A LURA 'YAN'UWA WANNAN MAGANAR CIN MUTUNCI NE DA TABA SHAKSIYYAR SAYYID ZAKZAKY(H). 👇:-



 ðŸ‡³ðŸ‡¬ Ma'asumah Hausa Nigeria News updates


*Tare da wakilinmu Muh'd Aliyu Daud (Dansudan) Azare 070-32803940*

 Ko ana neman dakusar da darajar Sayyid Zakzaky(H) ko kuma a gagarin daga darajarsa aka dakusar da ita. Mun soki wannan maganar ne sabida dalilai kamar haka!

1) Shin Malam ne zai yi hukunci akan abinda bashi da hurumi a addini!?

2) Shin yin mata biyar Shari'ar Musulunci ne, da har Sayyid ya yadda yai hukunci akayi!?

3) Shin Miyasa aka nuna cewa Sayyid ya yadda da cewa mace ta biyar din a matsayin mata, mi ake so a nuna mana anan!?

4) Shin Miyasa aka nuna mana, Sayyid ya sabawa ayar Qur'ani, da ta yi magana akan irin wannan matsalar.

5) Kuma wai Sayyid yace bayan hukuncinnan da ya yi duk duniya ba irin wannan hukuncin, yanzunnan na samo muku shi, da za ku zagaye duniya babu wanda zai iya muku shi. Wannan mi ake so mu fahimta anan, alfahari ba dabi'ar Sayyid bane, kuma sayyid baya hukunci da son ransa, sai abinda ya dace da fadar Qur'ani da koyarwar Manzon Allah da A'immah (A. S).

6) Shin miyasa labarin sai yanzu ya fito, tunda can bamuji labarinsa ba, irin cigaba na wannan zamani

  Da sauran tambayoyi na tsaya anan sabida gudun tsawaitawa, mai karatu kaci gaba daga inda na tsaya nasan sunanan birjik.

 Wannan in anyi da Shina ne ko kuma da kuskure toh, cin mutunci ne ga Sayyid Zakzaky(H). Yan'uwa sai mu rinka lura da irin wannan.  *A LURA DASHI 👇"PLEASE"*

----------------------------------------
ILIMIN SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY DAGA ALLAH NE!

Daga: Muhammad Makana

Wata rana Sheikh Zakzaky yana zaune a cikin falo, a cikin gida (Gyallesu), ya dan kashin gida kadan ana hira da sauran yan uwa. sai wasu bayin Allah mata suka shigo cikin gidan, matan su biyar ne, suna dauke da dukiya mai tarin yawa. sai suka sami waje suka zauna suka a jiye dukiyar a gaban Sheikh Zakzaky. aka gaggaisa suka ce sun zo gun Sheikh Zakzaky ne don ya raba masu gado.

Suka fara yiwa Sheikh Zakzaky bayani, mijin su daya ne dukansu, kuma su biyar ya aura, (ma'ana dai matansa biyar). kuma yanzu ya mutu ya bar masu dukiya, kuma su biyar ya bari, an rasa yadda za'ayi a yi wannan rabon gadon, domin sanin kowa ne a musulunci mata hudu ake yi, amma shi mijinsu Mata hudu yayi, kun ga ya sabawa musulunci. gashi yanzu ya mutu, kuma ga dukiya ya bari, an rasa yadda za'ayi a raba masu ita su biyar. sun je wajen Malamai dayawa, amma sun kasa yin wannan rabon gadon, saboda su biyar ne. sai wani Malami a nan Zaria yace masu; su zo nan Gyallesu gurin Sheikh Zakzaky domin shi kadai ne zai iya warware wannan matsalar, sannan ya raba masu gadon, wannan ne ya sanya suka zo.

Sai Sheikh Zakzaky yayi murmushi, yace to sun zo inda za'a raba masu gadonsu, sai suka gyara zama don jin yadda za'ayi wannan rabon gadon, na matan mutum daya su biyar. suka yi alkawarin zasu amince da duk hukuncin da Sheikh Zakzaky yayi masu.

Sai Sheikh Zakzaky yasa aka kawo takarda da abin rubutu, yace to daya zata yarda ita ba matarsa bace, amma za'a rubuta a takarda kowacce zata dauki daya, za'a rubuta (ni matarsa ce sau hudu, sai daya takardar a rubuta ni ba matarsa bace) sai kowacce ta zabi daya, duk wacce ta dauko ni ba matarsa bace to baza'a yi rabon gadon da'ita ba, amma tayi hakuri ita ma zata samu, dukkansu suka yarda. daya bayan daya, suka fara dauka, kowacce aka duba abinda ta dauko, sai daya aka ga ta dauko ni ba matarsa bace. Sai Sheikh Zakzaky yace ita ta koma gefe ta zauna.

Sheikh Zakzaky ya dauki dukiyar ya raba masu gadonta su hudun, dayar kuma aka barta ba'a bata ba, bayan Sheikh Zakzaky ya kammala rabama masu gadon gabadaya su hudun, sai yace to kowacce a cikin hudun nan ta dunkulo abinda ta gadama (Ihsani) a cikin nata kason kar kowa ya gani ta bai wa waccan da ba'ayi kasom da ita ba.

Dukkansu suka dibo wani kaso daga cikin kason da suka samu suka baiwa waccan dayar, da suka gama bata abinda suka yi niyya, sai aka kirga abinda wacce ba'ayi kason da ita ba aka ga mai tasamu, sai aka ga ai dan kason da suka hada mata ya fi wanda su kansu suka samu (abinda hausawa ke cewa da karo-karo giwa tafi kowace dabba kiba). sai suka yi godiya dukkansu suka kuma amince da wannan rabon. suka ce wallahi sun yi yawo an ma ba'a sami Malamin da ya raba masu wannan gadon ba, sai da suka zo nan gurin Sheikh Zakzaky.

Sai Sheikh Zakzaky yace ai duk duniya babu wannan hukuncin yanzun nan ya samo masu shi, in zasu zagaye duniya baza su samu irinsa ba, sai dai yanzu daya yi wannan hukuncin. akan wannan rabon gadon mai sarkakiya.

Sheikh Zakzaky mai ilimi daga Allah za babben Allah rabba, waye ke da jagora kamar nawa?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post