TSARIN ALLAH NE MAFITA GAREMU DUNIYA DA LAHIRA

TSARIN ALLAH NE MAFITA GAREMU DUNIYA DA LAHIRA


Misalin wanda yace yana neman mafita a nigeria ta hanyar siyasar Kasar to tamkar mutum ne ya ɗauki bukiti yace zai kwashe ruwan teku

Domin ba yadda za'ayi nizamin da ba ruwan sa da Allah ba ruwan sa da Manzon Allah ya kawo sauki ga Al'umma, har ace yau al'umma sun mance da Mahaliccinsu wai suna neman mafita a gurin Azzaluma kafira kuma fasikar gwabnati kasan abinda bazai samu ba kenan!
wannan duk Allah ne ya fada ba ni ba don kar kayi zagi.

Allah a cikin littafinsa mai tsarki yana cewa:"duk wadan da basu yi hukunci da abinda Allah ya saukar ba to su wa'annan kafurai ne wani gurin Allah yake cewa su fasikai ne wani gurin ya kira su da azzalumai kuma duk acikin sura guda wa'annan ayoyi suke duk da wa'annan maganganu da Allah Ta'ala ya faɗ amma abin mamaki shine yanda wasu malamai suke zaƙewa akan wannan siyasar alhali sune Muke tanƙware kafufuwan mu suna fassara mana wannan ayoyin,

kamar akwai wani malami wanda nayi karatu gareshi inda na sanya wani littafi gurin sa na sunni wanda nayi ta mamaki cewa a cikin wannan littafin, duk da ko littafi ne ƙarami amma ya taro maganganu masu yawa akan fassarar wa'annan ayoyin dama magana akan su waye Ɗagutai inda mai littafin ya nuna cewa wadan da suke hukunci da saɓanin dokar Allah sune Ɗagutai har ma ya nuna cewa imanin mutum bai cika har sai yayiwa Ɗagutai tawaye amma yau wannan malamin shine shugaba a runfar zaben su ana basu abubuwa suna rabawa wani lokacin su danne haƙƙin wasu,

Allah dai ya kyauta ya fahimtar da wannan al'umma sakon Addini na gaskiya kamar yadda ya fahimtar da mu, domin mu-ma fa baiwa aka yi mana ba dabarar mu bace ba yin kanmu bane,

Daga karshen ina roƙon Allah ya bamu sabbati ya kwato mana Syed Zakzaky daga hannun Miyagu Azzalumai alfarmar Amirul Mu'uminin Ali bn Abi Dalib (As)

Ishaq Muh'd Suleiman

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post