NASIHATA GAREKI KANWATA HAFSAT MAHADI.

Daga Ahmad Musa MC Suleja.

A yanzu da ya rage abin da bai kai awanni biyu zuwa uku ki zamanto matar aure ba, naga akwai buƙatar na baki gudummawata a matsayina na wanda muka kasance abokan juna a wannan dandalin na sada zumunta.

Kar kiji nace nasiha kiyi zaton zan ta janyo miki ayoyi da hadisan Fiyayyan halitta (S), dan a zatona kasancewarki cikakkiyar musulma zai wahala ki kasa tantance tsakanin halal da haram.

Bari dai kawai zanyi amfani da hikima wajen nasihantar dake cikin nishaɗin da ba lallai yanzu ki fahimci tasirin hakan ba.

Ki sani shi aure ibada ne, duk da wasu na ɗaukarsa a matsayin al'ada da zummar cewa abubuwan da ya ƙunsa ne ibadar, amma dai shi a karan kansa al'ada ne.
Ko ma dai ya abin yake, inason ke a naki ɓangaren ki kalleshi a matsayin ibada tun a matakin farko.

Wannan shi zai baki cikakkiyar damar amfani da duk wata nasiha da mu masoyanki za muyi miki, da ma kuma wacce Mahaifanki za su miki.

Ki sani, nasihar Mahaifanki za ta taƙaita ne kawai akan kiyi haƙurin zama da mijinki lafiya, ki kuma yi duk iyakar yinki wajen yi masa ladabi da biyayya, wato yi na yi, bari, na bari. Kinga kenan a dunƙule suna miki ishara ne da cewa, zaman lafiyarki a ɗakin mijinki ya ta'allaƙa ne ga yanayin irin haƙurinki.

Sai dai a zahiri kina buƙatar nasiha tun kafin akai matakin da za ki saurari ta Mahaifanki, wato kina buƙatar a nusashsheki tun kafin a fara shagulgulan bikin ki.

Tunanin zai matuƙar wahala ki samu wanda zai miki irin wannan nasihar ne yasa naga kyautuwar ni nayi amfani da wannan damar na miki.

Yana da kyau ki fahimci cewa ke ɗin halitta ce mai matuƙar girman matsayi da martaba gami da daraja. Amma ba lallai kai tsaye ki kai ga fahimtar hakan ba har sai kin tsarkake zuciyarki ta hanyar ƙudurcewa ranki da komai za kiyi za kiyi shi ne bisa ma'aunin yanda shari'a ta tsara. Kar kiji nace shari'a kiyi zaton taku ta ƴan boko nake nufi, ina nufin shari'a bisa ma'aunin addinin islama.

Tun a matakin farko ina mai miki nasiha da ki kyautata duk wata shiga da za kiyi a matsayinki na Amarya. Kar ki yaudari kanki da son kasancewa cikin rukunin rafkanannu, waƴanda suke ganin matuƙar Amarya ba ta yi shiga irin ta amaren zamanin yanzu ba bata kyau. Sunfi buƙatar su ganta cikin shigar da take tona asirin duk wata kyakkyawar surar jikinta. A irin wannan shigar ne za kiga Ƙirjin Amarya a bayyane, ma'ana taƙi sakayeshi da wadataccen lulluɓin da zai suturce shi. Yayin da kayan jikinta suka matseta ta yanda ko numfashi ta ja sai anga alamun hakan saboda a matse take.

Zan so ki suturce kanki tamkar yadda Angonki zai suturce kansa. Ki rabu da masu son su ganki cikin irin wannan shigar. Kar ki taɓa amincewa da su yaudareki da cewa "yau ɗaya dai". Na rantse da Allah za ki saɓawa Allah cikin sakanni, amma hukuncinsa yayi ta bibiyar rayuwar aurenki.
Dan haka ina miki nasiha da ki alkinta kyakkyawar surarki ta hanyar suturce kanki da wadatacciyar sutura.

