala ya dauka wa kansa rabon dukiyar, bai ba Sarakai ko Alqalai ba ballantana su yi zalunci. 

Muna iya ganin wannan misali a wajen rabon dukiya(gado), wadda in mutum ya rasu, aka ce iyayensa suna da kaza idan mutumin ba shi da 'ya'ya.
 In kuma yana da 'ya'ya, suna da kaza, mata na da kaza, maza na da kaza, da dai sauransu.
 AllahTa’ala ya raba gado, in mutum ya rasu dukiyarsa ba haqqin Sarki bane, ba kuma na Alqali bane. In ma aka je aka raba, mutum ba zai ce an cuce shi ba. 
Domin rabo ne daga Allah Ta’ala. In ko har ka ga an yi rabo, wani ya ga an cuce shi, to imma dai an yi masa adalci, yana ganin Allah bai yi adalci ba, wa imma dai Alqali ne ya yi masa zalunci, amma in dai rabo ne na Allah Ta’ala, to babu wanda ya fi Allah adalci.

To, haka kuma Allah Ta’ala ya sanya Zakka. Bayan ya sanya Zakka ta zama wajiba, ya kuma sanya wani wajibci, adalci na ihsani wanda ya bari a hannun mutum ya yi daidai gwargwado.
 In ya yi da yawa ya sami lada mai yawa. In kuma ya yi kaxan ya sami ladansa kaxan. In kuma ya qi yi, to ya sami azaba.
 Sannan bayan wannan, ya kuma sanya zakkar nafila domin ya zama rabo da adalci.

To, kuma (Allah) ya damfara arziqin nan naSa da biyayya gare shi. Za mu ga cewa kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa; 

“Ban halicci mutane da aljanu ba, sai don su bauta mani, ba na neman arziqi daga gare su kuma ba na neman su ciyar da ni”.

Da ma a ce an ba Allah abinci ya ci, wannan mustahili ne, domin Allah shi ne Mahaliccin mutum kuma shi ne Mahaliccin abinci. 
Shi ba mabuqaci ne ga abinci ba. Saboda haka ma Malamai sun fahimci cewa inda Allah Ta’ala yake cewa; 
“Ba na son ku azurta ni, kuma ba na son ku ba ni abinci,”
 ba yana nufin za ku tattara dukiya ne ku ce ‘ga shi mun ba Allah ba.’ Wanda ya halicci abu, ka je kana ba shi? Mene za ka ba shi? Ka yi noma ne ka ci alhali kuwa (Allah) shi ne ya yi ruwa da tsiro.
 Da yawa malamai sun tafi da fassarar cewa abin da Allah yake nufi shi ne, ya daukar wa kansa raba arziki da abinci. Allah bai ce su yi wannan ba.

Kuma ya zo cewa in aka bi dokarsa, Allah Ta’ala yana yalwata arziki. Kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa a cikin littafinsa ga Bani Isra'ila,
 “Da a ce Yahudu da Nasara sun tsaida Attaura da Injila, da sun ci arziki daga samansu da qarqashin qafafuwansu.” Misali Allah ya saukar da ruwa daga sama, kuma ya fitar da tsiro daga qasa.
Yanzu mutane sun dauka cewa su rabon arziki kayansu ne. 
Ai sun san arziki na Allah ne. In aka nemi ruwa aka rasa, ai sun san inda sukan nemi ruwa. Ba wani wanda zai je qaramar hukuma (Local Government) (ya nemi a yi ruwa) tunda ba a yi ruwa ba, (ya ce) to Ciyaman ka san yadda za ka yi ka yi ruwan sama.
 Ko kuma gwamnatin jiha (State) ku yi ruwan sama. Ba wanda zai iya wannan. Ko kuma a ce kogi babu kifaye, to lallai qaramar hukuma ta san abin yi.
 Ko kuma itatuwa ba su yi‘ya’ya ba, saboda haka gwamnati ta yi wani abu. Ko ta kafa doka, duk mangwarorin qasar nan su riqa yi da kyau. 
Kuma in Kaji ba su yin qwai babu wanda zai je wajen hukuma ya ce, to Kaji su riqa yin qwai.
 Wannan Allah ke yinsa, kuma damfare yake har wala yau da dokarsa.
_________________________________
Ma'asuma Nigerian News Update,

[Jawabin Allamah Sayyid Zakzaky Daga Littafin, {NIGERIA INA MAFITA]

®__Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post