FUDIYYA TAHFIZ DAURA TAYI WALIMAR HARDAR HIZIFI 40 DA 20.

FUDIYYA TAHFIZ DAURA TAYI WALIMAR HARDAR HIZIFI 40 DA 20.

A jiya Assabar Ne,

Madrasatul Fudiyya Tahfiz Daura sun gudanar da walimar Hardar Hizifi 40 da kuma na 20, bayan Karatu daga Dalibai Wadanda suka hardace hizifi 40 da 20, daliban sun gudanar Karatu a bangaren Karatun Boko, inda a nanma suka nuna hazakarsu.

A bangare guda kuma Daliban Fudiyyan sun yi Tamsiliyya wadda take Magana akan Karatu da Muhimmancin Zuwa Makaranta, Sai kuma Bangare IM Production sukayi nasu Tamsiliyyar suma dai akan Karatu da Muhimmancin tura Yara Makaranta.

Daga karshe Wakilin Yan Uwa na Da'irar Daura Malam Mustapha Muhammad ya yi tsokaci a wajen Taron, Malam yayi Magana akan Muhimmancin Karatu Alqur'ani da riko dashi, yace "anan gaba idan Addini ya tabbata ko Chairman zaka tsaya takara sai Wanda ya Haddace Alqur'ani saboda da Alqur'ani ake hukumci kuma shine yake Jagoranci a Kasar Insha Allah".

A cikin Jawabin nasa Malam Mustapha Muhammad ya yi kira ga Yan Uwa Dangane da Tallafawa Yan Uwa Yan Abuja Struggle, tallafin ya hada da Kudi, Kayan Abinci gero, dawa, shinkafa, Masara, Sugar da Sauran kayan bukatu. Kuma akwai tsarin karbar Tallafin daga Wajen Wakilan Da'irori da kuma Masu gudanar da Al'amura.

Sai kuma Jawabin godiya da Malam Abdulkadir Likita, a madadin Fudiyya Tahfiz, aka raba kayan walima, akayi Addu'a aka Sallami kowa.

Lallai iyayen Daliban sun nuna farin cikin su inda suka gayyato Yan Uwansu na Jini domin su tayasu farin cikin da Wannan ranar. Allah ya nuna mana ranar da wadannan Yaran Zasu Haddace Alqur'ani.

Ga wasu data cikin Hotunan Taron.












#FreeZakzaky
@ishaq sagir magaji
28-4-2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post