Kasancewar ki kyakkyawar Mace, ba na jin kina buƙatar irin make-up ɗin nan da za kiga ya karkatar da hancin Mace. Ko kusa ba kya buƙatar ɓarnatar da kuɗinki ko kuma kuɗin wanda za ki aura wajen irin wannan kwalliyar. Wallahi da za kiyi kwalliyarki da kika saba sai tafi miki kyau fiye da irin kwalliyar amaren yanzu da nake gani. Na ga amare da yawan gaske da wallahi kwalliyar muni ta sanyasu, maimakon ta ƙara musu kyau. Dan haka dan Allah ki taimaki kanki ki alkinta kuɗinki dan ki amfane shi ta wata sigar, amma ba ta wannan almubazzarancin ba.

Kasancewarki ɗalibar boko kar hakan ya ruɗeki ki yi yunƙurin amfani da ruɓaɓɓun shawarwarin masu kwarmato dangane da haƙƙin Mata. Ki sani, duk Mace mai wayo ba ta buƙatar tayi fito na fito da mijinta akan wani haƙƙi da take zargin yana danne mata. Mu kan kasance tamkar jarirai a hannun iyayensu mata a gurin matayenmu, dan haka banga dalilin da zai sanya har a ji ƙumajinki kan ana danne miki haƙƙi ba. Matuƙar kika kwantar da kanki wajen kyautatawa mijinki, tabbas kin biyo layin da aurenki zaiyi ƙarkon da na Mahaifanki yayi, wanda ga shi har za su aurar dake suna tare da daɗi babu daɗi.

Ki kasance Mace mai yawan alheri ta hanyar kyauta, musamman sadaka ga mabuƙata. Ki sani, ita kyautatawa ta kan toshe duk wata ƙofar cutarwa gareki, yayin da sadaka take bibiyarki da alkairan da baki isa kin tantance su ba. Dan samun ladan ciyarwa, ki nemi izinin mijinki ki samu ƙaramin almajiri ki sanya masa kwano a cikin tukunyarki. Hakan zai matuƙar taimaka miki wajen neman tsarin duk mai buƙatar cutar dake.

Ki kyautatawa maƙwabtanki ta hanyar zama lafiya da kyautatawa tsakanin ki da su. Ki sani, duk wacce Allah tasa tazamanto maƙwabciyarki tana da haƙƙin maƙwabtaka a kanki, wallahi muddin kika cutar da maƙotanki Allah ba zai barki ki samu cikakkiyar nutsuwa ba. Ki kyautatawa duk wanda zamansa ya kasance a ƙarƙashinki. Ki kyautatawa dangin mijinki tamkar yanda za ki kyautatawa naki dangin.

Wani bangare na 'Yan uwa mata a sahun Muzaharar #FreeZakzaky satin da ya wuce a garin Abuja. 

Kar ki taɓa wasa da addininki, ki dage wajen yawaita addu'o'i da nafilfili gami da azumin nafila idan mijinki ya sahale miki. Muddin kika riƙi waƴannan kinyi sallama da ƙuncin rayuwa ko wani iri ne.

A ƙarshe ina miki fatan Alkhairi a dukkan tsawon rayuwar aurenki. Allah ya baki dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali. Allah ya yalwata arziƙinku ya kuma kare ku daga dukkan wani sharri. Allah ya daidaita tsakanin ku ta yanda za ku fahimci juna ku zauna lafiya ba tare da husuma ba. Allah ya albarkaceku da managarciyar zuri'a, ya kuma tallafeku wajen tarbiyyantar da su, duk dan Alfarmar Annabi Muhammadu (S) da Alayensa tsarkaka.

A ƙarshen ƙarshe, ina mai nemawa abokina matashin Dan Jarida Muttaqah Kumasy afuwa saboda rashin samun damar halartar ɗaurin aurenki. Ba wai nesa da juna da ku ka yi bane ya hanashi halarta ba, halin yau da gobe ne kawai ya kawo masa cikas dangane da ƙudirce niyyar halartar ɗaurin Aurenki da yayi, har ga Allah yana da niyyar hakan.

Dan haka ina mai jaddada addu'ar neman zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin ku. Allah kuma yasa ayi taro lafiya a kuma gama shi lafiya.

   Wakilin Ma'asumah Nigerian News Updates -Idishia Jos ya nakalto muku labarin

Daga Yayanki Ahamad Musa Mc.
Suleja,Jahar Neja.
27/4/2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post